Chapter 1 Page 40

266 17 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 4⃣0⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*Ina mika ta'aziya ta ga yar uwar mu marubuciyya a kunguyar mu wacce kakan ra ya rasu wato NABIHA AMINU. Ina mai addu'a akan Allah ya jikan sa ya kyautata makwanci ya sa ya huta. Allah ya yafe masa su kuma Allah ya basu hakuri na rashin sa. Allah ya jikan dukkan musulmai ya kyautata namu zuwan. Amin*

*
*
*
*
Haka ya tafi a lokacin kuma Momy ta kara shige mata sosai dan bata da aminiyya sa ita. Haka ta dinga zugata har ita da kanta ta hada ta da wani babban Alhaji.

Rabi'a yadda taje jin ta a matse yasa ta bada kai bori ya hau. Ranar da ta fara bata iya runtsawa ba dan tsoro da fargaba ta dinga neman yafiyar Allah kuma tayi nada cewar ba zata kara ba.

Kwana tayi sallah da rokar Allah ya yafe mata. Washe gari haka ta yin wani iri. Amman Momy ta dinga zuga ta da mata hudubar tsiya a haka har Rabi'a ta yadda ta cigaba da hakar tayi tsamo tsamo a ciki.

Wanda sosai takejin dadi da samun kudi duk da ba dan kudi take ba kuma wani abun a duk lokacin da ta je ga wani ranar bata bacci sai rokar Allah ya yafe mata ya shiryata take.

In mijin ta ya dawo kuwa ko waje bata fita in ba tare zasu fita ba. Kuma sosai yake samun kulawa. Haka rayuwa ta dinga tafiya sai dai sam bata yadda ta dauki ciki ba dan tace in ta dauka bata san na waye ba dan haka ba zata shigar da dan shege cikin zuri'ar ta ba bare abin ya kara zama mata tashin hankali.

*
Juyi tayi akan gado tana me fashewa da kuka. Tabbas a yanzu ba zata kara biyewa rudin zuciya da shawarar Momy ba. Ta bar harkar nan ta har abada.

A haka ta mika komai ga Allah bata da abin yi sai rokar Allah ya yafe mata yini take zaune akan sallaya daga tayi sallah sai karatun alkur'ani.

Cikin kwana biyu ta rame tayi baki. Wayar ta gaba daya ta kashe ta ta daina kunnawa bare a dame ta.

Satin ta daya da ganin wannan abun tana zaune ta kunna wayar ta. Irin sakonnin da taga an turo mata ya bala'in kona mata rai. sai na mijin ta da yake ta tambaya lafiya wayar a  kashe.

Mikewa tayi ta cirw Sim din bayan ta dauki wasu numbers din. Wani sim da bata amfani dashi ta saka ta karya wamcan.

Sabon Whatsapo ta adaura da sabuwar number. Mijin ta tai wa text sannan ta dauki number Maryam S Indabawa tai mata magana cikin ikon Allah kuwa tana online wannan yasa tace
"Sister Rabi'ah ce please ina son ki sakani a Indabawa group na canja number ne.

"Ok ba damuwa."
Nan da nan tai adding nata. Sauka tayi tana mai dage kanta dan duk lokacin da ta tuna dan irin abinda ta aikata ita kanta kunyar kanta take.

Tana zaune Mustapha mijin ya kira ta. Dauka tayi tai sallama cikin sanyin murya.
"Assalamu Alaikum!"

"Wa'alaikum salam Baby ina kika shiga kwana biyu duk hankali na ya tashi."
Hawayen idon ne ya hau saukowa ta goge tace
"Wayar ce ta fadi na canja wata."

"Amman Baby har sati kika dauka baki canja ba ko ba kudi a gun ki?"
"A'ah!"

"Why to? Kinsan halin da na shiga kuwa."
"Am sorry."
Ta fada a sanyaye.

"Anjima zan karaso dan na riga na dau hutu hankali na ya tashi ban taba kwana daya ban ji muryar ki ba amman yau kar sati dole yasa na taho ina hanya."
"To sai ka karaso"

Nan ta mike ya  hau gyaran gidan nan da nan ta gama dan gidan daman a gyaran sa yake kitchen ta hada masa abincin da yafi so sannan ta shiga ta caba wanka tai ado cikin wata shaddar ta da akai wa dinkin three quarter da pencil siket. Tai kyau ta saka gold a kunne da wuyanta da hannun ta tai daura dauri tai kyau da ita kamar ka sace ka gudu.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now