Chapter 1 page 51

200 20 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 5⃣1⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

*
**
***
****
*****
Kabir na fita a office din Isma'il ya nufi patking lot. Motar sa ya dauka ya nufi gidan su Halima. Yana isa yai parking ya jima zaune a mota yana tunanin ta ina zai fara. Cam dai ya bude motar ya fito. Kalle kalle ya fara ta ina zai samu yaro ya aika sa. Ana haka sai ga Hajara zata shiga gidan. Da sauri ya karasa yace
"Sister Halima!"

Da sauri ta juyo. Tsayawa tayo har ya karaso tana kallon sa da tina a ina ta sanshi amman ta kasa har ya karaso ta dan durkusa tace
"Ina yini?"

"Lafiya lou. Baki sanni ba ni abokin Isma'il ne!"
Murmushi ta saki tace
"Allah sarki. Ya Yake kuwa dan Anty Halima duk ta rasa nutsuwar ta kwana biyu bai zo ba kuma bai kira ba."

Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Abinda ya kawo ni kenan. Nima na rasa gane kan sa. amman ina son ki tayani tambayar ta me yake faruwa a tsakanin su ki tambaye ta ko fada sukai duk yadda kukai ki fada min. Ki bani nunber ki sai na kira naji."

"Bani da waya sai dai na baka number ta."
"No!
Ya fada ya zura hannu a aljihu ya zaro wata karamar waya ya mika mata yace
"Ki rike wannan zamuyi magana please k tabbata kin gano mana menene kinji kanwata."
Amsa tayi yace
"Insha Allahu nagode."

Ya juya ya koma motar sa ya bar wajen gida ta shiga. A daki ta samu Halima kwance na rawar sanyi da sauri ta karasa wajen ta tana fadin
"Lafiya me yake damun ki."

"Sanyi nake ji Hajara samon abun rufa please."
Mikewa tayi ta mika mata abun rufa sannan ta dauko mata paracetamol da ruwa. amsa tayi ta sha sannan ta koma ta kwanta. Bata jiima ba bacci ya dauke ta.

Zama Hajara tayi ta zubawa Yayar tata ido. Ta rame duk bata da nutsuwa. Lallai akwai wani babba tsakanin ta da Isma'il. Yadda Isma'il yake son ta da damuwa da ita amman yanzi ba kira bare yasan a halin da take. Lallai zata taimakawa yar uwar ta ganin komai ya tafi dai dai. Zata bawa Kabir gudunmawa lallai kuma Kabir me son Anty Halima ne tinda har yake son mahance matsalar yayar ta yake son ya cire ta daga damuwa.

"Allah na roke ka ma magance wa Anty Halima abinda ke damun ta."
Ta fada tana gyara mata rufa.

"Hajara! Hajara!!"
Umma ta kwada mata kira tana daga tsakar gida.

"Na'am!"
Ta fada a hankali dan kada ta tashi Haliman.

A tsakar gida ta tadda ta tana ruden tuwo tace
"Me yake damun Halima ne Hajara?"

"Yanzu dai na shiga tace min sanyi take ji na bata magani tasha ta fara bacci"
"Allah bata lafiya."

"Amin!"
"Amman fa na lura tana cikin damuwa!"

Shiru Hajara tayi. Umma tace
"Me kike tunanin yake damun ta kwana biyu sam bata da kuzari ga damuwa kwance a fuskar ta."

Shiru Hajara ta karayi. Ummah tacr
"Na gane rayuwa Hajara a da na biyewa kawa ta kaini ta baro ni a yawon bara na rasa ya'ya na guda biyu daya an kade shi da mota daya kuma an sace shi dana tashi ganin sa ba wasu sassan jikin sa. Hakika nayi wasa da rayuwar ya'ya na ban zauna ba bare na gane damuwar ku. A da komai kuka kwaso ni kuke fadawa amman a yanzu na gane baku sanar dani komai kuma ba komai ya jawo hakan ba sai rashin zama na. In na fita tin safe sai dare."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now