Chapter 1 page 3

516 35 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 0⃣3

*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

Zaune yake a kofar shagon sa, wanda yake na provision ne duk da ba wasu kaya ne masu yawa can ba amman akwai kayan ba laifi. Don dashi yake rufawa kan sa asiri da mahaifiyar sa

Kyakyawa ne ajin farko, don fari ne dogo ga hanci yana da manyan idanu ɗan gayu da shi mai tsafta. Ba zai wuce shekara ashirin da bakwai ba zuwa da takwas don bai kai shekara talatin ba.

Sam ba zaka ce bai da shi ba don yadda yake cikin gyara da tsafta zai saka kayan sa masu kyau, kuma ya shafa turaren mai dadin kamshi.

Yana karatu anan Federal college of Education Kano yanzu haka sun fito Teaching practics wanda da sun dawo zasuyi second semester sun gama.

Yana daga kofar shagon nasa ya hango su ita da ƴan uwan ta, ƴan mata biyu wanda suka girme ta sai ita sai mai bi mata da yayen ta maza biyu suma sai wani karamin su. Wanda kullum suke shigewa ta kofar shagon nasa in zasu isilamiyya ko sun dawo. Dukkan su sanye suke cikin uniform dinsu sky blue karamar cikin su ce sanye da nikaf da safar kafa.

Dukkan su kyawawa ne bafulatanai dasu, wacce yake kalla ta ukun su ce, itama fara ce tas mai kyau da ita. Sam bai da dabi'ar kallon mata, amman inda zai hange su sai ya kalle su, wanda in har ya daura idon sa akan ta sai yaji kirjin sa ya buga, wanda yake rasa nutsuwar su har sai sun bacewa ganin sa sannan zai daina kallon inda suke.

Yaran suna da tarbiyya don sam baka gansu suna fada ba ko suna kula mutane a hanya ba sa kule kulen mazan nan. A nutse zaka gansu sun fito kuma a haka suke komawa gida.

Yanzun ma da kallo ya bisu har suka bacewa ganin sa sannan ya sauke wata ajiyar zuciya tabbas yanzu ya yadda ya kuma gane son yarinyar yake, wacce bai san sunan ta ba amman yasan gidan su don yar gidan Alhaji Ibrahim ce, duk wanda ke unguwar yasan da gidan don mahaifin su ɗan boko ne duk da yanzu ya yi ritaya mutum ne mai ilimi dukka biyun da sanin ya kamata da dattako da mutunci da tarbiyya don ya'yan sa ma yana kokari akan su sosai ba inda suke zuwa daga makaranta sai makaranta sai kuwa zaman gida. Ba wani mai kudi bane sai dai akwai rufin asiri wanda yanzu yake harkar kasuwanci kuma abin ya amshe shi sosai.

Matansa biyu Hajiya Binta ita ce uwar gida, mahaifinta yana da kudi sosai auren ta da Alhaji Ibrahim ya faru ne don d'an abokin mahaifin ta ne, ta tsani talaka, sam bata kaunar talaka, don ko harka da talaka babta yi ya'yan ta uku, Sailuba ce babba wacce take yar shekara ashirin da biyu sai Alkasim ɗan shekara ashirin sai autar ta Rukayya mai shekara goma sha tara.

Sai matar sa ta biyu Hajiya Amina mai hakuri da ilimi don malama ce tin tana budurwa ta haddace Alkur'ani, mahaifin ta ma malami ne, haka a fannin boko ma ta yi karatun ta zuwa NCE gata da amfani da ilimin ta. Ya'yan hudu Zainab mai shekara ashirin da daya sai Abdullahi mai shekara sha tara sai Ummulkursum mai shekara goma sha bakwai sai Autan ta Ibrahim da suke kira da Khalil wanda shekarar sa goma sha biyar.

Sam ba zaman lafiya a tsakanin su don Hajiya Binta bata son Hajiya Amina, haka ta daurawa ya'yan ta tsanar su Hajiya Amina, wanda a ciki Rukkaya ce kadai bata da wannan halin ita tana son ƴan uwan ta. Don babbar su Sailuba ko gaisar da Hajiya Amina ba ta yi, Rukayya kuwa kamar ƴar dakin Amina don kullum tana dakin ta bacci ne kadai ke kaita dakin su duk yadda uwar ta ke fada har ta fara gajiya sai tace ta asirce mata ƴar ta.

Rukayya da Ummulkursum tare suke duk da ta girme mata amman komai tare suke yi, Rukayya na SS 3 ita kuma Ummulkursum tana SS 1, inda Zainab da Sailuba suke university level 300 Abdullah da Kasim kuma suna level 100 sai Kasim dake JSS 3.

Komai na Ummulkursum da Rukayya daya ne, sai dai banbancin halaiya. Don Ummulkursum ita ta dauko dabi'un mahaifiyar ta, don haka ita tana da sanyin hali ga hakuri don ko a islamiyya ajin su ɗaya da Rukayya sun sauke suna maimaici ne kan ayi bikin sauka. Akwai ta da kula da addini don ko da yaushe cikin hijab da nikaf take har da safa.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now