Chapter 1 Page 6

303 21 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 0⃣6⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

A haka rayuwa ta cigaba da tafiya sakanni na komawa minti na, minti na komawa awa, awanni na komawa kwana, kwanaki na komawa satitika, satittuka na komawa wattanni. Don har anci wata uku da auren kamar yau akai abin ake gani.

Muhammad ya samu aikin koyar wa anan wata primary but gwamnati ce ta dauke shi yana daukar albashin sa dubu talatin da wani abu. Watan sa hudu da fara aiki ya samu admission inda zai juya degree din sa anan BUK sai dai ma'aikatar su tace sam ba zata bashi inservice ba saboda bai jima da fara mata aiki ba. Da ya zauna ya yi tunani sai yaga komai na Allah ne tinda ya samu admission din nan gwara ya fara karatun aiki ai daman bai zama lallai yayi ba ko kasuwancin sa Allah ya bawa sa'a sai ya zama wani abun. wannan yasa ya hakura da aikin kan cewar in ya gama karatun zai koma. Tin kan ya ajiye da ya yi shawara da Hajiyar sa itama cewa ta yi yaje ya karo karatun bai san gaba mai zai zama ba. Wannan yasa ya ajiye da gayya don shawarar Hajiyarsa.

A wannan lokacin ne kuma Rukayya ta fara laulayin ciki. Don haka komai shi yake mata sannan ya tafi makaranta. Tinda ya ajiye aiki sai abubuwa suka fara yi masa yawa don baya samun zaman shago da safe yana dawainiyar gida da rana yana makaranta in ya dawo da yamma ma yana kanta. Da dare shima ya gaji da kyar yake iya bude shagon ya kai goma sannan ya koma gida.

Da yaga abin na yawa ba kudi a gun sa sai yayi wa Hajiyar sa magana ita tace kanin sa yana zamar masa, don haka sai ya samu rangwami suke gungura rayuwar su a haka.

A lokacin ma Zainab na da ciki karami mijin ta kuma ya samu canjin aiki acan Abuja, Inda suka bashi gida da mota wannan yasa suka fara shirin barin Kano, ganin tana ɗan laulayi kuma tafiyar nesa ita kadai wannan yasa suka je har wajen Abba neman alfarmar a basu Ummulkursum tinda ta gama karatu secondary.

Abba ya ce ya samar mata admission amman Mijin Zainab yace shima zai samar mata acan. Ba don Abba yaso ba sai don nauyin sirikin nasa da yake ji ya yadda ya amince. Suka tattara suka tafi da Ummulkursum.

Sailuba kuwa sam bata da ciki sai duniyar ta take ci da tsinke, don da mijin ya mata maganar komawar ta can gidan iyalan sa sai tai wa Mama magana. Mama tai wa wata kawar ta magana nan suka tafi gun wani malamai har aka samu aka rufe masa baki. Bai kara maganar ba.

Suna komawa Abuja ogan su Suleiman ya samar wa Ummulkursum makaranta ta fara karantar pharmacy. Sam bata da damu dakin ta daban akwai komai haka nan sai abinda take so mijin yayar ta yake mata, itama yayar tata haka. Har yanzu bata canja shiga ba zata saka kaya masu kyau da tsafa amman fa zata dauki hijab da nikaf da safa ta saka. Zaman ta a gari ta kara kyau da wayewa, suna zaune lafiya da yar uwar ta, sai dai su yi waya da can gida ko da Rukayya.

Cikin Rukayya da ya cika wata tara mama tace dole ta koma wankan gida don ba mai zuwar mata, Muhammad bai so ba amman ba yadda zai yi haka ya barta ta tafi, don ita kan ta Rukayya bata so komawa gidan ba.

Sai dai tinda taje zaman gida sai Mama ta dinga hure nata kunne, bama da taga yayar ta irin suturar da jin dadin da take ciki ga katon gida da mota, kudi kam sai dai taji ana maganar dubu dari kaza. Tin tana kin biye musu har ta fara jin shawarar yayar tata tana ina ma ita ce.

Haka in suna waya da Ummulkursum ko vedio call taga a irin gidan da suke sai duk taji jikin ta ya yi sanyi. Kullun Mama ce cikin cewa ta fadawa Muhammad ya kawo kaza da kaza, daga baya ma ta ce ya kawo kudin kayan abincin ta, Rukayya ta ce
"Haba Mama, a gidan ubana fa nake,"

Mama ta ce
"A gidan uban naki fa ai a karkashin sa yanzu kike nauyin ki na kan sa."
"Gaskiya Mama bazan iya ba ai sai ya raina mahaifina bayan Abba bai ce ba don dai cin abinci kawai. In Abba ya yi magana na masa amman ba ke kike ciyar dani ba."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now