Chapter 1 page 8

295 19 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 0⃣8⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

Tana fita suka hadu da Muhammad zai shigo,
"Yaya Muhammad!"
Ta kira sunan sa. Juyowa ya yi yana kallonta ya ce
"A'ah Ummu ce! Yaushe kika zo?"

"Dazu ya kake ya masu jegon?"
"Lafiya Alhamdulillah! Ya hanya?"

"Alhamdulillah!"
Ta bashi amsa. Sannan ta ce
"Yaya Muhammad a ƙara hakuri da Anty Rukky. In sha Allahu za ta gyara!"

"Allah yasa toh!"
Ya mika hannu ya amshi jannah yana fadin
"Mama na ya Baby?"
Ummu ce ta amsa da
"Yana lpy!"

Wani envelope ta dauko ta mika masa ta ce
"Ga wannan bayawa, Allah ya dafa."

"Menene wannan?"
"Kudi ne ba yawa!"

Kai ya girgiza ya ce
"A'ah ba zan amshi kudin ki ba Ummu. Ke da Abba kuna so na. Abba fa shi ya siyan ragon suna, sannan ya ban kudi masu yawa. yanzu ina da kudi."

"Don Allah Yaa Muhammad ka amsa, kyauta ce daga kanwar ka."
Sai da ta yi da gaske, sannan ya amsa ya ce
"Nagode kanwata ya ckul din?"

"Ckul ta zo gan gara kai fa?"
"Nima haka saura semester ɗaya ai ta yi mana addu'a."

"In sha Allahu. Allah ya taimaka."
"Ameen!"

"Bari mu tafi dare na yi."
"Muje na rakaku."
Har kofar gida ya rakasu sannan ya koma gida.

A gida Hajiya ta nuna masa abunda Ummu ta bata shima ya bude yaga dubu hamsin ta bashi. Nan suka yi ta saka mata albarka.

A gida kuwa ranar agunta Jannah ta kwana. Washe gari ta kaiwa Rukky kayan barka.  Rukky bata yi wata murna ba duk da kayan sun burgeta din yanzu bakin ciki take yi don me ita bata samu miji mai kudi ba da zai na siyo mata wadan nan kayan. Da-na-sani take akan me ta auri Muhammad itama dama mai kudi ta aura. Bata yi godiya ba itama Ummu bata damu da ta yi ba don ɗaya ta dauke su.

Ran suna Baby ya ci suna Abba Ibrahim ana kiran sa da Junaid. lokacin kuma Sailuba ta fara kwadayin haihuwa wai ko don ta samu gado kuma ta nunawa su Ummu itama fa mijin ta mai kudi ne, wanda kudin suke a banza daga ita sai uwar ta don ko Abba basawa wani abu. Mijin Zainab kuwa duk wata sai ya ajiyewa Abba kayan abinci da kudi. duk da Abba yana fada amman sai yace
"Yanzu Abba don na maka abu sai kana hanani in babu ai ba zan yi ba tinda da akwai kana amsa kana sa min albarka, Abba yanzu in su Abdullahi ne suka yi maka suma haka zaka yi musu. Don Allah Abba ka dauke ni kamar yadda su Mu'azam suke a gunka."

Abba ya kan ce
"Allah maka albarka. Wallahi Suleiman yadda na dauki ya'yan cikina haka nake daukar ku, domin in sone ma nafi son ku. Allah ya yi albarka."
Haka suke kusan kullum. Don Abba sam bai da son abin duniya. Kuma shima haka yake kyautatawa surukan nasa kan jiki kan karfi.

Kan Ummu ta koma ta zaga dagin Umma da Abba kuma duk ta yi musu alheri iya karfi ta. Sannan ta fara haramar tafiya don hutun ta ya kare. Tinda tazo bata ga Yaa Muhammad yazo gida ba, A jirgi ta koma da ta koma Anty Zainab da Babyn ta sai murnar dawowar ta suke. Sai da ta zauna sannan take fadawa Anty Zainab halin da Rukky ta sauya. Anty Zainab ta ce
"Allah ya kyauta yanzu itama halin uwar ta zata dauka kenan. Allah ya shirya. Mu da ake ganin matsiyata ai gashi nan Allah ya yi mana rufin asiri muna zaune lafiya a gidajen mu. A juri zuwa rafi wata rana tulun zai fashe. Don in dai ka ce tukunyar wani ba za tai zafi ba to taka ko tafasa ba zata yi ba. Aka ce in ka tashi gina ramin mugun ta ka gina dai dai kai."

"Allah dai ya kyauta!"
Ummu ta fada. Anty Zainab ta amsa da
"Ameen!"

*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now