Chapter 1 page 93

186 14 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 9⃣3⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Tana daki tana hada kayan ta ya shigo. Jikina yayi da kofa yana kallon ta. Ta dago tana fadin
"Yaya Muhammad ya dai?"

Kura mata ido yayi yana murmushi. Ta ajiye kayan da ta dauko ta dago tana kallon sa. Karasowa yayi ciki yana fadin
"Me kike ganin za a kaiwa su Anty Zainab da Yara?"

"Haba dai ai ziyarar da zamu kai ma.ta isa ko?"
"Ki sauri ki shirya muje muyiwa Hajiya sallama sai mu biya mu sai musu abu. Tayaya zamuje musu hannu haka ba komai."

Yana kaiwa nan ya fita. Tai murmushi ta karasa hada kayan sannan ta shiga ta shirya ta fito. Shi da yara ta same shi a falo duk suka dago suna kallon ta. Tace
"To muje kada yamma tayi."

Ya mike yace
"Yarana ku kalli yadda Mamin ku tayi kyau."
Junaid yace
"Sosai Abbi!"

Jannah tace
"Mami kinyi kyau!"
Rai murmushi tace
"Kuma haka muje kunji!"

Ta dago ta harare shi  yai mata gwalo yai gaba. Suka bi bayan sa mota ya bude mata ta shiga gaba yaran suka shiga baya. Gidan Hajiyar sa suka je suka gaisa sai da akai isha'i dan acan yaran duk suka ci abinci sannan sukai mata sallama suka taho.

A wani super market ya tsaya yai suka shiga. Yace
"Kowa ya dauki abinda yake so."
Yaran suka shiga zagaye wajen duk abinda suka ga suna so suka dinga dauka.

Muhammad kuma yaiwa ya'yab Anty Zainab siyayya sosai. Ummu kuwa ba abinda ta dauka nata duk Muhammad taiwa siyayyar under wears da turaruka sai da suka je total ta daukar musu ice cream nan ya biya suka saka a mota suka tafi gida. Kan su karasa duk yaran sunyi bacci. Ya parking ta fito zata dauki Junaid yace
"No muje kawai zan dauko su "

Ya dauki Jannah ya kai dakin su tabi bayan sa ta canja mata kaya tai mata addu'a sannan ya kai Junaid dakin sa shima kaya ta canja tai masa addu'a sannan ta nufi dakin ta. Wanka ta shiga tayi ta fito daure da towel.

Akan karfet din dakin taga ya zube ledar kauan junaid ball ce da JC sai mota da biskit ya maida yana murnushi. Jannah kuma yar tsana ce da story book sai kayan kwalliya. Nan ma yai murmushi ya dauki ledar sa yace
"Ga kayan su Anty Zainab nan."

Ta juyo tana fadin
"Allah ya saka ya kara budi."
"Amin"

Ya januo ledar ta ya zazzage sai ya tsaya kallon kayan juyowa tayi tana ganin yana kallon kayan ta mike tayo gun sa tana fadin
"Wa yace ka buden kaya na?"

"Baby ke me kika siya?"
"Yaa Muhammad ba abinda nake bujata kai kawai nai wa siyayya."
Ta fada tana mai da kayan cikin leda.

Janyo hannun ta yayi ta dago suna kallon juna nunfashin su na gauraya take ya fara sakin layi dan yadda yake jin shigar dumin jikin sa nata. Janta yayi jikin sa yace
"Allah miki albarka Baby nagode sosai "

"Kaji Yaya kudin ka ne fa."
"Kudin mu dai!"
Ya fara kissing bakin ta daga nan kidan ya sauya.

Washe gari da safe suka daga karfe sha biyu suna garin Abuja sun karasa gidan Anty Zainab wacce tai musu tarba ta musamman ta rasa ina zata saka su komai suka samo su haka yaran sun hadu da yan uwan su duk sun kasa zama sai murna suke abinsu.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now