Chapter 1 page 73

164 19 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 7⃣3⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Washe gari karfe bakwai a gida tai musu. Ummu dakin su ta shige tai kwanciyyar ta. Umma da Yaya Zainab sai hada hada suke na abubuwan da za ayi.

Karfe Tara motocin daukar su ya zo Nan aka fada musu, Yaa Zainab ta shiga dakin Mamah inda su Sailuba da Rukayya suke sunci kwalliya kamar me.

Mama ta gaisar ta amsa sannan tace
"Daman kafi za'a tafi nace Bari nazo na fada muku."

"To me za'a a kafa nasan dai ba wata tsiya bace."
"Haka ne Mama Amman bama mu zamuyi kafin ba na dai fada Dane Dan company din su zasuyi komai!"

"To gamu Nan Zainab!"
Fita tayi tana Mai girgiza Kai.

"Ni ba inda zani!"
"Haba dai ku tashi muje mu kashe kwarkwatar idon mu!"

Mamah ta fada. Mayafai kawai suka saka suka fita. Umma dake tsakar gida tayi mamaki.

Zainab ma da ta fito daga dakin Abba tayi mamakin ganin su zasuje dukka. Waje suka fita suka samu mota suka shiga.

"Zainab nasan ba ruwan ki Amma ki kula!"
"Insha Allahu na turawa company din address Bari muje Kar suyi ta jira ga keys din."

"To Allah tsare."
"Amin Yaa Suleiman zai zo ya Kai ta wajen make up din ta zama cikin shiru Dan ayi da wuri Kar azo a makara."

"Insha Allahu. Sai kin dawo."
Ta fita. A mota ta samu su Mamah ta shiga wata daban aka dauki hanya Dan motoci hudu ne daya dagin Abba mutum biyu da dangin Umma mutum biyu itama sai wacce su Mama suka shiga da wacce Zainab ke ciki.

Tin da aka shiga unguwar jikin su Mama yai sanyi Dan so sukai suka unguwa marar kyau suna zuwa kofar gidan  gate man ya bude kofar a ciki suka samu motar kamfani na jiran su.

Parking akai. Su Mamah an shigowa gidan suka bi gidan da kallon mamaki. Key Zainab ta dauko ta bude bangaren su Ummu Nan suka shiga aka share akai mopping sannan suka fara kafi.

Mamah da Sailuba kuwa jiki. Su yai mugun sanyi dan ko motsi sun kasa. Dagin Abba da Umma ne suka ce
"Mu shiga muga gidan kan agama kafi."

Ciki sukai su Mamah suka tsaya suna bin compound din da kallo. Sailuba tace
"Uhmm karyar banza kila ma hayar gidan akai Dan a nuna man burga kawai."

"Ai kuwa nima abinda na fada bama yanzu da komai ake hayar sa dan naga wani shago a rimi Wai ana aran kayan kitchen da daki na wata daya wasu ma sati. Dan nasan gidan Nan dai Muhammad ba zai iya kama shi ba sai dai in haya irin na wata dayan Nan Dan a burge mu."
"Ai kuwa dai."

Rukayya dai kasa magana tayi Sailuba tace
"amman da akace Abba ya Basu gida."

"Karyar tasa su amsa!"
"Ikon Allah muje mu kashe kwarkwatar idon mu Dan kila ba zamu dawo mu same su a gidan ha."

Sukai ciki. Har an gama kafa gadaje da wardrobe da mudubi suna kan yin decoration din dakunan.

Wasu Kuma sun fara na falukan abin abun sha'awa kayan masu kyau da tsada suna ganin kayan sai da gaban Mamah ya buga hankalin ta ya tashi ta kallo Sailuba tace
"Ke mu koma gida tinda ba abinda zamuyi".

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now