Chapter 1 page 70

172 23 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 7⃣0⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Ana magariba ya kira ta cewar yazo. Hijab ta saka ta mike Anty Fauziyya tace
"Zo nan ko yar hoda?"

"Anty ai dare ne"
Jaka ta mika mata tace
"Maza shafa."

Sannan ta dauko turare ta bata. Amsa tayi ta shafa tace
"To sai kin dawo."

"Aha!"
Ta fita yana ganin ta ya shigo soron wayar sa ya dauko ya fara haske ta,  kai tayi kasa dashi tace
"Ina yini?"

"Lafiya lou ya kike ya gidan?"
"Alhamdulillah!"

"Masha Allah!"
Ledar hannun sa ya mika mata yace
"Gashi ba yawa!".

"Nagode!"
"Good!"

"Gobe zan tafi Baby sai kuma na dawo zanyi kewar ki."
"Hmm nima haka!"

"Da gaske?"
Kai ta gyada. Yace
"Naji dadi."

Tai murmushi tace
"Nima yau zanbi Anty na zamu dagin mijin ta."

"Masha Allah sai yaushe zaku dawo?"
"Nima ban sani ba."

"Ba matsala mana communication in ta kama nazo nan din ma zaki ganni."
"Gidan mutanen?"

"To ba wajen matata zan zo ba."
Tai murmushi.

*
Muhammad da Khaleel yini sukai suna yawo a garin neman gidan su Sakina. Anan kasan layin su Sakina sukai sallah. Sannan suka fito ya fara kallon unguwar yace
"To ni ban sani ba ko wrong address ta bani."

"Gaskiya dai ina tunani."
"To nagode!"

"Ba matsala yanzu sai gobe kenan nima zan tafi gida."
"Oh shigo to na sauke ka mana."

"Ai ba nisa can layin zani fa zan dauko matata sai mu tafi gida."
"Oh muje ba sai na sauke ka ba."

"kar mu bata maka lokaci fa."
"haba ba komai sai kace zani wani waje yanzu faaki zan koma kawai."
"Shikrnan nagode."

Suka shiga ya nuna masa suka isa layin su Sakina. Parking yayi inda yace yayi ya fita ya nufi kofar gidan su sakina.

*
Hafsat na ganin Muhammad ta karasa tana fadin
"Yaa Muhammad sannu da zuwa."

"Yauwah Hafsat."
Ya mikawa Ahmad hannu suka gaisa yace
"Kice tazo mu tafo kuma naga kina zance ai."

"Oh shine mijin Antyn tamu ashe yayan mu ne."
Suka kara gaisawa. Ahmad yace
"Ai nima tafiya zanyi je ki mata magana."

Ta juya ta shiga waje suka fito tare. Khaleel dake mota yana tunani Muhammad yace
"Fito ku gaisa mana."

Kamar kar ya fito ya fito suka gaisa. Hafsat ta dawo tace
"Yace kazo kuyi sallama da Ummah."

"Toh!"
Ya kalle su yace
"Ina zuwa."

Sannan ya shiga gidan. Sallama sukai da Ummah tai musu addu'a. Sannan Sakina da Hafsat suka fito har da Halima dan yiwa yayar tasu sallama.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now