Chapter 1 page 103

159 13 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣0⃣3⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Washe gari ya Kai ta gida shi Kuma yaje gida anan Dady yai Masa maganar Hanna. Ahmad yace
"Ni Dady ban Kore ta ba duk sanda tayi niyyar ta koma kofa a bude take Amman ta sani ba Zan dauki abinda tayi min a da ba."

Nan ka Kira Hanna ya fada Mata dole ta Yi biyayya dashi ta amince wanda Mami tace gobe zata koma Ranar suka tafi ita da Basma suka gyara sashen ta sannan suka dawo.

Zuwan Hafsa gida ta sha mamaki domin duk wata sai Ahmad ya Kai kayan abinci gida Banda kudi Kuma Sam bata sani ba baya fada Mata.

Hakan Yaa Muhammad da Khaleel da Kabir Dan haka gida yanzu kayan abinci har yawa yake musu ga Wansu Fauziyya ta dashi a makaranta duk yaran ta maidasu private Mai kyau ga sutura suna zaman su lafiya. Umma tana business din ta.

Sai dare Ahmad yazo ya dauke ta duk sai taga ya sauya suna shiga ta wuce Tai wanka ta fito ta shirya cikin kayan Bacci. Falo ta same shi ya zuba tagumi ta Shiga jikin sa ta kwanta tace
"Me yake damun miji na?"

"Baby I love you."
"I love you more. Kullum kwanan duniya kana Kara samun sonka yau naje gida Naga abun alherin da kake Allah saka da Alheri Allah Kara budi kaima Allah Baka Mai maka. Allah ban ikon maka biyayya har karshen rayuwar mu. Nagode nag..."
Hannu ya daura Akan bakin ta yace
"Bana son godiya Baby addu'ar ta wadatar Allah miki albarka."

"Amin Amman me yake damun miji na."
"Yau naje gida mun zauna dasu Mami da Dady har da Hanna!"

"Shine me?"
"Gobe zata dawo."

Kai Masha Allah Amman naji Dadi wallahi Allah ya bamu zaman lafiya."
"Murna ma kike Yi?"

"Eh Mana My Deedat zai samu kulawa fiye da tawa ko?"
"Baby nafi son zama dake akan da......"

Hannu ta daura a bakin sa tace
"A'ah Deedat kada ka Fadi haka duk mu matan ka ne. Kai Mana addu'ar zama lafiya kawai Kai Kuma kayi adalci."

"Allah Miki albarka."
"Amin!"
Ya rumgume ta.

Washe gari Hannah ta dawo da dare. Ahmad ya Tara su a dakin Hannah yai musu nasiha sannan yace
"Bana son fada duk matanane ku hade kan ku."

"Insha Allahu Yaya."
Hanna ta fada.
Hafsa tace
"Insha Allahu."

"Allah muku albarka."
"Amin!"

"Kwana nawa za anayi to?"
Ya kalli Hanna tace
"Kwana biyu!"

Ya kalli Hafsa tace
"Duk yadda kuka ce!"
"To ayi kwana biyun."

"Toh."
Yace
"Yau a dakin Hannah nake kenan ko?"

Kai Hafsa ta gyada tace
"Allah hade kanmu."

"Amin!"
Sannan ta mike tace
"Sai da safe."

"Allah bamu alheri."
"Amin!"

Ya kalli Hanna yace
"Bari na raka ta."
Suka fita tana Shiga tace
"Ka koma Deedat."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now