Chapter 1 page 92

204 13 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 9⃣2⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

*
Da daddare sukai waya da Sakina ya fada mata sai da gaban ta ya fadi dan tsoro. Tace
"Khaleel Momy ta yadda ne?"

"Momy zaki aura ko ni?"
"Kai!"

"To shikenan ni na yadda na aminta."
"To Allah kaimu."

"Amin. Gobe zan kara ganin Baby na."
"Uhmm!"

Haka yai ta janta da hira amman ina hankalin ta sam bai wajen yana ga tunanin irin zaman da zasuyi da sirikar ta. Duk sai taji ta damu da wanne ido zata kalle ta. Anya kuwa batai wauta ba na aminta da auren Khaleel.

Yaya Fauziyya ce ta shigo ta tsaya kallonta amman bata ma san ta shigo ba. Zama tayi a kusa da ita ta cire mata tagumin tace
"Tunanin me kike?"

Juyowa tayi fuskar ta cike da damuwa tace
"Tayaya zan kalli sirika ta da wanne ido."

"Shine zaki damu. Shawara daya zan baki ki rike Allah irin matan nan ba haka suke zaune ba sannan ki kalle ta da daraja a matar mijin ki daga haka kada wata mu'amala ta hada ku ki girmamata tinda mijin ki na son ki ai shikenan."

"Haka ne nagode Yaa Fauziyya."
"Kada ki damu."

Tai mata murmushi tace
"Mai gyara gobe zata zo zata ga me kuke bukata kan ta dawo ta fara gyara ku."

"Allah kaimu amman kin fada mata..."
Sai tayi shiru fauziyya tai murmushi tace
"Na fada mata ku zawarawa ne zaku sake aure a gyaran ku sosai"

"Mungode Anty Fauziyya ba wannan a tsakanin mu."
Ta mike tace
"Bari naje na kwanta kaina ke ciwo."

"Ayyah sannu Anty ciwo ciwon nan ba zamu je asibiti ba kuwa?"
'Me za ayi daga ciwon kai."

"Ni gani nake ko dai an harbu!"
Dakuwa tai mata tace
"Gidan ku."

"Tai dariya tace
"Allah inganta."
Ta juya ta fita.

*
**
***
Soyayya suke sha Hafsat da Ahmad dan da ya tafi kamar kara shakuwa aka saka musu ko agun aiki tare suke yini makale da juna haka da dare dan sai ta taka masa birki sannan yake barin ta.

Haka ma Khaleel baya sati bai zo ba soyayya suke sha mai tsafta da fahintar juna abinsu.

Duk soyayyar Hajara da Sani tafi ta kowa burgewa domin Hajara yarinya ce karama mai kunya. Gashi Sani na masifar son ta da kaunar ta. Sai doki yake da son kasancewa da ita domin kuwa ba karamin son ta yake ba itama kuma tana son abun ta.

Halima da Kabir kuwa sun shaku sosai da junan su. Dan ko da yaushe zai kira ya take ya ka me take so ko ya aiko mata da abu in ya samu dama yazo su gaisa. wanna yasa ta kara sakewa dashi ta dauke shi a matsayin yayan ta. Sai take jin wani abu daban akan sa har take jin ina ma shi ne yaso ta a baya ba Isma'il ba.

Son da yakewa Halima bai sa ya kasa bawa Sadiya kulawa da nuna mata so badan bazaka taba cewa ita tace tana son sa ba. Dan yadda yake bata kulawa sun aminta da junan su sosai su kuma yadda da junan su.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now