Chapter 1 page 20

263 10 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 2⃣0⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

Not edited

Kallon wajen tayi tace
"Mu dan shiga daga soro."

Tayi gaba yabi bayan ta. tsayawa tayi shima ya tsaya, yace
"Dan Allah ki saurare ni da abinda nazo miki kwana ki na fada miki wallahi son ki nake kuma da aure dan Allah ki amshi soyayya ta kada ki duba rashi na....."

Kanta a kasa kanwar ta ta shigo daga waje tace
"Anty Fauziyya wai kizo?"

"Inji wa?"
"Inji wani a waje!"

"Je kice ba zan zo ba."
"A'ah!"
Muhammad ya dakatar da yarinyar daga shirin fitar da take yace
"Nima haka ake min kuma wallahi kasa bacci nake! Dan Allah kije kiji me zai ce miki!"

Dagowa tayi tana kallon sa. Son gaskiya take gani a cikin idon sa. Yace
"Jeki ki dawo ina jiran ki!"

Fita tayi a kofar gidan ta tsaya tana kallon motar dake kofar gidan wacce bata gani na ciki saboda tint ce. Dan haka ta tsaya tana kallon motar da tsana duk da bata san waye ba tasan irin samarin ta na baya ne wanda ba son Allah suke mata ba sai jikin ta.

Kamal ne tinda ta fito ya zuba mata ido bai taba ganin ta da Hijab ba amman ta masa kyau wannan yasa ya kasa ma fitowa a motar ya tsaya yana kare mata kallo.

Ganin yaki fitowa ne yasa ta daka tsaki ta juya zata shige cikin gidan. Da sauri ya dannan horn tare da bude kofar motar ya fito da sauri har yana tuntube ya karaso yana fadin
"Haba ranki yadade ayi hakuri laifin me nayi ne?"

Jin muryar kamal yasa ta juyo kallonsa tayi taji wata tsanar sa na karuwa a zuciyar ta. Wani banzan kallo ta aika masa sannan ta juya zata shige gidan hannun ta ya kamo da sauri, a fusace ta juyo ta daga hannu ta kwada masa mari sannan ta zare idanu hadi da daga hannun ta ta nuna shi da yatsa tace
"Ka kiyaue ni, ba Fauziyyar da bace wannan!"

Fuska ya dafe amman bala'in da yake ciki na rashin ta yasa ganin zata shige yace
"Naji please kiyi hakuri minti biyu dan Allah ba dan ni ba."

Jin ya hada ta da Allah yasa ta juyo tace
"Ina jinka menene?"

"Fauziyya wallahi na kasa jure rashin ki dan Allah ki taimaka min please kome kike so zan baki."
Wani kallon kasa da sana tai masa sannan tace
"Kasan me ya yi silar haduwa ta dani? Baka sani ba to ka sani ni a wajena ba kudi ya sa na aikata abinda na aika a ba kaddara ta ce ta saka ni a ciki kuma ina mai son fada maka yanxu kaddara ta ta canja."

Tai shiru sai kuma tace
"Kasan me?"

Tsaki ta saki tace
"Bai da amfani kaji amman ka sani kaji tsoron Allah. Minti biyun da ka nema ya kare dan haka ka bar mana kofar gida."

Tana fada ta shige soro idon ta na zubar da hawayen abinda ta aikata wanda duk Kamal shi ya fara lalata mata rayuwa. tana shiga soron gidan tayi turus ganin Muhammad a tsaye. Hijab din ta ta saka tana goge hawayen idon ta sannan tace
"Please kayi hakuri. Ni yanzu ba aure a gaba na. Ko da aure zanyi ban dace da kai ba."

Nan tayi ciki da sauri saboda wani kuka da yazo mata. Kai ya girgiza a ran sa ya ma rasa tunanin da zai in har bai samu Fauziyya ba yasan mutuwa zai yi. Shin ko dan bai dashi Fauziyya ke kin sa. Dan yaga yadda manyan Alhazawa ke neman ta su bata musu haka ko dan su zasu bata kudi.
Kai ya girgiza dan baya son zuciyar sa ta kawo masa aibun Fauziyya dan son ta yake son Allah kuma da aure yayi bincike an fada masa wasu halayar nata na da da yanzu duk da a yanzu ba wai tana rashin mutunci ko shigar banza bane ance dai daga wannan motar ta dauke ta sai waccan ta dawo da ita. Wanda ake zargin bin maza take to shi yaji ya gani yana son ta. Dan Allah shi ya daura masa son ta daga kallo daya da yai mata. A haka ya ja kafa ya bar gidan jiki a sabule.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now