Chapter 1 page 26

262 17 0
                                    


*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 2⃣6⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*
*




"ina dashi amma......"
"amma mei? bakada hujja har awajen Allah ka gwamace kayi ta sabon Allah, Isma'il ba kasan mata nawa ka lalata ba, kasan mata nawa ka budawa ido suke aikata zina, ko kasan girman zunubin da kake aikatawa kuwa, inkasan kana da sha,awa kayi aure mana, amman bazakayi ba ka gwamace kai ta lalata, ya'yan mutane, Shin ka manta duk abinda kayi sai an maka kana da kanne zakai aure za kuma ka haife shin in su akai wa haka zakaji dadi."

Kai ya girgiza yana jin abokin nasa. Kabir yace
"A gaskiya Isma'il abokanta ta da kai tazo karshe dan ba zan zauna da mutumin da ba zan fada masa yaji ba. Kuma kowa yasan ka nima da halin ka za ana kallo na dan haka ba zan iya cigaba da abokanta da kai ba."

"Haba friend u know dat I can't leave without u!"
"In har kuwa haka ne sai dai in zaka bu sharadi na if not wallahi Allah Isma'il bani na kai"

"Menene sharadin?"
Isma'il ya tambaya.

"In har kana San in cigaba da abota dakai, u have to make a promise to me, zaka auri Halima, now tunda kai kafara sanin ta ya mace."
"But her father will not get her marriage now!"

"I know but it's a promise duk lokacin da Baban ya yadda zaka aure ta."
"Naji kayi hakuri ka yafen!"

"Ba kai min laifi ba friend. Allah zaka nemi yafiyar sa da Halima"
Kai ya gyada.

Wayar sa Kabir ya ja yana dane danne. Isma'il yace
"Ya naga kana hade rai to."

"Kar na hade? Isma'il baka taba batan rai kamar yau ba."
"Haba friend ba mun aje matter ba."

Kafada ya dage kawai. Nan Isma'il ya dinga jan sa da hira ammn sam ya kasa sakewa dan zuciyar sa a kuntace take ga zafi ga kishi ga tausayin Halima.

***** **** *****
Halima kuwa sai da aka kira magariba ta tashi da wani  ciwon kai wannan yasa ta mike a daddaf ta shiga tai wanka ta dauro alwala ta tada sallah. Tana idar wa taji vibration din wayar ta janyowa tayi tana ganin Isma'il ke kira taki dagawa. Da ta tsinke ma taga misaed call nasa yayi twenty, tsaki ta saki tana shirn ajiye wayar ya kara kira kin dagawa tayi da taga zai dameta ta kashe wayar gaba daya dan wani irin haushinsa takeji.

********************************************************************************************************************************************************
Muhammad kuwa yana yawan kiran Abba su gaisa dashi dan so yake ya amshi Number Ummu amman yana jin nauyin tambayar Abba. Wata rana da sukai waya da Abba bayan sun gaisa yake cewa
"Abba ya mutan Abuja?"

Abba yace
"Suna lafiya ai Ummun ma bata dade da zuwa ba ta koma ma."

"Allah sarki!"
Can zasuyi sallama yace
"Abba ina bukatar Number wayar Yaa Suleiman!"
Nan Abba ya tura masa.

A haka ya fara jin soyayyar Ummu bama in ya zauna yana tunanin abubuwan da Ummu tai masa wanda yake kara jin son ta. Ta tausaya masa a rayuwa ta kaunace sa shi da iyayen sa to shikan me zai yi in ba ya saka mata da soyayyar sa ba. Ga alherin mahaifin ta da mahaifiyar sa agareshi. Tabbas Ummu ta cancanci ya so ta fiye da komai.

In yana tuna surar ta kuwa sai yaga Ummu bata da aibu sam dan a kyau kamar larabawa take. Ba ta da kiba tsayin ta dai dai gwargwado fara ce tas mai idanu da hanci mai fara'a ko da yaushe Gata a cike take daga saman ta har kasan ta. Ga kunya da tabiyya bata taba iya kallon mutum sai dai kullum kan ta akasa. Tabbas Ummu ta cancanci a so ta dan duk wanda ya samu Ummu kuma yasan ya gama dacewa.

Yakan kira Yaa Suleiman su sha hira abinsu dan sun saba sosai lokacin da Yaa Suleiman yaje umrah ma sun hadu. Yana son yai waya da Ummu amman bai da number ta kuma ya kasa cewa a turo masa. Sai dai in sunyi waya da Yaa Suleiman yace Yanzu Amaryar ka ta shiga daki ko ta tafi makaranta haka dai.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now