Chapter 1 page 66

225 23 3
                                    


*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 6⃣6⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Cikin gida suka dawo Hafsa ta shiga daki wayar ta tagani tana haske tana dubawa taga Ahmad ne dauka tayi tai sallama yace
"Ina kika shiga ne ina ta kira!"

"Wallahi na fita naje gun Halima ne!"
"Ohk ya jikin nata?"

"Da sauki!"
"Allah kara sauki!"

"Amin"
"Daman zan fada miki gani nan karasowa! Zan zo naga my princess naga ita me takara sannan in amshi amsa ta."

Murmushi tayi yace
"Toh Allah kawo ka lafiya."
Yace
"Amin nagode! Kin shirya kenan"

"A'ah!"
"In nazo ma kya shirya ai."

"Sai ka karaso."
Ta fada yace
"Ok!"

Mai fruit ya sama ya siyawa Halima da yawan gaske sanna ya tada mota ya nufi gidan su Hafsa yana mai jin wani farinciki da dadi na ratsa dukkan jikinsa da zuciyar sa.

Yana kashe wayar ta mike ta canja kaya sannan ta zauna kirjin ta na dukan uku uku tunanin ta tayaya zata amshi soyayyar sa in taki kuma menene dalilin ta.

Tana zaune wayar tabta hau kara dauka tayi ta duba taga Ahmad ne dauka tayi yace
"Ina kofar gida!"

"Ok!"
Ta mike ta saka hijab sannan ta shafa turare ta fito. Umma ta sama tace
"Umma nayi bako bari naje mu gaisa."

"To a kiyaye dai."
"Insha Allah!"
Sannan ta fita. Yara ta gani suna shigo da bugun dankali da goya sai kayan marmari.

Kanin ta Lukman yace
"Yaya ke akace mu kawowa!"
"Ni kuma inji wa?"

"Yana waje!"
"Ok!"
Ta fada tana basu hanya sannan ta shimfida masa darduma ita kuma tayi waje. Tsaye ta ganshi jikin motar sa ya zubowa kofar gidan ido yana hango ta ya saki murmushi sannan ya fara takun sa mai kyau da nutsuwa yayo kofar gidan.

Sam bata san ya karaso ba, sai ganin sa tayi a gaban ta ba karamin kunya taji ba ta juya tayi ciki yabi bayan ta. Zama tayi a can karshen dardumar sannan shima ya cire takalmin sa ya zauna.

Kanta a kasa tace
"Ina yini?"
"Alhamdulillah ya kike?"

"Alhamdulillah!"
"Ya me jikin?"

"Da sauki!"
"Allah kara afuwa!"

"Amin!"
"Uhmm ina jin ki?"

Dagowa tayi ta dan kalle shi sai karaf suka hada ido. Kai ta dauke da sauri yai murmushi yace
"Ashe ke barauniya ce."

Da sauri tana kallon sa. Yce
"You stole me heart!"
Waya ajiyar zuciya ta saki yace
"Haka ake kin dauke tawa amman kin ki bani taki biyu ta miki yawa ki taumaka ki ban taki zan kula miki da ita fiye da yadda zan kula da tawa."

Bata san lokacin data sake wani murmushi ba tare da lumshe ido. Shima murnushin yake Yace
"Hafsa na fada miki ban taba soyayya ba kece the  first girl dana taba cewa ina so kuma kece macen da na taba  zama da fadawa ina so har nake bin ki kina gudu na. what I know is that your love makes love change me har nake abubuwa ba tare da na sani ba. Wanu lokacin cin naji sam in ban ganki ba kanar zan mutu ne. Hafsa i love you amson da ban san dashi ba da ban yadda da wani abu so kamar haka ba saib yanzu a yanzu ina jin I can do anything just to have you."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now