Chapter 1 page 101

205 15 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣0⃣1⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Da ta farka ta same shi zaune a dakin ta lumshe ido ya mike ya karaso ya kama hannun ta yace
"Sannu My love!"
Kai ta gyada kawai dan da ta bude ido hawaye ne zai zubo,  juyo da fuskar ta yayi yace
"Bude idon mana."

Bata motsa ba yace
"My life!"
A hankali ta bude idon ta dake cike da hawaye ai kuwa take ya wanke fuskar ta ya hau zube yace
"Ya salam kuka kuma."

Nan ya hau goge mata fuska zatai magana Sadiya ta shigo dakin rike da katon plate da ta dauro fulas fulas na abinci. Ajiyewa taui ta karaso tana fadin
"Jikin ne?"
Goge hawayen yayi yace
"A'ah!"

"Ok. Sannu!"
"Yauwah."

"Ga abinci fa."
"Ni na koshi."

"A'ah ki kada ci ko kadan ne."
Kai ta girgiza. Sadiya tace
"Ko sai anjima."

Kai ta gyada. Ta kalli Kabir tace
"Kai fa?"
"Nima sai anjima."

"Ok bari naje."
"Ina zaki?"

"Daki."
"Me zakiyi?"

"Ba komai "
"To xauna kawai."

Kallon Halima tayi ta zauna  mikewa zaune tayi Halima sai ta dafe kan ta Kabir yace
"Sannu!"
Kai ta gyada ta mike ta shiga daki kan gado ta kwanta take kuma wani baccin ya kara dauke ta.

Kiran sallah magariba ne ya tashe ta ta mike tayi alwala sannan ta shiga tayi wanka tare da dauro alwala. Ta fito ta saka doguwat riga ta tada sallah tana idarwa ta fita falo ba kowa dan haka ta koma daki ta dauki alkurani tana karantawa. Tana zaune akai isha'i shima ta mike tayi sallah ta zauna tana addu'a.

Ta daga hannun ta sama tana kai kukan ta ga rabil Alamin aka budo daki bata dago ba ta cugaba da addu'ar ta har da hawaye a idon ta. Shafawa tayi sannan ta rufe alkur'anin gaban ta ta maida wajen da yake sannan ta juyo. Yana tsaye a bakin kofa ya shigo ya durkusa a gaban ta yace
"Dan Allah na rokeki ki daina kukan nan da saka damuwa kukan ba menene to?"

Yana fada ta fashe da wani kukan da sauri ya mike ya kamo ta yana lallashinta yace
"Please kiyi hakuri kinji?"
Kai ta gyada ya goge mata hawayen sannan ya mike ya fita. Kwanukan da Sadiya ta kawo ya kwaso ya shigo dasu ya ajiye sannan ya dauko ledar da ya siyo musu nama da fura ya dauki na Sadiya yace
"Ina zuwa."

Ya mike ya fita. Bai jima ba ya dawo ya kamo hannun ta ya zaunar akan karfet ya zuba mata abinci sannan ya dauki spoon ya bata,  amsa tayi kadan taci tace ta koshi ya bata nama da furar ta sha furar naman biyu taci tace bata ci. Magani ya bata ta sha sannan yaci abincin bayan ya gama ya kwashe kwanukan wanka yaje yayi ya saka kayan bacci sannan yaje yaiwa Sadiya sai da safe. Dakin Halima ya shiga ya same ta a gefen gado yace
"Ya jikin?"

"Naji sauki."
"Allah kara sauki ni zanje na kwanta sai da safe!"

Kallon sa ta tsaya yi har ya juya ya juyo yace
"Menene?"
Kai ta girgiza kawai. Ya juya ya fita ta koma ta kwanta hawaye na bin fuskar ta. Bacci ne ya dauke ta sai wajen uku ta farka tayo alwala ta tada sallah tana zaune tana lazumi har aka kira assalatu. Kabir ya shigo dakin ya same ta akan sallaya. Juyawa yayi yaje ya tashi Sadiya sannan ya tafi masallaci. Tana idar da sallah tayi azkar sannan ta shiga kitchen. Shigowa yayi yana jin motsin ta a kitchen ya shiga.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now