Chapter 1 page 28

225 30 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 2⃣8⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

Hawaye ne ya fara zubowa daga idon sa. Hannun ta ta saka tana share masa. Dagowa yayi yana kallon ta yace
"Ki yafe min!"

Hannu yasa a aljihunsa yaciro wani zoben gwal mai dan girma, yakamo hannunta ya zura mata a yatsarta na tsakiya, ya kalli yadda zoben yai mata kyau. Kissing hannun yayi yace
"Wannan alkawari nane ni dake mutu ka raba."

Wani hawayen farin ciki ke zubowa Halima, Isma'il kuwa ganin ya shawo kanta, ya cigaba da mata alkawaririka ta kuwa kara saki jiki ta manta duk kuncin datake ciki...........

Sun jima dan sai da ya wanke duk laifin sa sannan ya bata wata katuwar leda da aka cika da shopping kala kala na ciye ciye da sutura har da sabuwar waya ai kam taji dadi sosai haka ta fito tai cikin gidan zuciyar ta fes dan Isma'il yace ba zai bar ta ba.

********************************************************************************************************************************************************************************************************
Hannah ce ta mike ta shiga falon Momy. Momy dake zaune tana neman layin Ahmad tace
"A'ah ina lallen?"

Fuska ta bata tana turo baki tace
"Yanzu Momy dan Allah Yaa Ahmad ba zai yadda ai yar dinner nan ba please so yake kawaye na su rainani haba Momy please kiyi masa magana nasan zai ji ki."

Murmushi Momy tayi tace
"To Allah yasa ya yadda dan kinsan Halin Ahmad sa kafiya."

Hawaye Hannah ta fara Basma ce ta shigio tana fadin
"Wallahi Anty Hannah za a farai min!"

"Ba sai a farai mikin ba."
Ta fada tana hararar ta.

Dariya Basma tayi tace
"Uhmm Momy kunyi waya da Yaa Ahmad din ne? Yaushe zai zo!"

"Yanzu nake neman layin nasa dai a kashe."
Ta fada tana kallon Hannah tace
"Hannah jeki ayi lallen kar dare yayi"

"Mikewa tayi ta fita tana turo baki. Basma tace
"Ina tausayawa Anty Hannah wallahi."

"Da me?"
"Yaa Ahmad sam bai son ta Momy."

"Kar na kara jin wannan maganar kuma in anyi auren ai zai so ta."
"Uhmm to Allah yasa."

"Amin!"
Ta fada tana fadin
"Amman Momy gaskiya ni ko ba zai zo ba ai mana abin mu!"

"Bare zai zo ma. Ai shiyasa ya kashe wayar tasa wallahi yayi wasa gobe ya ganni a Abujan."
Mikewa Basma tayi tace
"Gaskiya dai Yaya yaci ya dawo gobe fa za ai bridal shower!"

"Uhmm!"
Kwafa Momy tayi tace
"Wallahi Zai zo ya samen ne."

Mikewa Basma tayi tace
"Bari naje Anty ta gyaran kai kan a zo min lallen."

"Ok!"
Ta fice.

***** ****** ****** ****** *****
Kwance yake duk abin duniya yai masa yawa ga auren da za ai masa ga mafarkan Hafsa da yake yi kullum tana me neman taimakon sa.

Ya kasa gane kan mafarkin nasa akan me take neman taimakon sa bai sani ba wannan ya kara masa wutar son ta wanda yadauki damarar ceto ta ya taimaka matan.

Duk da yasan weekend din nan ne bikin sa amman ya yanke shawara sai friday zai shiga kano Saturday a daura aure wannan yasa ya kashe wayar sa dankar Momyn sa ta dame shi dan yasan in ya kunna bataki tace ya dauki hutu ya tawo ba.

A gida kuwa ana ta shirye shirye dan ranar alhamis bridal shower, Friday dinner asabar daurin aure da kai amarya. Wanda gidan Dady ne ya gina masa shi da kansa, kuma shi yayi wa amarya komai na gidan.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now