Chapter 1 page 35

247 25 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 3⃣5⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*
*
Doctor na fita Isma'il ya mike ya dawo gaban Halima a kasa ya durkusa gwiwar sa a kasa. Hannun ta ya kamo yana mai zubar da hawaye. Dagowa tayi tana kallon sa idon ta jajir dan yadda kan ta ke ciwo har jijiyoyin kan ta sun tashi.

"Halima ki yafe min dan girman Allah wallahi bana jin dadin yadda kike min tin jiya kin ki dauki waya ta kin bar ni a cikin tashin hankali ashe baki da lafiya baki fada min ba. Halima wallahi da gaske nake son ki ba zan taba son abin da zai cutar dake ba. Wallahi wallahi Halima na shiga damuwa na ganin kema kina cikin damuwa a ta dalili na nayi da na sanin yin abinda nayi da na sani mutuwar nayi da wannan halin da kike ciki...."

"In ka mutu ka bar ni da wa Isma'il bayan kasan yanzu ban da abinda wani 'da namiji xai yi alfahari dashi a waje na. In har ka mutu to ka sani nima mutuwa zanyi dan ban san ya zanyi da son ka da kuma halin da nake ciki ba. Kasan na rasa martaba ta kai kadai nasan zaka amshe ni a yadda nake in kuwa ka mutu in doshi wa?"
Ta gama magana tana kifa kan ta akan table din gaban ta.

"Ya isa daina kukan ba zan mutu ba ina tare dake har karshen rayuwa ta amman dan Allah kina min uzuri kome nake *son ki ne sanadi* dan a dalilin sa nake kasa controlling feeling dina. I love u Halima. I love u wit all my mind u re my happiness my life my everything i can't do with out u. U re my soul mate Baby i will never leave u dis is a promise with my heart and my god i will never....."

Sai kuma yai shiru yana kallon ta. Hawaye take tana mai murmushi. Kalaman isma'il ya sanyaya mata rai kuma yadda yake daukar mata wadan nan alkawarurukan ta yadda dasu dari bisa dari dan haka sai ta saki kuka tana fadin
"Wane irin so kake min haka Isma'il na yadda na aminta dakai dan Allah kar ka juyan baya ko ka cutar dani zuciya da kai ta saba da kai ta yadda dan Allah Isma'il ka rike ni amana na maka alkawarin yi maka kome kake so in har zamu kasance tare har karshen rayuwar mu."

Kuka ta fashe masa dashi. Tashi yayi ya karasa wajen ta. Rumgume ta yayi yana lallashin hadi da bubbuga bayan ta.
"Kar ki damu kinji. Fatana Baba yace ya yadda a turo da zancen auren mu daga nan ne zaki gane irin son da nake miki."

Ya fada yana goge mata hawaye. Dr ne ya shigo yana ganinsu a haka yace
"Kai Isma'il kai fa dan love ne ka kyale ta bata da lafiya ma sai ka takura mata."

Murmushi Isma'il yayi yana fadin
"Mu ka bamu magani mu tafi na damu naga my life ta warke wallahi."

Murmushi Dr yayi yace
"Anyi test amman ba wata matsala sai dai jini ta da ya hau shi yake causing mata headach din nan. Me take sawa a ranta da ta ke shiga wannan halin har jininnta ya hau. Any way dai ya kamata ta daina saka damuwa a ran ta komai na duniya a bishi a sannu. Zan bata magani sai ana kulawa kinji?"

Ya fada yana kallon Halima. Kai ta gyada ya saki murmushi ya rubuta mata magami ya bawa Isma'il suka fita. Yana masa godiya. A compound din asibitin ya shiga dasu cikin mota shi kuma ya tafi ya siya mata magunguna sannan ya dawo zai shiga mota kenan sai ga kiran Kabir nan.

Mota ya shiga Halima ta shiga gaba sannan ya dauki wayar tashi.
"Hello guy ya kake ne?"

"Lafiya kana ina ne?"
"Gani na kawo Halima asibiti bata da lafiya."

Gaban Kabir ne ya fadi yace
"Me yake damun ta?"
Yai tambayar cikin tashin hankali.

Kallon Halima Isma'il yayi yace
"Ciwon kai ne amman da sauki."

"Ayyah bani nai mata sannu."
Wayar Isma'il ya mika mata sannan ya tada motar suka dau hanya.

"Assalamu alaikum!"
Halima tayi sallama cikin sanyin murya.
Tsikar jikin Kabir ce ta tashi. Ido ya lumshe kafin ya amsa mata sallamar.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now