Chapter 1 page 71

166 19 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 7⃣1⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Dagowa yayi yana kallon ta yace
"Sakina na sha wahalar neman ki yau kwana na biyar a garin nan kullum sai na zagaye unguwar nan ina cewa gidan su Sakina amman ban dace ba."

"Ina ka hadu da Yaa Muhammad?"
"A masallaci ina kukan rashin ki."

"Kuka kuma?"
"Wallahi kuka Sakina na rasa yaya zanyi to."

"Haba sai kace ba namiji ba."
"Namiji baya kuka kenan!"

"A'ah amman an san shi da juriyya ne."
"Tawa ta kare akan ki ni kadai nasan me nake ji. Amman alhamdulillah."

"Ya akai kazo nan to."
"Wallahi gida zan kaishi da matar sa shine Ashe Allah yau zan ganki."

"Ikon allah."
"Sakina meyasa kika kashe wayar ki kin tadan hankali na rasa nutsuwa da farin ciki kin zama rayuwata ban sani ba."

"Hmm sim din na karya shiyasa na manta ban dauki number ka ba."
"Saboda baki damu dani ba ko?"

"Ba haka bane."
"To yaya ne?"

"Kawia na manta ne."
"To ya kike ya bayan rabuwa?"

"Sai godiya."
"Masha Aah!"

Agogo ya kalla yaga tara tayi yace
"Dare Yayi My love zan koma masauki na gobe zan zo sai mu tattauna."
"Allah ya kaimu nagode."

"Amin i love you!"
Murmushi kawai tayi ya juya ya tafi. Ji yake kamar kar ya tafi amman dare yayi ga gajiyar da yayi.

*
**
***
****
*****
Yana komawa masaukin sa ya shiga yai wanka ya ci abinci sannan ya kwanta yana mai farin ciki baccin da ya jima baina shi yayi.

*
Karfe shida ya bar gida dan yana son ya zarce office. Ai kuwa karfe tara a office tai masa nan ya hau kan aiki da ya tarar masa ba laifi bai samu kan sa ba sai karfe daya da rabi yaje yai sallah ya dawo.

Waya ya dauka ya fara kiran Hannah wanda tin da ya tafi bata kira sa ba sai shi da duk safiya zai kira yaji ya take kuma da dare kan yai bacci zai kira yai mata sai da safe.

Dauka tayi yace
"Ya kike?"
"Lafiya and you?"

"Alhamdulillah!"
"Masha Allah."

"Nace miki yau zan dawo ko?"
"Eh Allah kawo ka lafiya!"

"Amin. Me kika tanadar min?"
"Ba komai!"

"Haba dai ki shirya tarbar angon ki."
"Uhmm sai ka dawo!"
Ta kashe wayar ta.

Yai murmushi ya fara neman layin Hafsat. Suna mota suna tafiya kiran ya shigo dauka tayi tace
"Ina yini?"

"Lafiya Alhamdulillah ya hanya?"
"Ai na jima da sauka."

"Masha Allah kace hutawa kake!"
"Wane hutu aiki dai baki san ko gida ban je."

"Ah haba dai sannu!"
"Yauwah. Ya hanya?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now