Chapter 1 page 32

257 14 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 3⃣2⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*
*






Kuka sosai Halima take Isma'il na rarrashinta, ji tayi ta tsani kanta tana kuma jin haushin Isma'il, ga wani irin tsoro da takeji, dakyar ya shawo kanta, tayi shiru tashiga bandaki dan ta tsarkaka jikinta.

Falo Isma'il ya dawo yana wani irin shu'umin murmushi, dan shi kadai yasan dadin da yaji, gaskiya Halima tayi.

Halima tana fitowa Daga bandaki kayanta ta mayar still a lokacin kuka takeyi, ta nufi sallaya dan ta rama sallar, dan yanzu shida da rabi, Sallah tayi batada nutsuwa, a haka tayi sallarta, ta koma tayi sujjada, tana rokon Allah ya yafemata, a haka ta shafa adduar tana nadamar biyewa Isma"il datayi.

Falo ta fito ta samu Isma'il a zaune, ko kallon inda yake batayi ba ta dauki Jakarta tayi hanyar waje. Isma'il gabanta yasha da sauri ya durkusa har kasa yana fadin
"Baby am sorry bazan sake ba please."

"Naji!"
Ta fada tana kokarin wucewa ta gefensa. Rigarta ya riko yace
"Please?"

Fizge rigar ta tayi. Ta wuce abinta.
Tana fita ya mike yana tabe baki, yana wani murmushi sannan yace
"zama ki dawo ne dani kike zancen Halima."

Tana hawa adaidata hawayen da take ta boyewa ne suka zubo mata nan ta kifa kan ta akan cinya ta dinga kuka.

Wayar sa dake kan kujera ya dauko, dan ya kira Kabir har yayi dailing yayi sauri ya katse, dan ba karamin warning, Kabir yai mishi ba akan in yaje yagama iskancinsa kar yakara tunkarinsa da zancen, bama kuma akan Halima da ya kafa masa doka.

Kiran Kabir ne ya shigo wayarsa, ya daga yace
"Ya akayi naga kamar kiran ka ya shigo yanzu ya katse."

"No wlh bansan na kiraka ba, wayar na cikin aljihuna."
Isma'il ya fadi yana inda inda.

Yaji shine amman yasan ba gaskiya ya fada ba tayaya waya a aljihu zata hau kiran sa. Sharewa yayi yace
"Ya Halima ne?"

"Tana lafiya."
"Ok meyasa baka shigo kasuwa ba yau."

"Ban jin dadi ne."
"Ok!"

Ya kashe wayar. Kawai ji yayi bai yadda da Isma'il ba anya ba Halima ya kara kira ba kuwa yasan halin Isma'il da bin mata kamar dan akuya.

Shi har yanzu fa yana tsoron Isma'il da Halima dan yasan waye Isma'il, yasan in yana son abu to sai yayi yadda yayi yaci riba akan abun nan. Bama Halima dole ya tsairatar da ita daga cigaba da fadawa tarkon Isma'il har sai abinda yake so ya tabbata wato mahaifin ta ya yadda Isma'il ya aure tan.

Duk da yana son Halima amman zai sadaukar da son da yake mata dan samuwar farin cikin ta. Dan yasan farin cikin ta shine samun Isma'il dan ya yadda da yadda take son Isma'il har cikin zuciyar ta. Dole ya dage da addu'a ko dan Allah bashi ikon yin wannan sadaukarwa. Zai ta addu'a akan Allah ya cire masa son ta.

Halima tsabar kukan data sha ya haddasa mata ciwon ka, ,bata Iya Daga kanta ji take kamar kanta ba ajikinta yake ba. Tana kwance ta kasa tashi tayi sallah magariba sai da kyar ta mike tayo alwala ta yi a xaune dan yadda kanta ke ciwo.

************************************************************************************************************************************
Rakasu yayi ya dawo ya tadda ita tana zaune. Baki ya tabe yayi dakin sa. Wanka yayi ya saka jallabiyya sannan ya dawo falo. Tana zaune a inda take.
"Je ki dauko plate da cups."

Fuska ta shagwabe tace
"Amman fa Yaa Ahmad ba haka ake ba."

Dagowa yayi a fusace sai dai yana kallon ta yaji ya kasa fadan sai cewa yayi
"Yaya ake yi toh?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now