Chapter 1 page 54

309 22 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 5⃣4⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Kabir ne zaune a dakin sa yayi nisa wajen tunanin Halima. Wayar sa ce ta hau kara wannan yasa ya dago ta da sauri yana dubawa. Isma'il ne tsaki ya saki dan yanzu ba wanda yake jin haushi kamar Isma'il na ganin halin da ya jefa Halima. Duk da bai gama bincikawa ba amman yasan tabbas da wani abu a kasa. Har ta katse bai dauka ba,  wani kiran ne ya kara shigowa da bazai daika ba amman yana tuna wani abu sai yai saurin dannan receive  kan yayi magana Isma'il ya riga shi yin magana
"Hae guy where are you ne?"

Dakin sa ya kalla sannan yace
"Menene?"
"Yarinyar mana na samo mana inda take yanzu dan Allah kazo ka taimaka min."

Wani murmushi Kabir yayi yace
"Ok send me the address!"
"Kazo mu tafi dai."

"No in kana son in taimaka maka ai ba sai ka sani a gaba ba ko?"
Kai ya gyada yace
"Shikenan dan Allah ka tsara min ita sosai."

"Kar ka damu send me the address!"
"Ok thanks you!"

"Never mind!"
Ya kashe wayar ya mike ya  fara cire kayan jikin sa. Yana gamawa ya shiga bandaki wanka yayi ya fito ya tsane jikin sa sannan ya shafa mai bayan ya gama ya saka wata dakakiyar shadda mai kyau ruwan kwai wacce ta amshi jikin sa. Wanka yayi da ruwan turare sannan ya saka agogo ya dauki sandal ya saka kalar shaddar sa. Bai saka hula ba gashin kan sa dake a kanannede saboda yadda yake da tsantsi yana samun gyara ya kwanta yai luf luf.

Fita yayi ya nufi cikin gidan nasu. Main parlon ya nufa a cikin gidan su.  Da sallama ya shiga katon falon da aka kawata shi da kayan more rayuwa kamar ba mutu ba. Hajiyar sa na zaune a hakince akan kujera taci kwalliya tana kallon sunnaTV. tana ganin sa ta saki murmushi tana fadin
"Wannan wankan fa ina fatan dai gun suruka ta zaka je."

Kai ya dan shafa yana murmushi yace
"Ina neman addu'ar ki Ummi. Allah ya ban sa'a;"

"Kabir kenan kullum cikin maka adsu'a nake Allah ya baka sa'a ya shige gaba ya baka mace ta gari ya saka gama da duniya lafiya. Dan haka duk inda kake sa'a na biye dakai da izinin Allah. Allah dai ya kiyaye min kai."
"Amin Ummi nagode!"

"Zan tafi Ummi sai na dawo."
"Allah ya tsare ya kiyaye hanya ya dawo dakai lafoya."

Kai yayi kasa dashi sannan ya amsa da
"Amin Ummi nagode!"
Ya mike cikin nutsuwa ya fita. Yana fita ya nufi gun motoci ya zabi wacce zai shiga ya shiga sannan ya zaro wayar sa a aljihu yana duba text din Isma'il yai masa. Karantawa yayi ya ajiye wayar sannan yayi bismillah ya tafa motar ya nufi katon gate din gidan nasu.

Mai gadi na ganin sa ya bude masa gate yana zuwa ya daga masa hannu kawai ya fice a guje. Park din da aka turo masa ya nufi. Parking yayi ya fito ya nufi entrance din. Yana shiga ya nufi inda aka fada masa.

Tin daga nesa ya hange ta sanye da golding yellow doguwar riga wacce aka bi gaban ta da tsakiyar ta da silver stone. Tayi rolling kanta da mayafin rigar sai ta fito tamkar yar saudiyya wato balarabiyya.

Kirjin sa ne ya buga da sauri ya runtsa id kan yayi ta maza ya fara tafiya toward her. Yana karasawa yai sallama cikin muryar sa mai dadi. Dannana waya take ta dago a hankali tana amsa masa sallamar sa.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now