Chapter 1 page 47

244 17 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 4⃣7⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

*Wannan shafin naki ne _Antyn Kowa_ really appreciate Allahu ya bar zumunci. Muna godiya.*




Kwanan su uku amman sam Muhammad bai nuna yana son ya kusance ta ba. Itama kuma hakan da yayi sai ya kara bata damar sakewa dashi. Dan a kwana ukun nan sun kara shakuwa sosai. Tare suke yin komai na gidan shara wanke wanke sannan girki. Su zauna suci abincin su. Sannan suyi wanka kowa yai wa dan uwan sa kwalliya su zauna hira. A hirar yawanci akan gidan suke yi. Wanda Fauziyya ita ba abinda tafi ji kamar Hafsa da ta baro takira wayar ta a kashe kuma daman tasan ita waya bata dame ta ba ko dan  saboda abokan shashancin su su dame ta duk da ta canja sim amman Farisa sai take basu sabon sim din da ta canja.

Zaune suke a falo kan ta a kan cinyar sa tana kwance shi kuma yana zaune. Sanye take da wata atamfa kofi kala wacce take da zane circle an yiwa circle din colour da milk, orange,  and yellow. Dinkin riga da siket. Rigar three quarter ce kan ta a tsefe yake yana ta shafa shi dan baki ne sidik kuma mai yawo da laushi. Fuskar ta tashafa hoda da jan baki sai kwalli da tasa. Sai tashin kamshi mai dadi take.

Shi kuma yana sanye da milk kala shadda yai kyau in ka ganshi kaga sabo ango. Wayar sa ce tai kara wannan yasa ya dauka yana ganin Ummin sa ce ya saki murmushi sannan ya dauka ya kai kunnen sa yana fadin
"Gaskiya Ummi nayi fushi yau three days baki kira bi ba kuma na kira wayar ki a kashe."

"Sorry mai babban su. Na barka ne ka dan huta da amarya. Kuma na bar Dubai ne ina China shiyasa. Ya kake ina 'yar tawa."
"Alhamdulillah! Ya kike to ya hanya?"

"Alhamdulillah. Bani 'ya ta naji ya take."
Mika mata wayar yayi ta kalle shi yace
"Ummi na ce."

Da sauri ta amshi wayar ta mike zaune ta kara wayar a kunnen ta.
"Assalamu Alaikum!"
Ta fada cikin sanyin murya da nutswa.

Murmush Ummi ta saki sannan tace
"Wa'alaikum salam 'ya ta ya kike?"
Alhamdulillah ina yini?"

"Lafiya lou. Ya sabon waje da bakunta ina fatan dai ba wata matsala ko? In da matsala ki fada min dan nasan Mai babban suna da damu kar ya na damun ki da yawa."
Kai tayi kasa dashi dan kunya ma ta bata tace
"Ba komai."

Hannun ta dayan ya kama yana wasa dashi. Ummi tace
"To madallah. Jibi zan dawo bansan yaushe zaku zo ba amman zan so da na dawo kuzo ayi komai da wuri."

"Insha Allahu Ummi."
"Yauwa. Allah miki albarka. Sai anjima"
Mika masa wayar tayi tai kasa da kanta. Ummi tace
"Mai babban suna a kula da 'ya ta kada ka na takura mata."

"Ummi wane takura mata zanyi?"
"Ni dai na fada maka."

"To Ummi yaushe zaki dawo?"
"Jibi insha Allahu. Yaushe zaku taho?"

"In kin kwana biyu kin huta"
"Toh shikenan. Allah ya baku zaman lafiya"

"Amin Ummi nagode."
Sukai sallama. Kallon Fauziyya yai da ta nutsu waje daya yace
"Ya dai Bae?"

Dagowa tayi yaga idon ta ya kawo ruwa matsowa yayi da sauri yana fadin
"Menene kuma."

Jikin sa ta fada ta saki kuka.
"Ya salam! Whats wrong? 😤"
Kuka take sam ta kasa magana in banda shishshika ba abinda take yi.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now