Chapter 1 page 72

172 20 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 7⃣2⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

*HML Bestie Khadija Taiyeb Na'abba. May Allah bless your union. Amin*


Karfe tara taji an bude dakin da sauri ta daga kan ta tana ganin Muhammad ta mike da sauri ya karaso a hankali ya kama hannun ta yace
"Sannu ya gajiya?"

"Alhamdulillah. Ina ka kawo mu nan Muhammad?"
"Gidan mu ne?"

"Gidan ku!"
Kai ya gyada yace
"Muje Abbi na son ya ga sirikar sa tin da na shiga fada yake fadin in kawo masa sirikar sa."

Ya kalli Hafsat yace
"Taso kanwata!"
Mikewa tayi tabi bayan sa. Wani bangare na daban suka shiga wanda kyaun sa da haduwar ta suke daban. Suna shiga Ummi ta mike tana fadin
"Sannu da Zuwa!"

Ta kamo hannun ta. Fauziyya ta zame ta fara gaishe ta cikin girmamawa. Ta dago ta tana fadin
"Ya gajiyar hanua?"

"Alhamdulillah!"
Ta kamo ta ta zaunar a gaban Mai martaba kusa da muhammad. Gaishe dashi tayi ya amsa cikin farin ciki da tambayar ta ya hanya nan mata amsa masa. Hafsa ta gasihe ya amsa yana saka musu albarla.

Shiru yai yana kallon su can ya kalli Ummi yace
"Alhamdulilah yau ga Yarima da mata Fulani Yarima na ya girma ko a yau na mutu Yarima zai amshi mulki Alhamdulillah."

"Lallai kam Allah shine abin godiya. Allah ya karawa Annabi daraja Allah kuma ya bashi ikon riko da dabiun ka ya bashi ikon yin adalci."
"Amin Fulani. Baki na ya gaza yin godiya na rasa tayya zan nuna farin ciki na. Agobe akwai liyafa ta dawowar Yarima da mai dakin sa. Dan haka jibi akwai taro kamar yadda kika ce gata zakiyi yini bikin da ba ai ba."

"Haka ne Ranka ya dade Allah ya saka da alheri."
"Amin! Allah muku albarka gaba daya. Ina alfahari dake Fulani kin haifa min farin ciki abin alfahari na yaro daya tamkar da dubu Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka."

"Amin Amin!"
Nan ya dinga musu addu'a da nasiha. Duk sai jikin su yai sanyi har Hafsa dake gefe ita ma.

Sai wajen goma da rabi suka baro bangaren Mai martaba dakin da aka kai su direct suka nufa. Bedroom suka shiga Fauziyya da Muhammad.

*
Hafsat kuwa ta zauna anan falo tana kallo can taji wayar ta na kara. Dauka tayi taga Ahamd ne murmushi tayi ta dauka ta kai kunnen ta tana fadin
"Asaalamu alaikum"

"Wa'alaikum salam!"
"Ya kake ya dare ya gajiya?"

"Duk Alhamdulillah. Gajiya taji muryar ki ta gudu."
"Kai Deedat!"

"Da gaske!"
"Na zata kayi bacci ai!"

"Tayaya zanyi bacci banji muryar ki ba."
Tai murmushi tace
" hmm kaji ai kaje kai bacci dan kasamu gajiyar ta tafi kaga gobe da aiki."

"Korata kike?"
"Ni na isa?"

"Gashi nan kuwa.!"
"Aah tuba nake."

Yai murmushi yace
"To shikenan zan tafi amman ya garin naku ya gajiya?"
"Alhamdulillah."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now