Chapter 1 page 53

219 17 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 5⃣3⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

9:00am

"Son kaci abincin in aike ka mana!"

Hajiyar ya kalla yace
"Mom where is Sakina ne? I can't eat untill i see her!"

Ido ta zaro tace
"Ibrahim!"
Da sauri ya dago dan bata taba kiran sunan sa haka ba.

"Ka fita a ido na in rufe wallahi!"
Kallon ta kawai yake ya kasa magana. Mikewa tayi ta haye sama da sauri idon ta na kawo ruwa.

Tana hawa sama ya mike ya nufi dakin da Sakina ke. A gaban mirrow ya same ta tana gyara fuskar ta. Sanye take da riga da siket na atamfa sun amshe ta batai make up ba amman tayi kyau tayi daurin ta mai kyau. Ta mirrow ta hango shi yana kallon ta. Itama kallon nasa take ta kasa ko da dauke kai ne.

Sun jima a haka sannan ya tako a hankali ya shigo cikin dakin. A jikin kofa  ya tsaya ya rumgume hannun sa a kurji yana kallon ta. Kai tayi kasa dashi ta juyo a hankali tace
"Ina kwana?"

"Lafiya lou Baby mie kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillah."

"Na kasa cin komai saboda ban ganki ba."
Dagowa tayi da sauri. Yace
"Sure. Muje mu karya ko?"

Ya bude kofar yana nuna mata waje. A hankali ta taka ta fita ya bi bayan ta. Shi ya ja mata kujera ta zauna ya hada mata tea ya zuba mata cheeps sannan ya tura mata gaban ta. Nasa ya hada amman ya kasa taba komai in banda kallon ta da yake. Kasa ci itama tayi da ta dago sai su hada ido yana sakar mata murmushi. Ganin sun kasa cin abincin gaba dayan su yace
"Bismillah mana!"

Kai ta make a kafada tace
"Ka daina kallo na to!"

Murmushi yayi ya dauki mug din tea din ya kurba sannan yace
"Na daina."

Nata ta dauka ta fara sha tana ci a hankali bata yadda ta dago ba dan tin bata dago ba tana jin idon sa a kan ta. Bayan ta gama ta dago taga ya kure ta da ido. Kai ta gyada masa alamar
"Ya dai?"

Kan sa ya shafa yana murmushi yace
"I love u Sakina."
Shiru tayi tai kasa da kanta. Yace
"Baki ce komai ba."

"Khaleel kayi hakuri!"
"Inyi hakuri dame Sakina. Kada kice nayi hakuri da sonki dan sonki ya riga ya gama shiga jiki na ta yadda ba zan iya rayuwa babu shi ba."

Kwarewa tayi ta fara tari dan yadda ta tsorata. Da sauri ya mike ya dauko mata ruwa ya kawo mata ta. amsa ta sha sannan ta lumshe idon ta sai sannu yake mata ta jima a haka sannan taji ya fada mata dan haka ta mike tayi dakin da take. Da kallo ya bi ta. Mikewa yayi ta tafi sama dan amsar sako wajen Mom din sa.

*
Hajiyar ce zaune a gefen Sakina,  tace
"Yaushe zaki tafi ne?"

Kallon ta Sakina tayi ta dauke kai dan wani tsanar Hajiyar take ji. Tace
"Ni ko yau ma ina son tafiya Hajiyar!"

"Da gaske?"
Kai ta gyada. Hajiyar tace
"Shikenan ki hada kayan ki in kin tafi zan neme ki amman yanzu nayi missing din ki ba zaki dan ragen zafi ba."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now