Chapter 1 page 86

205 14 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 8⃣6⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

*
Sakina ce kwnace a dakin ta tana waya da Khaleel yace
"Baby kewar ki tai min yawa sosai."

"Haba Khaleel naga gobe fa.muna tare ya kamata kewar na ta kyale ka haka."
"Wallahi gani nake lokaci ya min yawa. Tsayi yake."

"Kai Khaleel?"
"Wallahi da gaske nake My love."

"To ka kwantar da hankalin ka a sannu gibe zatayi insha Allahu mu gadu da juna."
"Allah ya yadda kamar na janyo lokacin wallahi."

"Ina Momy?"
"Tana nan."

"Tasan zaka zo."
"Eh na fadawa Dady ya fada mata dazu take min maganar."

"Ka gaishe min da ita."
"Zata ji."

"Dare yayai bari na kwanta."
"Ya kamata kam. Good night."

"Sweet dreams!"
"Aha thanks!"
Ta kashe wayar tayi addu'ar bacci. Bacci ya dauke ta.

*
Washe gari Ahmad yana dawowa daga masallacin asuba ya wuce dakin ta.  A kwance ya same ta da alama ma batai sallah ba.
"Hannah! Hannah!!"

Juyi tayi tace
"Uhmm!"

"Ki tashi kiyi sallah har an idar fa."
"Yaya ka bari anjima nayi"

Dagota yayi ya tsayar da ita akan kafar ta. Ido ta fara mutsikewa yace
"Jekiyi alwalar."

Ta turo baki ta shige ta dauro alwala tazo ta tada sallah ranta a bace idar ta mike zata hau gado. Yace
"Kin hada kayan ki ne?"

"Haba Yaya tin yanzu?"
"Karfe bakwai zan fita in kina son zuwa ki hada kayan ki in kuma bakya so shikenan"

Yana fada ya mike ya fita. Ba dan tana son zuwa ba da ba inda zata bishi to tin da tazo ko sau daya bata je kano ba. Ba yadda zatai tana jin bacci ta mike ta hada kayan ta. Ta shiga tai wanka ta fara shiri.

Yana komawa wanka yayi ya saka kayan sa. Tea kadai ya sha ya zauna yana hada abinda yake bukata. Karfe shida da arbain ya gama ya fita da akwatin sa ya saka a mota. Dakin ra ya shiga ya same ta ta shirya kwance tana bacci.

"Hannah! Hannah!!"
Ido ta bude yace
"Tashi mu tafi"

Mika tayi hadi da hamma sannan tace
"Ban karya bafa."
"Baki shirya tafiya ba kenan."

Ya fada yana mikewa. Ta mike da sauri ta dauki mayafin ta ta fara jan akwatin ta da sauri ta fita ta same shi a mota. Jakar ta ajiye ta koma ciki. Kitchen ta shiga ta debo dankalin da aka soya ta hado tea tana jin horn din sa dan ta diba a guje.

Tana shiga ya tada mota. Suna tafe ta gama.cin dankalin ta ta sha tea din ta sanan ta gyara kujera tayi kwanciyyar ta bacci mai dadi ya dauke ta. Haka suka yi tafiya tana bacci shi kuwa suna waya da Hafsan sa. Har sai da suka iso gida sannan ya tashe ta. Tana bude ido ta ganta a gidan su.

Fuska ta bata tace
"Yaya na zata gidan Mami zamu fara zuwa?"
"A'ah!"

Ya fada ya fita yana shiga ya wuce dakin sa. Kwanciyya yayi dan lokacin goma na safe take bacci ya dauke shi. Hannah kuwa tsaki tayi ta fito ta dauki jakar ta tayi dakin tata ajiye ta haye gado ta cigaba da ramuwar baccin ta.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now