Chapter 1 page 105

223 19 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣0⃣5⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Ciki ta shafa yace
"Yunwa ko?"
Kai ta gyada ya kamo ta yace
"Muje ki karya kinji."

Kafada ta make tace
"Kaje Kai wanka sai mu karya tare."
"Kada na Dade fa."

"Ba matsala."
Ta Kama hannun sa ta Kai shi bakin kofar bandakin ya juyo ya kalle ta ta sakar masa murmushi. Ya shige ta hau gyara gadon kan ya fito har ta gama ta fito Masa da Kaya ta fita. Yana fitowa a gurguje ya shirya ya fito a falo ya same ta ta mike tace
"Kayi kyau Deedat."

"Kinfi ni kyau Baby."
Tayi murmushi yace
"Muje ko?"

Tare suka karasa ya dinga bata sai da ta koshi shima yaci sannan ya Bata magani ya fita wajen Hanna.

A falo ya same ta sanye da kayan Bacci tana Shan tea da bread da butter tsabar kwiwar Hannah ko Abu a cikin ta ba zata iya dafawa ba duk da Yana so.

Zama yayi tace
"Ina kwana?"
"Lafiya kin tashi lafiya?"

"Alhamdulillah ya me jikin?"
"Da sauki."

Ya mike yace
"Ba wata matsala?"
"Babu."

"Ok!"
Ya zaro kudi a aljihu ya dire Mata ya fita. Yana Shiga ya juyo Hafsa a kitchen tana aiki.

Har tayi wanke wanke tana yanka carrot. Ya karasa ya amsa Yana Taya ta, ta dauko kaza ta gyara. Tare sukai girkin Rana tayi fried suppegette da pepper chicken sai lemon pineapple.

Karfe daya da Rabi ta Gama suka ci abincin su. Biyu ya tafi masallaci bai dawo ba sai wajen uku lokacin har ta Yi cin cin Yana shigowa ya same ta tana ci da lemo ya zauna ya dauki daya ya ci yace
"Uhmm Dadi."

Tai murmushi haka suka cigaba da hirar su. Sai da akai la'asar ya fita Bayan ya sanar mata ba zai dawo da wuri ba. Haka yaje ya fadawa Hanna.

Har biyar da Rabi bai dawo ba wannan yasa ta Kira sa a waya Yana dauka tace
"Deedat yayi Nisan kiwo."

"Wallahi gani Nan."
"To Allah kawo ka lafiya me Zan dafa maka?"

"Tuwo nake so miyar yauki."
"An gama sai ka dawo."
Ta kashe wayar ta Shiga kitchen Tai Masa tuwon semo miyar kuka ta hada Masa lemon ginger ta ajiye.

Wanka ta Shiga tana fitowa ana magariba ta tada Sallah sai da tayi isha'i sannan ta mike ta shirya cikin wani Riga da wando tayi parking kan ta ta fito dashi sai tashin kamshin take.

Karar motar sa yajiyo ta fita da sauri ta tsaya ta taga ta ga ya fito ya nufi bangaren Hanna. Bai jima ba ya fito yayo bangaren ta.

Buya tayi a Bayan labule ya shigo da sallama Yana fadin
"Baby na."

Har ya zauna sai ya mike yayi dakin ta ba kowa ya duba toilet Nan ma haka fitowa yayi ya Shiga dayan dakin Nan ma haka sai da ya duba duka gida Bata Nan ya shiga kitchen Nan ma haka kofar fita yayi ta fito ta Dane bayan sa.

Ya saki ajiyar zuciya Yana fadin
"Shine Kika biyar min."
"Sannu da zuwa."

Ya juyo da ita yana kallon ta sai ya rumgume ta Yana fadin
"I miss you my Love."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now