Chapter 1 page 99

219 17 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 9⃣9⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Su Rukayya aka hau hura hanci aka shirya. party da dinner. Da ta ajiye kati na Umma da Ummu ma sai Anty Sailuba ta kwashe ta bayar. Da da tazo tana neman katin ta nema ta rasa shine ta tambayi Anty Sailuba tace
"Wa zaki bawa?"

"Su Ummu!"
"Ba irin su muke nema ba mayan yara muke nema."

Kallon ta Rukayya ta tsaya tace
"Amman Anty yan uwan mu ne fa."
"Shine me ai da daurin gindin uwar ta hana Abba daura miki aure."

"Kai Anty me zatayi ita dan Allah."
"Rufen baki shashasha kawai kila kina zaune sa kashe miki aure."
Bakin ta ta rufe amman ranta ya baci.

Ranar daurin auren mijin Anty Sailuba ya daura mata aure kamar yadda suka tsara akai party sannana akai dinner  an kaiwa Abba goro da alawa Abbah ya diba ya kaiwa Ummu sannan ya bawa Umma yace
"Allah sanya alheri."

Ranar kai amarya da Rukayya tace a kai ta tayi sallama da Abba sai cewa sukai aah sai da Rukkay ta tubure sannan aka kai ta. Ana shiga da ita Abba yace
"A'ah Amarya ce?"

Durkusawa tayi tace
"Abba ka sa min albarka dan Allah."
"Allah miki albarka Allah ya bada zaman lafiya"

"Amin!"
Yace
"Ku tafi"
Aka daga ta aka fita da ita. Ummu sai da aka kai mata alawa da goro sannan tasan da auren Rukayya. Daga nan aka dauki Rukayya aka kai katon gidan ta da Alhaji Khamis ya gyara mata ya zuba mata kaya a ciki.

Haka aka watse aka bar amarya. Alhaji Khamis ya shiga bayan kowa ya watse da kaji da lemuka. Haka suka ci suka sha sannan sukai sallah suka kwanta. Haka suka sha amarcin su cikin jin dadi da kwanviyyat hanlali. Rukayya komai a gidab ta kamar zai magana kaji da kayan dadi dan haka sai ta kara yadda da mijin ta tana ganin kamar daman can bakin ciki ake mata

*
**
***
****
*****
******
Kabir kuwa da lokacin komawar sa dakin Halima yayi har wani zumudi ua dinga yi dan maya boye saboda kada Sadiya tagane. Ana magariba ya shigo musu da kaji bangaren Halima ya nufa yana zuwa,  ya same su dukka su biyun zaune kowa yavi kwalliya kanar me masu zuwa biki wani dadi da farin ciki yaji ya ziyarce shi. Dan haka ya zauna yana fadin
"Halima da Sadiya matan Kabir!"

Sukai murmushi a tare Sannan suka ce
"Barka da zuwa!"
A tare kallon junan su sukai duk sai sukai murmushi shima yace
"Gaskiya ne suna iri daya magana ma a tare kun zama twins!"

"Haba dai ai ta girmenfa."
Halima ta fada. Sadiya tace
"A aure kuma kece yaya ta ko?"

Sai tai murmushi kawai. Lesar hannun sa ya ajiye yace
"A kawo mana muci ko?"
Sadiya tace
"Anty a kawo mana."

Halima ta baya fuska tace
"Ni dai bana son wata Anty ni bance miki ba sai ke."
"To sorry sister! Tashi muje."

Tayi murmushi ta mike sadiya ta dauki ledar sukai kitchen,  Kabir ya bisu da kallo yana jin dadi. Tare suka fito Halima rike da plate da yake cike da gashin kaji,  Sadiya kuma cups ne da lemo ta ajiye a kasa ya sauko ya zauna kowa ya zaua a gefen sa yace
"Bismillah!"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now