Chapter 1 page 7

316 21 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 0⃣7⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

A haka har ta yi arba'in da yace ta dawo Mama ta ce sai ta zaga dangi don haka ya zuba musu ido. Da Abba yaga yakumbo ta dawo da kaya niki niki daga gun masu jego ya ce
"Har anyi arba'in?"

Ta ce
"Ai yau kwanansu sittin ma."
Wannan yasa Abba ya tuna da Rukayya dake gida ba ta koma ba. Da ya yi wa Mama magana sai cewa ta yi sai taje ta zaga ƴan uwa. Haka taje yawon arba'in sai da ta kara sati uku sannan ta dawo nan Abba ya ce lallai-lallai ta koma dakin ta washegari.

Ba yadda zata yi haka ta fara hada kayan ta. Bai ma san da dawowar ba sai da dare ya koma gida ya ganta zo kuga murna gun sa kamar zai hadiye ta. Nan ya yi ta tarairayar ta har ta ɗan sauko suka koma kamar da. Duk abinda ya aika Mama taki amsa yana nan ajiye don haka kayan abincin suke amfani dashi. Kayan barka kuma ya bata abinta.

Sai dai yadda ta fara canjawa ta ce ita zata yi cefane ya bashi mamaki amman haka yake bata sai ta raina wata rana ta yi shiru kuma in ya bata dari biyar bai fi ta yi cefan dari da hamsin ba sauran ta boye. Washe gari ta ce ba kudin ya kare.

A gidan su uku ne akwai dayar matar da mijin ta ba mazauni bane.  sai ya yi wata shida ma baya gari duk irin kulawar da Muhammad yake bawa Rukayya haushi take ji, don ita bata samun wannan kulawar. Haka ta shige mata da ta gane matsalar ta sai ta samu abin yi itama ta dinga zuga ta tana fadin
"Me za ai da talaka."

Ita kuma Rukky idon ta ya rufe ta kasa gano a matsalar da makwabciyar tata Asiya take ciki, sun dinke tana ƙara daura ta akeken ɓera.

Anty Bebi ta dayan bangaren kullum fada da nasiha takewa Rukky amman ba ji take ba don irin shawarwari da Mama da Anty Sailuba suke ba ta ga na Asiya.

Tinda ta dawo gida ya kasa gane kan ta komai sai hakuri daga yau ta ce sai ya siyo mata kaza jibi ta ce kaza. Haka dai in ya yi mata dinki ta raina in yayo cefane ta ce ita yana bata tana yi da dare ta ce ita ba zata iya cin abinci ba kaza take so ko Furar Rufaida wata rana tace shawarma tsurfa dai kala kala. Kayan shagon sa duk sun yi kasa saboda yadda take cin kayan kamar me? Dan Muhammad nason ta shi yasa komai ta ce yake mata. Ga Karatu baya ga cin su da shan da kudin haya ga iyayen sa dashi ke daukar nauyin su. Wata rana da kyar yake samun abinda zasuci.

A *Wannan Rayuwar* suka shafe shekara biyu wanda acikin ta sai hakuri yake da halin Rukky, in sun yi waya da Ummu ta yi ta bashi hakuri inda Rukyy suka yi ta yi ta bata rashin gaskiya da nasiha daga baya ma sai ta daina sanar da ita komai. Ita kuwa Ummu har kudi take turowa Yaya Muhammad don Yaya Suleiman duk wata sai ya bata kudi ban da na ckul haka nan Abba  yakan turo mata duk wata ita kuma ba ma'abociyar cin abinci ba, makaranta ma kai ta ake yi. Da ta ce ya daina ba ta ya hau ta da fada. Sai ta yi shiru. Abba ma ya ce sam ba zai daina ba kada tana takura Yayan ta da tambayar kudi.

Samari masu kudi da mu'kamai suka yi mata rufdugu amman duk taƙi sauraron su, Don Ummu tafi duk ƴan gidan su kyau don ma tana boye kyan nata amman daga sufar ta zaka gane mai kyau ce.

Har yanzu Sailuba bata haihu ba kuma bata damu ba dan ita a ganin ta ma hakan yafi, yanzu da Rukky ta kuna samun ciki zo kuga yadda Anty Sailuba da Mama ke mata sai ka ce cikin shege ne, duk abin ya dameta da ta fadawa Ummu hankali ta dinga kwantar mata dashi, duk da yar ta shekarar ta uku kuma a lokacin Muhammad ya gama degree din sa inda ya samu scholarship ya zarce masters din sa. A lokacin kuma Ummu na level 400.

Rayuwa ta yi masa zafi duk da da kyar yake samun na ci da sha ko makaranta a kafa yake zuwa amman duk da haka baya taba barin Rukky da Jannah da yunwa.

Duk safiya sai ya yi mata shara wanke wanke da girki ya yi mata wanki sannan ya fita, amman duk ita bata gani, Anty Asiya ta yi ta zuga ta  Anty Babi ta kan ce
"Wallahi ni burge ni kuke yi."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now