Chapter 1 page 61

198 22 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 6⃣1⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

*
**
***
*DUNIYATA*

*Ina ma'abota karatun littafan hausa? Ku matso kusa kakarku ta yanke saqa.*
*shin kun karanta littafin FARAR TAFIYA?labarin soyayyar Amina da Isma'il wanda ta qullu bayan qaddarar fyade ta gifta tsakaninsu.*
*ga kuma littafin RUMFAR KASUWA wanda ya lakuto bangarori da dama na abubuwan da suke faruwada yara masu talla a kasuwanni da shaguna,ya fito muku da illa tallace tallace da kuma barin yanmata suna yawo sakaka babu kimtsi*.
*sannan ya fito muku da hanyoyin da za ku bi ku ciro wa yaranku hakkinsu idan aka zaluncesu musamman akan fyade ko yaudara.sannan ya fadada muku matakan aurar da yaran da kaddara fyade ko yaudara ya afka musu tare da jan su a jiki da kuma nuna musu kulawa ba tare da an qyamacesu ba*.

*TO YAU MA GA WATA SABUWA NAN*

*Littafin DUNIYATA labari ne da ya zo muku a lokacin da kuke bukatar irinsa a duniyar rubutu,ya zo muku da sabon jigo mai ma'ana.tare da warware kullin da aka zarga cikin ruwan sanyi da karfin addu'a.labarin ya zo muku ne da salo na daban da saura.ya kuma taho muku da abin lura da cewa ba mata kadai suke fuskantar qalubale a rayuwa ba,maza ma suna fuskantarsa wanda na Muktar Jarumin littafin ya bambanta.za ku ji yadda badaqala ta karke tsakanin ďa da mahaifinsa ,ya kuma fito muku da illolin rashin yarda da qaddara.gwagwarmayar ďa namiji tsakaninsa da mahaifinsa wanda ta kai uba ya yi wa dansa qazafin yunqurin kisa.*

*Kina bukata? ko kuna bukata?*

*Ku garzayo domin biyan naira dari biyu kacal ta wannan account number 0140772170 MURJA SALISU UNION BANK sai ku turo shaidar biya a wannan number 07034624830*

*Ko kuma katin MTN na naira dari biyu ta wannan number 07034624830 ku tura shaida kuma still ta wannan number din*.
***
**
*


Tin da ya fita kai Sakina airport hankalin ta ya kasa kwanciyya tai ta zarya a parlournta ta kasa zama ta kasa tsaye waje daya. Gashi ta kira wayar sa ya bar ta a cikin mota wacce ke hannun sa kuma bata da number sa. Haka tai ta zagaye dakin sai kuma ta leka window ko zai dawo duk ta damu ta rasa akan me.

Tabbas ba zata taba yadda danta da ta fiso ya auri Sakina ba yarinyar da taga tsiraicin ta ina sam wannan ba zai yiyu ba da Sakina ta auri Khaleel gwara ta bar duniyar gaba daya.

Tana zaune ta kara daukar waya tana kiran sa kiran ne ya shiga tana addu'a allah yasa ya dauka ai kuwa taji ya dauka yace
"Hello Mom ya akai gani nan na taho ko akwai abinda kike bukata?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace
"A'ah daman naga ka jima ne sai ka karaso."
Yai murmushi yace
"Ok thank you."

Ya kashe wayar yana murmushi shi kadai. Yana shiga gida yai parking sannan ya fito ya shigo fuskar sa dauke da murmushi. A falo ya samu Hajiyar tana zaune ya zauna a gefen ta yana fadin
"barka sa hutawa Mom."

"Yauwah ka dawo lafiya?"
"Alhamdulillah."
Ta kalle shi taga sai murmushi yake saki tace
"Lafiya naga kana murmushi."

Ya gyara zama yace
"Mom na wa Sakina magana ne tace ita bata da wanda take so shine nake murna kinga kenan tawa ce ko?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now