Chapter 1 page 88

176 14 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 8⃣9⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*


Kabir yaiwa Yaa Hafsat waya ya fada mata ranar zuwan su. Bayan sun gama waya ya kira Halima ta dauka nan suka gaisa suka taba hirar su sannan sukai sallama. Sadiya ya kira yana dauka suka gaisa sannan yace
"In nace xan turo gobe nayi wuri."

"Tayaya xance kayi wuri Kabir  Allah kaimu da safe sai na fadawa Abbi."
"To shikrnan ina fatan kina sane da ku biyu ne."

"Ba matsala zan fadawa Abbi."
"Nagide Sadiya."

"Nice da godya Kabir"
"Aah nine ni da ake so na."

"Aah ni dai ni da aka amshe ni"
Haka sukai tayi kowa yaki ya yadda har Abbi nata ya dawo ya leko ta wannan yasa tace
"Ina zuwa Kabir."

Ta kashe wayar ta mike tana fadin
"Sannu da zuwa."
"Yauwah ya gidan?"

"Alhamdulillah!"
"Ba dai matsala ko?"

"Babu Abbi amman ina son muyi magana."
"To!"
Ya zauna yace
"Ina jin ki."

Tace
"Abbi daman wanda yake so nane yake son ya turo gobe."
Sai ta rufe fuskar ta da hannun ta. Abbi yace
"To toh dan waye?"

"Nan taiwa Abbi bayani."
"Abbi yace
"to Allah ya kaimu."

"Amin amman Abbi mu biyu zai hada a lokaci daya."
"Ku biyu kuma Sadiya?"

"Eh Abbi!"
"Ke ba matsala a wajen ki ko?"

"Babu Abbi na aminta."
"To Allah yasa haka ne mafi alheri. Allah ya hade kawunanku."

"Amin Abbi nagode."
Ya mike yace
"Sai da safe."

"Allah bamu alheri."
Ya tafi ta dauki waya ta kira Kabir suka cigaba da hirar su.

*
Ranar da zasu zo kuwa Yaa Muhammad da Baba suka tarbe su. Suka zauna cikin gurma da arziki. Bayan gaishe gaishe. Uncle din Kabir yace
"To mu dai dan mu Kabir yaga yar ku kuma yana so munzo gaba daya zamu ba kayan komai da aure da saka rana sai kuyi bincike kan cikar lokacin in kunga ba wata matsala shikenan lokaci nayi sai a kawo laifi  da biki in da matsala kuma sai muce shikenan Allah haka nemafi alheri."

Baba yace
"To shikenan"
Nan suka dire komai sukace suna auren nan da wata daya. Yaa Muhammad yace
"ba matsala in mun bincika munga ba matsala zamu aiko da mun baku ita."

"Muna godiya amman ina fatan kunsan su biyu zai aura a lokaci daya ko?"
Yaa Muhammad da yasan da komai yace
"Eh ya sanar damu."

"To madalah!"
Nan sukai bankwana. Sai da suka tafi Baba yace
"Wanne bincike za ayi ai da an basun kawai"

"A'ah Baba abi komai a tsari itama Haliman tafi daraja a idon dagin mijin ta."
"To ai shikenan!"

Yaa Muhammad ya mjka masa kudin yace
"To Baba gasu"
"Ai da ka ajiye kan zuwan sauran ko?"

"Haka ne!"
Nan sukai sallama shima ya tafi. Gida ya koma yaiwa Fauziyya bayanin komai. Ya bata kudin ta ajiye. Tace
"Mungode Baby Allah saka da alheri."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now