Chapter 1 page 45

218 21 3
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 4⃣5⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*


A cikin ma ba abinda take sai safa da marwa. Ta kasa samun nutsuwa bini bini ta daga kai ta kalli agogon dakin. Tin bayan la'asar suka fita amman gashi har magariba basu dawo ba. Ta kira Hajiya Ni'ima tace mata ai ko zama basu yi ba suka bar gidan.

Take taji ta rasa nutsuwar ta nan ta hau neman layin su amman sam bata shiga gaba daya layin nasu.

Sakina da Khaleel kuwa suna fitowa daga gidan Hajiya Ni'ima abokin Khaleel Marwan ya kira sa. Yana dagawa yace
"Yanaga baka zo ba?"

"Ina?"
"My birthday mana kada kace baka ga text."

"Wallahi ban gani ba bro ya za ayi kenan?"
"Malam ka taho kawai."

"Ok ba damuwa."
Ya juyo ya kalli Sakina da tin da suka fito batai magana ba.

"My love kin ji fa,  friend dina ke birthday please zaki rakani?"
Dagowa tayi ta kalle shi. Ya marairaice mata yace
"Please!"

"Ok but ai ban shirya ba."
Kallon ta yayi yace
"Menene da ke a hakan u re beauty ba abinda kik bukata more. But in kina son canja shiga muje a siyi wasu yanzu."

"No ka barshi kawai."
Kai ya girgiza yace
"Ina ai kuma sai an je fa."

A wani hadadden wajen sai da kaya yai parking sannan ya kalle ta ya fita. Xagayawa yayi ya bude mata kofa ta fito a hankali.

Kai daga ganin wajen kasan wajen masu kudi ne dan tin daga enterance din abin kallo ne har ciki. Shi da kansa ya zabar mata wani blue black gown mai sky blue stone. Sanna ya daukar mata cover shoe da vail.

Wani daki aka kai ta ta shirya ita kanta sai a ta tsaya kallon kan ra a mirrow dan tadda tai kyau kamar aljanna.a hankali ta fito daga dakin.  Tin da ya daura idon sa akan ta ya nemi komai nasa ya rasa. Har ta karaso bai sani ba. Dan sai da ta masa tafi sannan ya dawo cikin hayacin sa.

Murmushi ya saki yace
"Kinyi kyau Baby sosai."
"Thanks you!"

Fita sukai suka koma mota. Wajen party suka zarce waje ne da ya hada ya'yan manya masu ji da kansu. Sai rawa ake wasu na zaune suna hira da yan mata wasu na pictures haka dai.

Tana shiga wajen wani tsoro ya kamata dan bata taba zuwa waje irin haka ba duk abun ta. Dan haka a bayan Khaleel ta dinga buya.

Suna shiga wata kawar Khaleel Ase ta taho ta mika masa hannu. Hannu ya mika mata suka gaisa tana cewa
"Yaushe ka shigo kasar?"

"Sati na daya."
"Amman naji dadin ganin ka wajen two years rabona da kai fa."

Yai murmushi kawai. Sakina ta gani a bayan sa ta janyo hannun ta tana fadin
"Wow budurwar ka ce?"

Kai ya gyada yace
"Ita zan aura insha Allah."

"Wow amman tayi kyau kuma kun dace sa juna."
"Thanks!"

Marwan ne ya karaso sjna haduwa sukai side hug da juna yace
"Happy birthday Guy!"

"Thanks you!  Mu karasa."
Ya kamo hannun sa ya kai shi gu ya zauna dagowar da zai suka hada ido da Sakina.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now