Chapter 1 page 2

551 30 0
                                    

Alhaji Kasim Babban ɗan kasuwa ne wanda yake kasuwanci kala-kala, ba abinda baya siyar wa ya kan yi order kaya daga waje ya kawo ya siyar wa da ƴan kasuwa, bayan shagu nan da yake dasu banda wanda ya bada haya, haka nan yana da gidaje da ake masa haya sannan yana da filaye da yake siya in sun shekara ya siyar lokacin sun ƙara kudi. Alhaji Kasim dai mai kudi ne kuma Allah ya rufa masa asiri.

Sai dai duk wannan abun bai kula da iyalan sa bare ya dauke nauyin su. Tin yana saurayi ya auri Sa'adatu wacce yanzu ya'yan ta shida da shi, tinda sukai aure take shan wahalar sa don a lokacin ma ba wani hali ne da shi sosai ba. Inda da yaga budi yazo masa sai ya fara aurece-aurece.
Wanda in ya tashi aure an mata masu kyau da jini a jika yake aura a waje zai kashe miki kudi amman da kin shiga gidan sai hakuri bama idan aka gama cin amarcin kika fara laulayin ciki. A haka yake wasu da yawa sun fita kuma in zaki fita ba inda zaki je masa sa ya'yan sa.

Akwai wata Yarinya da ya aura Hibbatu sunan ta a waje sun sha soyayya inda har ya aure ta bayan ya jika iyayen ta da kudi, gidan ta da ban ya saka ta bayan aure daga baya kuma ya ce zai hada ta da matan sa da ta tada hankali iyayen ta suka yi mata fada tinda tana zaune Lafiya kuma tana ci da sha ta yi hakuri haka ta hakura aka kai ta gidan sa.  sai da tazo gidan taga yadda yan gidan suke jikin ta ya yi sanyi, wanda bata jima a gidan ba ta fara laulayin ciki sai ya yasar da ita kamar ba ita ce suka sha soyayyar nan ba inda bata yi kwana kadan ba ya ƙara yin wani aure.

Haka ta cigaba da rayuwar a wannan halin har Allah yasa ta sauka Lafiya da taga baza ta iya ba ta sa ya sake ta dole, da kyar ya sake ta dalilin sakin ma don ya gano wata ne. Bayan ya sake ta taso ta tafi da yarinyar da ta yaye amman yace tinda ta yaye ta ba inda zata da ita don ta ce yana bata kudin abincin yarinyar har koto a kaje amman da yake mai kudi ne har alkalin ya siye haka suka hakura amman hankali ta na kan yar ta don sai da da-na-sanin neman sakin da ta yi saboda taga irin rayuwar da yaran gidan ke ci ba kula ba ci bare sutura. Wannan ya tada hankali ta duk ta kasa sakewa. (Shiyasa wani lokacin ba wai sakin ne ba a so ba makomar ya'yan ka wani lokacin da dadi da ba dadi gwara ka zauna ko don tarbiyyar ya'yan ka.)

Babar ta ce daman kullum in ta kawo kuka take lallashin ta da ta dage aka sake ta tazo tana kukan take mata nasiha kamar haka
"Hibba ba wahalar da kike sha nake Jin dadi ba sam bana Jin dadi amman nasan Alhaji Kasim ba bar miki yar ki zai ba ko don kar ace yana bada kudin kayan abincin ta, Wanda ke ganau ce kinga irin rayuwar gidan yanzu gashi can kin baro yarinya ƴar shekara biyu gidan da yara suke da yawa ita ma Sa'adatun abun ya yi mata yawa ita ke kula da ya'yan goma sha da zaman ki kika yi da dadi ba dadi kika kula da tarbiyyar 'yar ki da yafi amman yanzu duk inda kike hankalin ki na kan 'yar ki sai dai ki dage da mata addu'a Allah ya kiyaye ta ya shirya ta amman nima ina Jin ciwon barin 'yar kankanuwar yarinyar can addu'a dai zamuyi tayi mata."

Haka ta hakura ba don taso ba da yawa matan haka suke barin ya'yan, daga bata su dawo suna da-na-sani don sun san irin rayuwar gidan.

Yanzu a gidan daga Sa'adatu uwar gidan wacce suke Kira da Yaya Babba sai Jummai mai bi mata sune kadai suke zauna don ya'yan su don sune masu ya'yan da yawa Sa'adatu ya'yan ta shida sai Jummai mai ya'yan takwas ban da waɗan da yake aura daga haihuwa daya su fita wasu biyu wasu uku, ga Samira na da 'ya daya ga ciki nan a jikin ta wanda bata san da zaman sa ba sai amaryar sa Haule da ke da ciki itama haihuwa yau ko gobe.

Duk gidan ba mai Jin dadi duk a kare suke a rame, ba cima bare makwancin mai kyau sam bai san halin da suke ciki ba. In ance wane ba lafiya kan ai magana zai janyo wani kwando da yake zuba tarkacen magungunan sa ya dauko duk wanda Allah yayi ya baryar wani in ansha Allah ya taimaka aji sauki wani kuma asha jinyar in Yaya Babba ta samu taimako ta kai yaron asibiti wani kan haka zai gama jinyar ya hakura.

Ƴayan sa ƴan matan sunkai su takwai don wadan da za su yi shekara goma sha tara sun kai su biyu sai yan sha bakwai su uku yan sha biyar su hudu haka abin yake bi da bi. Inda yake da Babban ɗan sa ɗan shekara ashirin da biyu amman duk ya'yan ba wanda yaje makaranta don da ance kudin PTA sai dai su zauna sai in anja lokacin su koma inda ba wani karatun kirki suke samu ba Sam.

Shikan Lawan Babban ɗan nasa ya gama secondary school amman har yanzu yaki ya Samar masa makaranta ya karasa, ƴan matan sa kuwa da yawa an fito ana neman su da aure yace bai da kudin da zai aurar dasu.
Rayuwar gidan dai sai wanda ya gani abin tausayi.

Jummai ce zaune ita da Sa'adatu, Sa'adatu ta ce "Jummai ni dai na gaji da rayuwar gidan wallahi."

Numfashi Jummai taja ta ce "Haba Yaya Babba keda kike bamu kwarin gwiwa yau ke kike wannan maganar."

"Ai baki sani ba wata mafita na samo ne."
Gyara zama jummai ta yi ta ce "Wacce mafitar fa?"

"Gani na yi da wannan rayuwar wahalar da muke mai zai hana mu fara fita yawon bara mu da ƴan matan nan namu kinga daga nan ma na samun na abinci ke har aure ma yi wa ƴan matan tinda dai ba karatun suke ba amman Yaya kika gani."
"Yaya kina ganin za a dace wannan shawarar taki."
Jummai ta fada tana kallo ta.

Kai Sa'adatu ta gyada ta ce "Ai baki sani ba wallahi 'ƙawata Hanne ita tazo gidan nan jiya take fada min har gida ta siya ana mata haya da kudin bara fa."
Ido Jumma ta zaro ta ce "Kai haba dai?"

"Wallahi tallahi haka ta fada min kuma na yadda da maganar ta. Yanzu dai kinga in Alhaji ya fita kan zuwa dare ya dawo ai munje mun samo abinda zamu samo ko ya kika ce."

Da sauri Jummai ta ce "Hakan ma yayi ki mata maganar sai mu fara fita gobe ni da ke yadda muka ga tsarin wajen yaran namu ma sai duk mu shiga gari tare."

"To shi kenan."
Wani yaro ɗan shekara uku ne ya karaso wajen Yaya Babba ya ce "Mama yunwa nake ji."

"To ishaq ka ƙara hakuri bari baban naku ya dawo mu gani."
Ta janyo shi jikin ta. Don ita akwai tausayi ba kamar Jummai ba da iya ya'yan ta kawai take rikewa amman Yaya Babba duk wacce ta fita ya'yan gun ta suke.

Washe gari gidan Hanne suka nufa bayan mai gidan ya fita samun ta suka yi ta fito rike da ledar ta tana rufe kofar dakin ta, Sa'adatu ta ce "A'ah Badai har kin fito ba kace da mun jima da baza mu same ki ba."

Hanne ta ce "Ke dai bari ai da wuri ake  fita."
Ta fada tana kulle kofar ta gama ta ce "Ya na ganku ku kadai."

"So muke mu fara ganin ya hanyar abin yake."
Tsaki ta yi ta ce "Ai wallahi da kun taho da ya'yan ku ko da har mazajen aure zasu samu, ke nifa Allah ne yasan manufar jaki da baiyo shi da ƙaho ba amman da ina da yara ko wacce hanya ce zan daura su don su samar min na kashewa ni ina gida ina hutawa."

Yaya Babba ta ce "A'ah ba dai ko wacce hanya ba Hanne."
Jummai da Bata tanka ba tinda suka fara tafiya ta ce "Wallahi Yaya Babba in dai zamu samu kobo da sisi zan tura ya'yan na, Hanne fada min shin da wata hanya bayan wannan abin ya ishe ni naga in bamu tashi tsaye ba wallahi zamu mutu mu bar ya'yan mu a bala'i don wannan rayuwar ta gidan mu bala'i ce."
Da irin waɗan nan maganganun har suka karasa bakin hanya inda suke zaman Hanne da Jummai na da tattaunawa.

Antty

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now