Chapter 1 page 68

104 9 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 6⃣5⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*


"Ni dai nayi mafarki da Yan gida Kuma abun ba Dadi!"
Tana fada ta fashe da kuka.

"Ya Isa haka?"
Ya rumgume ta Yana shafa bayan ta a hankali kukan ta ya dinga tsayawa har tayi shiru gaba daya. Ya dauke ta suka hau saman gado ya kwantar da ita.

Mikewa tayi da sauri tana Fadi
"Dan Allah Muhammad kada ka barni Ina son ka Dan Allah kada ka juyan baya."

"Ki daina fadar haka Baby. Insha Allahu mutuwa ce kadai zata raba mu Ina son ki ba Zan taba barin ki ba."

Kai ta gyada tace
"Mu kwanta to."
Kwanciyya yayi ta shige jikin sa. Ya tofa Mata addu'a. Take Bacci ya dauke ta.

Karfe 5:10am suka farka Dan sun Saba a tare suke tashi. Wanka sukai ya tafi masallaci ita Kuma tayi a daki. Tana idar wa tayi addu'a sannan ta tashi ta hau gyara gidan.

Ta gyarra daki ta share ta saka turaren wuta sannan ta share tsakar gida ta wanke bandaki. Kitchen ta shiga tai shara sannan ta fara wanke wanke ta gama ta daura tea.

Sannan ta shiga ta fara wanka tana fitowa ta zuba tea a flask sannan ta soya kwai ta shige daki.

Daki ta shiga ta shafa Mai tai kwalliya ta saka wani bakin less Mai adon ja dinkin riga da siket yai Mata kyau ta daura dauri.

Sam Bata ji bude kofar sa ba sai ji tayi an daga ta ta baya a tsorace ta juyo tana ganin shine ta fada jikin sa tana sakin ajiyar zuciya.

Yace
"Wai tsoron menene haka?"
Kai ta girgiza tace
"Ina ka shiga."

"Yawo."
"Katafi ka barni."

"To ba gashi na dawo ba."
"Ba ruwa a dakai."

Ta tashi a jikin sata fita. Ruwa ta hada Masa ta dawo tace
"Na Kai maka ruwan wanka."

Janyo ta yayi yace
"Ke Yar Nan da ni kike fushi to tuba nake naje maganar shagon Nan ne."

"Amman kace yawo."
"Tsokanar ki naje. Kinga Naga kosai na siyo Mana."

Amsa tayi tace
"Kaje Kai wanka sai mu karya."

Daki ya shiga ya cike kayan sannan yai wanka ya shirya yazo suka karya. Shi ya wanke cups din da plate sannan ya dawo daki. Tace
"Yaushe xamu tafi ne?"

"Ai ma Bari Sha biyu tayi ko?"
"Kai ai Rana tayi Nan da goma dai!"

"Sha daya dai Baby goma yai safiyya."
"Shikenan Allah kaimu "

Tin goma ta dauki mayafi da jaka da takalmi Yana zaune Yana Tai Mata Dariya Basu fita ba sai Sha daya d arabi.

Wani supermarket suka shiga ya siya buhun shinkafa da tafiya Mai Maggi sabulun wanki da wanka sai biskit da alawa na yara. Sannan aka saka musu a napep suka fito suka dau hanyar gida.

Sha biyu da arbain da biyar suka Shiga unguwar ana tsayawa a kofar gida ya fito ai da gudu ta fito ta fada gida ya bita da kallo Yana girgiza Kai.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now