Chapter 1 page 104

189 13 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣0⃣4⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*


Haka tayi ta fadi tana kuka, tana addua ganin zaman hakan bashine mafita agareta ba yasa ta mike ta shiga bandakinta ta tsarkaka jikinta, ta daura alwala ta fito, doguwar riga ta zura da zumar tayi sallah taji gaba daya batada nutsuwa tunani tayi gwara taje taga halin da Kabir ke ciki, ta fice daga dakin ta nufi dakin sa.

A lokacin Kabir na kan sallaya, yana jan carbi idonsa a rufe, ta tura kofar a hankali ta shiga, zama tayi a gefen sa, ta kira sunan sa
"Kabir"

Bude idan sa yayi ya zuba mata ido, tayi kasa da kan ta tace
"Dan Allah ka yafe min, nayi kuskure, dama abinda nake ta gudu kenan, shiyasa naki barin ka,  ka kusancen da farko, karka manta alkawari kayi min kace zaka manta abinda ya shiga tsakanina da Isma'il kace min ba jiki na kake so ba, amman meyasa...."
Ta kasa karasawa saboda kuka.

Ajiye carbin hannunsa yayi, ya rungumeta sosai, yace,
"Ban baro dakin ki dan haushin ki ba na baro ne saboda bana jin zan iya magana a wannan lokacin har na rarrashe ki,  kukan ki na konan zuciya bana so sam naga kina zubar da hawaye, hakika na tino Isma'il da halin da kuka kasance a baya saboda abinda naji a gareki ya wuce misali haka shima yaji,  dole ce tasa na tuno My Love,  ina son ki,  dole nayi kishinki,  kishin ki yasa  na tuna, bansan ya zanyi ba, ban taba jin zafin abinda ya shiga tsakanin ki da Isma'il ba kamar yau ba, bana so ina tunawa ki tayani da addu'a Baby nah ina so na manta gaba daya,  dan burina a rayuwa, in ganki cikin farin ciki, kuma nasan in dai zan tuna, sai kin shiga kunci kiyi hakuri My Sweetheart."

"Na hakura amman please My Guide Angel ka daina tinowa in kana tinowa zan rasa nutsuwa ta zan kasance cikin kunci a rayuwa."
Dagota yayi ya zuba mata ido, yace
"Am sorry for making you cry and disappointed."
Ya fada yana share mata hawayen ta.

Kai ta girgiza hawaye na zubo mata bakin su ya hade waje daya ya fara kissing dinta, Daga nan kuma fa ya kara biyan bukatar sa yana tai mata sumbatu, sai wajen karfe hudu ya kyalle ta, ya shiga bandaki yayi wanka, yana fitowa yazo ya tarar bata dakin, doguwar Riga ya zura ya tayar da sallah, Halima itama tana zuwa dakin ta  wankan tayi itama ta daura alwala, tazo ta tada sallah, a haka su biyun sukayi nafilfili, suka ta addua, kabir na addua Allah ya bashi zaman lafiya shi da matansa, yasa ya manta abinda Halima tayi, ita kuma Halima na adduar Allah ya yafe mata yasa mijinta ya manta abinda ta aikata, sai da aka fara kiraye kirayen sallah asuba, Kabir ya Mike, ya nufi dakin Halima dan yaga ko Halima bacci takeyi yaje ya sameta akan sallaya ta Daga hannu tana tana addua tana hawaye, tausayinta ne ya rufeshi dayaji irin adduar da takeyi yabar dakin dan inya tsaya zai Iya zubar da hawaye.

Bangaren Sadiya ya nufa dan ya tashe ta, yana tura kofar yaga Sadiya kwance tana bacci tashin ta yayi da kyar ta tashi dan jiya batai bacci ba. Ya mike ya kama hannun ta sai da tayo alwala sannan ya tafi masallaci.

Bai dawo ba sai karfe takwas ya shiga bangaren Halima dakin ta ya nufa, ya tura kofar hade da sallama, a lokacin Halima na gaban mudubi tana daura dan kwalli, sanye take da wani coffe din less anyi mishi dinkin doguwar Riga, juyowa tayi ta amsa sallamar da fara'a, a fuskarta karasawa yayi gurinta ya rungumeta ta baya ya kai mata kiss a wuyanta
"My Sweeheart kinyi kyau."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now