chapter 1 page 109

223 13 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣0⃣9⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Halima ce ta fara haihuwa ranar da ta tashi da nakuda sam bata nuna wa kowa ba amman Kabir na kula da ita duk motsin ta sai yace
"Menene?"

Sai dai ta kalle shi tayi murmushi da yamma ma da suka fita zagaye sai cije baki take yace
"Baby ko muje asibiti ne?"

Tai murmushi tace
"Me zamuyi?"
"Na ganki ne kamar abar tazo."

"Kai Honey a ina kasan abun kawai dai uau naji cikin ya kara yin kasa ne."
"Ayya sannu ko na dauko mota ne."

"Haba dai ina nan ina gida."
Suka karasa tana tafiya da kyar a compound ta zauna ya zauna yana fadin
"Me zan kawo miki?"

"Yau bana bukatar komai."
"Ah haba dai har ruwan?"

Kai ta gyada tana cije baki. Sadiya ta fito daga sashen ta hannun ta rike da tray akai lemo da ruwa ne da cups ta karaso tana fadin
"Shine kuka tafi kuka barni ko?"

Da hannu Halima ta nuna mata Kabir! Ta kalle shi yace
"Kin gama abincin ne?"
"Yanzu na gama."

"To kinga da mun tafi fa."
"Ba wani nan gobe ba zamu da kai ba."

Ta bude lemon ta tsiyaya a cup ta miko mata,  kai ta girgiza tana fadin
"Nagode."

"Saboda me?"
Mikewa tayi tana fadin
"Ban son shan komai."

Tayi ciki. Kabir ya bita da kallo Sadiya ma haka sai da ta shige ya dawo da kan sa kan Sadiya yace
"Sweety kinga canji a gun My Love ko?"

"Na gani ko abar ce?"
"Haka nace amman tace a'ah cikin ne taji yayo kasa kawai."

Lemon ta mika masa tace
"Allah raba lafiya na kagu ta haihu na samu Baby nima."

Ya amsa yace
"Kema Allah ya baki naki!"
Fuska ta bata tace
"Nata ba nawa bane?"

"Inji wa? Naki ne ke kadai."
Tai murmushi ya sha ya mike dan an fara kiran sallah magariba.

Halima na shiga daki kafar ta ta rike da kyar ta karasa dakin ta ta shiga bandaki dan wani fitsari da take ji tana tsugunnawa taji abu yayo kasa hannu ta saka dan jin gaban ta ya dan dube wani taushi taji ta tsorata wanda tsoratar da tayi ya bawa Babyn damar kara turo kai jin abu na son fito mata yasa ta kara gyara tsugunnon ai sai ji tayi Babyn ya karasa fitowa ai kuwa ya kwanyare ihu. A tsorace ta dinga kallon Babyn yana kuka.

Sadiya ganin ta idar da sallah magariba ta nufi bangaren Halima ba kowa  a falo ta zauna na mintina taji shiru ta mike ta shiga bedroom din ta kukan Baby ta fara ji da sauri ta karasa bandakin kwance a kasa ta ganshi da sauri ta karasa ta dauke shi ta dauko kayan aiki ta gyara Babyn taje ta kwantar ta dawo ta taimakawa Halima ta gyara jikin ta.

Ta kai ta daki ta gyara wajen sannan ta fito ta dauki Baby Boy mai kama da Abban sa sak tace
"Masha Allah Sis ko ki kira ni."
Murmushi halima kawai tayi,  Sadiya ta dauki waya ta kira Kabir amman bai dauka bata kara kira ma haka, sai da akai isha'i ya dawo ya shiga bangaren Halima yasan Sadiya na can amman ba kowa a falo bedroom ya nufa yana shiga yaga Sadiya rike da Baby a hannu da sauri ya karasa yana fadin
" 'Dan waye?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now