Chapter 1 page 60

218 20 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 6⃣0⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Yaya Zainab ce zaune ita da Umma. Umma tace
"Zainab naga kyaan kitchen kinyi kokari sosai wasu abun ai an siya anan ma Zainab."

"Ba komai Umma rabon ta ne yanzu ma ga ragowar kudin da Yaya Suleiman ya bayar dan a mata siyayya nace me kike ganin za a siya mata!"
"Har nawa ne?"

"Million biyu ya bayar to mun kashe million daya dayar ma tace tana son a saka mata dining munyi ciniki da wani mai siyar da kaya shine nake so a bashi kudin yanzu dai dubu dari takwas ne a hannu na in an siyi dining table din."
"Ai ba sai an siya ba domin Abban ku ya mata kaya komai da kika san yarinya zata bukata yai mata. Dan komai daki biyu yai mata bedroom ma kuwa har uku ya siya mata kayan wani gidan sa yace zai basu bansan wannene ba dai amman a gaskiya Abban ku ma ya kashe kudi nima nan ya bani dubu dari biyar wai in tana bukatar wani abu a dada mata to ni kan me zan dada mata kaya har sun mata yawa."

"Allah sarki kanwata mahakurci mawadaci insha Allahu zataji dadin Muhammad za kuma tai alfahari dashi tai murna da zabin abban mu daman kuma can Ummu ai yar gaban goshin Abban muce!"
"Haka ne. Nima dai tunanin me zan wa Ummu nake!"

"Umma ni a ganina wadan nan kudaden a siya mata gida a zuba haya ragowar kuma a cigaba da juya mata a business din ta ko ya kika ce?"
"Hakan ma yayi Zainab!"

"Yauwah Umma, Muhammad ya kawon wata magana jiya!"
"Ina jinki!"

" wai walima yake so ayi kan ta tare!"
"To wannan ai sai dai muje ga Abban ku in ya yadda shikenan ko?"

"Haka ne!"
"Tashi muje!"

Ta mike suka fita. Mama suka sama a tsakar gida tana gyara kayan miya ta kalle su ta saki shewa tana fadin
"Ana ta kulla kulla kenan!"

Ba wanda ya kulata suka shige dakin Abban. Yana zaune akan carpet suka shiga. Ya mike zaune yana fadin
"Ina amarya Ummu?"

Zainab tai murmushi tace
"Au Abban ni ba tani kake ba sai ta amarya."

"Eh mana kinsan amarya da farin jini."
Zama Zainab tayi tace
"Lallai kam!"

Tayi kasa da kai tace
"Ina yini Abba?"

"Lafiya lou! Kunzo lafiya ina kishiyoyina aka barsu."
"Suna gun Ummu!"

"Madallah!"
Ummah ce tai masa bayanin kudin da Suleiman ya bayar da abinda akai har da ragowar. Abban ya jinjina kai yace
"Suleimanu kenan shi dai baya gajiya to madallah Allah ya saka yayi masa albarka shima Allah ya basa masuyi masa."

Duk suka amsa da
"Amin!"
Umma tace
"Sai wata magana da Zainab tazo da ita daga Muhammad!"

"To to me ya faru?"
"Daman jiya mukai waya yace yana son ayi walima kafin tarewar Ummu!"

"To shi ya nema ko ku kuka nema?"
"Abban sam bamu muka nema ba dan mu ba mu shirya komai ba in banda yan uwa suzo ayi yini akai ta."

"To in dai shi ya nema ai ba matsala zamuyi magana dashi Allah sanya alheri."
"Amin Abba!"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now