Chapter 1 page 13

258 19 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣3⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*



Nan ta mike har da magajiya a masu rakata har bakin kofa. Nan ta hau napep ta tafi gida. Akan layin su nan ta samu wannan almajirar gaishe ta tayi a bude jaka ta bata dubu daya sannan ta wuce ta da kallo matar ta bita dan ta gane me yarinyar takeyi. Tana shiga kannen ta suka yo kanta suna mata sannu da zuwa, dan suma suna jin dadin ta dan sai dai bata ga yaro ba sai abinda yake so take masa. Dan haka nan da nan ta bayar a siyo muusu kaji sannan ta shige daki. Wayar ta ta dauka tayiwa su Magajiya transfer kudi masu tsoka sannan ta ajiye wayar bata minti byar ba sai ga kiran magajiya nan da an dakin suna zuba mata godiya tace ba konai ta kwanta dan ta huta.

Kamal ne ya kira ta na ta dauka yadda suke wayar ka rantse da Allah da mijin ta suke waya sai wani karairaya take da juyi akan gado. tana cikin wannan halin Samira ta shigo yadda ta canja kai baka ce itace a kwanakin baya ba dan yanzu ta goge ta zama fara tayi kiba ganin Fauziyya na waya yasa itama ta janyo wayar ta a jaka text ta tura ta ajiye. Wayar ce ta hau kara ta dauka cikin murya mai sanyi ta amsa sallamar sannan tace
"Ah haba na gane mai magana ko ba Alhaji Bilya ba."

Tai shiru tana murmushi tace
"Ah haba ka shigo gari kenan."

Tai shiru tana jin abinda yake fadi sai kuma tace
"Kaga yamma fa tayi da dai zaka bari ko gobe da safe."

Tai shiru tana sauraron sa sai kuma ta fashe da dariya tana fadin
"To gani nan kai kam akwai ka da jaraba ka baro matar ka xaka zo ka kwakuleni in nazo ma baifi kai round daya ba dan dare ya kusa kuma kasan yau a daki na mai gidan yake."

Tai shiru sai kuma tace
"Shikenan gani nan."

Dai dai lokacin da Fauziyya ta gama wayar kenan. Kallon ta Fauziyya tayi tace
"Allah Anty Samira ki daina abinda kike da auren ki."

Hararar ta tayi ta mike tafice bata tamka mata ba. Itama kwanciyya ta cigaba dayi har akai magariba tai sallah sannan ta mike tai wanka ta hau kwalliya sai kace mai zuwa biki sannan ta fice a gidan a bakin layin su ta tadda matar Wannan almajira zata tafi gida tana kokarin tashi dan haka da sauri ta karasa ta taimaka mata tana mata sannu. Amsawa tayi tace
"A dawo lafiya Allah ya tsare."
Sannan ta tafi.

Gidan Kamal ta isa tana zuwa yana falo yana jiran ta. kallon sa tayi a shekeke sannan ta samu gu ta zauna.
"Yau sarautar ce ta motsa ne gimbiyya ayi hakuri kisan yau a matukar matse nake tinda muka rabu a daddafe na karasa komai nawa."

Fari tai masa da ido wanda ya kusan zautar dashi nan ya mike ya shiga daki sai gashi da wani yar jaka yazo ya xauna a gefen ta ya dauko wata takarda ya mika mata yace
"Ga takardar gidan nan."

Ya kuma dauko wata yace
"Ga wata kyautar nan."
Sai ya miko mata mukullin motar yace
"Ga abinda kika nema kuma. Wai ke ina kike kai motocin kine?"

"Ina ruwan ka."
Ta fada tana tattare takardun da mukullin sannan ta mike tayi hanyar bedroom tana girgiza jikin ta wanda duk motsin ta kara jefa kamal take a cikin wani yanayin. Ido ya lunshe ya cije lebe yana jin wani iri a jikin da sa sauri ya mike ya bita dakin.

Yaya Babba kuwa wato Sa'adatu ta maida kananun ya'yan ta jari yau daga wacan unguwar gobe sai waccan zuciyarta ta gama mutuwa ta yadda yanzu ta wannan hanyar kawai zatai arziki wanda har tasa matasan yan matan take fito dasu daga baya ta barsu su shiga gari suna bin gida ana basu sadaka yan yaran kuma suna tare sai ta labe a wani gun suje su amso mata sadaka. Cikn ikon Allah sai gashi tana samu dan kudi yanzu take dashi sosai kullum a mai gidan ya fice itama take ficewa.

Maman su Farisa ma Jummai ma ta rika a yawon bara sun dinke ita da hajiya kaltum dan yanzu zance tafiyar su saudiyya na sukeyi dan itama yanzu kudi bata da matsalar sa sam.

Inda ita ma samira  abun da take yawon bin maza dan acan baruki suka hadu da masu aure irin ta suke rayuwar su tare. A cikin su akwai Rabi da Barira.

Rabi dalilin fara bin mazan ta mijin tane sam bai zama a garin kullum yana can yawon neman kudi bai fi yaxo yai mata sati a wata uku ba wanda ita kuma bazata iya jurewa ba shine ta fara bin maza dan ita da kananun yara yan unguwar su ta fara lalatawa inda daga baya ta shigo harkar sosai dan in taga babban Alhaji yai mata ma har gun malami take zuwa a ja mata hankalin sa. Ba ruwan ta da batsa a gaban kowa idon ta ya bude sosai tana da ya'ya amman har kwana take a waje sai ta dura musu maganin bacci suyi ta bacci ita kuma ta fice.

Barira kuma tana da mijin ta amman yau shekarar sa uku rabon sa da ita dan yayi balaguron samun kudi wannan dalilin ya jefata itama yawon bin maxa da auren su.

Inda Samira kuma mijin ne bai sauke nauyin cin su da shan su har ta fada harkar. Allah ka shirya ka sa mufi kafin zuciyar mu Ameen.

Fauziyya ce ta fito taci kwalliya sauri take zata je wata unguwa tana fitowa suka hadu da wannan almajirar kudi ta dauko ta mika mata sai almajirar tace
"Amman ina son ganin ki yarinya kinji?"
"Toh Baba sai dai in na dawo."

"Ba komai Allah ya tsare."
"Ameen nagode."

Tana tsaye akan tit taji wayar ta na kara tana dubawa taga Kamal ne. Dagawa tayi tace
"Ya akai Kamal dina."

"Please Baby wata tafiya ce ta sameni har london please kizo zamuyi wata magana."
"Kamal unguwa zani gaskiya."

nufashi yaja yace
"Kina ina?"

"Ina titin unguwar mu."
"Ok ki tsaya ganinan."

Ya kashe wayar. Tana tsaye tsaiwar jiran sa ai ga wani matashin saurayi nan yana sAnye da wani yadi wanda daga gani ba wani kudi ne dashi ba amman kyakyawa ne sosai. A gaban ta ya tsaya yace
"Assalamu Alaikum!"

Dagowa tayi tare da amsa sallamar wanda suna hada ido kirjin ta ya buga dan haka tace
"Wa'alaikum salam."

"Barka da yamma!"
"Yauwah!"

Ya danyi murmushi da ya kara fito da kyan sa yace
"Wallahi tinda zan shige na ganki sai naga kin min ina son ki."

Wani kallo tai masa zatai magana kenan sai ga motar Kamal nan taxo.
"Sorry!"
Ta fada tana daga masa hannu tayi gun motar ta tafi ta barshi a tsaye.

Motar yabi da kallo zuciyar sa na kuna ba tin yau ba ya ke ganin ta kuma yaji yana sonta da aure dan bai taba son wata a rayuwar sa ba amman ita kam yaji ya kamu da son ta da ya fara bincike akan ta sai yaji ance masa tana yawace yawace abinda ya daga hankalin sa kenan dan yadda yake wa Fauziyya addu'ar neman shiriya kanar shi ya haife ta ba dare ba rana addu'ar sa Allah ya shirya ta kenan yai sadaka yai azumi duk shi kadai.

Kamal daga nan Airport ya nufa a hanya yace
"Please Fauziyya once a rayuwar mu yau ki yadda ki rakani wannan aikin wallahi bazan iya nisa dake ba. Please ki yadda dani ba cutar dake xan ba."

Murmsuhi tayi a ranta tace
"Ai cutarwa ka gamai min tinda har ka kwanta dani ba tare da aure ba."

"Kinyi shiru."
Ya katse mata tunanin ta. A ranta sai taji itama dai yau bari tabi shi ta bashi wannan chance din da yake nema dan haka tace
"Ba damuwa."

Juyowa yayi yana kallon ta da mamaki yace
"Kin yadda sa gaske?"

Kai ta gyada masa. Jikin sa ya janyo ta yana aika mata da kiss sai da yaji motar zata kwace ne ya komar da hankalin sa kan titin. A take akai musu komai suka bar kasar.

*Antty ce!!!*

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now