® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''*SA'EEDA MUSA DAUDA😍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *SaeedaMusaDauda*
*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''7⃣
Jikin ta ne ya bata yana kallon, da sauri ta k'awar da kan ta gefe ta inda take tunanin ba direction d'in da yake bane ta d'ago fuska taffffff da hawaye tana kallon saitin window.
Duk wanda ya gan ta a wannan lokacin zai rantse da Allah cewa tana gani ne saboda yanayin zaman da tayi, ba tare da ya Abdallah ya d'aga idanuwan shi daga gare ta ba ya gyara zama yana kallon irin baiwar kyau da Allah yayi mata, wai ace ga mace har mace kamar Aysha ga kyawun fuska da ta jiki amma bata gani??,
"uuuhhhmmmm" ya fad'a da k'arfi dan shi kad'ai ya san irin yanda yake jin ta a ran shi dan har ga Allah yana tsananin son ta kuma baya jin zai iya rabuwa da ita amma ya sani cewa koh kad'an inna bata son alakar shi da ita kuma zata iya kawo mishi cikas wurin mallakan ta.
Saurin sakin hannun ta yayi ya mik'e tsaye yana magana murya na sarkewa a sakamakon b'acin ran da yake ciki yace" shikenan k'anwa ta babu komai koh ma dai wanene Allah zai saka miki, ina so ki mik'a lamuran ki ga Allah shi ke da maganin duk wata musifa da ta samu bawa ciki, a sanyaye yace" Aysha" "uuuummm" ta amsa, yayi jimmmm kad'an saboda fargabar yanda zata d'auki maganar idan ya fad'a mata da kyar ya bud'e baki cikin tattausan muryar shi yace" shin zaki aure ni??.
Tambayar ta shi ce ta zo mata a bazata cikin tsananin mamakin abunda ya fito daga bakin shi ta dafe k'irji alamar kad'uwa tace" na shiga ukuuu ya Abdallah aure fa kace koh ka manta cewa inna bata k'auna ta,, yayin da a zuciyan ta take nanata Inalillahi wa'inna ilaihiraji'un" gaban na fidda sautin k'ara dum dum duuuummm kamar ana doka ganga dan k'iris ya rage na kwashi shoki sai da na dad'a saurarawa before na gane cewa sautin daga k'irjin Aysha ta ce ke fitowa.
Kwantar da murya yayi cikin tsananin tausayin k'anwar tashi yace" ehhhh k'anwa ta wannan shine kad'ai zai fitar da ke daga cikin halin da kike ciki ya kuma sada ki da farin ciki mai d'orewa a rayuwar ki da yardar Allah,,
Runtse idanuwan ta tayi da jin kalaman shi wasu silent tears ne suka fara gangarowa a idanuwan ta ba ma maganar ammincewar inna ce ke damun ta ba sai dai tunawa da tayi da *Macucin* da ya cutar da ita ya mai da ita tamk'ar bazaura,, ta yaya zata iya ammincewa da bukatar shi bayan ta san cewa da matsayin ta da fanko duk d'aya ne a wurin duk wani namijin da ta aura,, bata da wata sauran daraja balle ta sa ran zata samu rayuwa mai inganci ??.
Ba tare da ta ce komai ba ta tsinkayo muryar shi yana cewa" ki taimaki zuciyar yayan na ki ki amince da bukatar ki wallahi Aysha a shirye nake na fuskanci duk wata kalubale da zata doso mu a duk lokacin da inna ta fahimci akwai wata alaka a tsakanin mu.
"Uhhhhmmm" ya Abdallah baza ka fahimci abun da nake nufi bane", Aysha kenan take fad'a a kasan zuciyar ta yayin da a fili ta daidaita nutsuwar ta ta kuma sakin ajiyar heart cikin matsananciyar damuwa tace" bazan tab'a k'in ka ba yaya na sai dai abu d'aya nake fargaba a rayuwa ta wanda koh da inna ta amince shi kad'ai zai mana katanga".
A razane yace" What !!! please kar ki min haka ki taimaka ki bani dama da yardar Allah ba zaki yi dana sanin aure na ba,, kuka ta fashe mishi da shi ganin ba zai iya jure ganin zuban hawaye a fuskan ta ba ya mik'e tsaye ya daga d'akin cikin k'unan rai.
Jin alamar tafin shi tare da rufe k'ofan d'akin ne ya tabbatar mata da cewa ya fita a, sai da taci kuka iya isanta kafin ta tsagaita ta sa hannu face d'in ta a hankali tana share hawayen da suka zubo mata.
YOU ARE READING
WAYE MACUCI
Historical FictionLabari ne a kan wata mak'auniyar Allah mai suna Aysha wacce take soyayya da yayan ta amma kwatsam sai wata tsautsayi ya afka mata har hakan ya saka ta cikin bakin ciki,ba tare da ta bayyana mishi ba sai daga baya ya fahimci halin da take ciki a tsan...