Chapter 1 page 90

190 17 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 9⃣0⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

*
Ahmad yana komawa ya samu Dady a falo. Shiga yayi ya zauna yace
"Dady daga gidan su Hafsa nake"

"Yarinyar da kake neman aure ko?"
"Eh ita!"

"To me ya faru?"
"Dady iyayen ta ne suka nemi da in aiko."

"To ba damuwa zuwa jibi sai aje sai ka sanar."
"Insha Allah nagode Dady."

"Ba komai Allah bada zaman lafiya amman ina son ka bani address nay bincike kan naje ko?"
"Eh Dady hakan ma yana da kyau."

Nan ya bashi address da sunan yarinyar yai masa sallama. Cikn gida ya shiga sauri sauri ya wa Momy sallama ya tafi dan dare yayi.

*
A falo ya same ta tana aikin nata. Ya shiga da sallama ya zauna akan kujera ta juyo tace
"Shine ka tafi ka barni ko?"

"To kina bacci tashin ki zanyi?"
"Eh mana."

"Gobe kya je."
Ya mike yayi ciki. Tabishi da kallo tana son mijin ta. Zaman ta dashi ta gane yana da saukin kai da kyautatawa iyali. Amman dan me ita ta kasa bashi dama su zauna lafiya. Saboda zugar kawaye sunce in tana masa biyayya sosai sai na wulakanta bama da baya son ta. Kuma ta yadda dan wanda sukai auren soyayya suma ya zaman ke kayawa bare ita da auren hadi ne ita ke son sa.

Zata bashi lokaci taga gani in yaso sai ta sakar masa. Amman itama tana son mijin ta tana son tana kyautata masa.

Tashi tayi ta kashe kayan kallon tai daki ta kwanta kawai. Waya ta dauko ta shiga whatsapp kawar ta Kausar ta sama a online tai mata sallama ta amsa yana fadin
"Ai ma zata kina wajen mijin naki."

"Ina fa yanzu ya dawo wallahi Kausar Yaa Ahmad tausayi yake bani."
"Tausayi akan me?"

"Abinda nake masa."
"Zauna tausayin ki ya samu dama ya gasa ki. Malama ki cire wani tausayin sa ki gama kame shi sannan."

"Har yaushe kenan watan mu nawa da aure mun fi wata shida fa haka rayuwar aure na zata kasance."
"Ki bari sai kinyi shekara lokacin nima haka nayi yanzu baki ga zaman mu muke lafiya."

"Shikenan yaushe zaki zo?
"Eh to zan duba yaushe zaku tafi?"

"Kinsan kwana biyu zamuyi dai mu juya."
"Zan kokari na samu na shigo."

"Shikenan"
Haka suka cigaba da hirar su har goma sha daya sannan sukai sallama.

Ahmad na shiga yai wanka ya fito ya shirya cikin kayan bacci sannan ya hau gado. Waya ya dauka ya fara neman layin Hafsa.

"Ya kaje gida?"
"Alhamdulillah nayi kewar ki."

"Kai Deedat!"
"Da gaske nake. Ina fatan kasancewa dake har abada. Mutuwa kadai nake son taraba mu soyayya ni dake zan kasance."

"Fatana da kai kenan! Na baka riko kai ka ajiyen zuciya ta dake gun ka dan har abada kana raina. Kada ka guje min."
"Hmmm Mai niyyar alheri kada ka canja Allah baya son mai nuna izza zan tarairaya baza na gaza zan kula dake zan tarairaye ki tamkar kaza kece ni,  nine ke soyayya da taraiyya."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now