Chapter 1 page 19

274 14 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣9⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*Wannan page din naku ne Meenal Ummu sakener, Maman Islam, Fauzy cool,*

Not Edited

Washe gari bayan sun fita bara kamar yadda suka saba Hajara tayi hanyar ta itama tayi wajen Isma'il. Tana zuwa ya hau murmushi. Fuska ta dan rufe da mayafin jikin ta tace
"Ina kwana?"

Baki ya lashe ya kura mata ido har ta dago fuska ta dan bata yace
"Ina gaishe ka baka amsa ba."

Murmushi yayi yace
"Kin tafi da nine. Wallahi ina son ki Halima in na rasa ki mutuwa zanyi ban san tayaya zan iya rayuwa babu ke ba. Please kiso ni ko rabin wanda nake miki ne."

Murmushin jin dadi tayi tace
"Haba Isma'il sau nawa zan fada maka ina son ka nima."

"Tayaya zan yadda."
"Zan iya baka komai nawa akan ka ba zan kula kowa ba. Ka sani ban taba soyayya ba da kai na fara kuma ina fatan ka zama miji na."

Ido ya lumshe alamar yaji dadi yace
"Tashi muje yau hirar bata nan bace sai an fadan matsayi na a cikin zuciyar ki."

Mikewa sukai ya kira wani yaron sa ya barwa jura suka bar wajen. Sannan suka tafi dn zuwa suka hau motar sa. Ta kofar wajen su Kabir suka bi zuwan Kabir kenan suka hadu da ido yabi Halima dan yana son yarinyar kamar zai yi me? Amman bai san ta ina zai fara ba ga wannan dan iskan yazo ya hure mata kunne.

Har ya shige kamar bai gansu ba Ismail yace
"Au abun yar haka ce!"

Juyowa yayi yace
"Am sorry ina sauri ne da yake fita zanyi ne!"

Ya mika masa hannu suka gaisa. Yace
"Ina zaka ne?"

Ido daya ya kashe masa yace
"Zamuje musha soyayya ne!"

Baki ya tabe yace
"Sai ka dawo!"

Kace
"Allah bada sa'a!"

Dan tsaki yayi ya shige cikin wajen. Da kallo Isma'il ya bishi yana dariya yace
"Big Alhaji kazo kaji dadin rayuwar ka ga kudi ga kyau ka kuruciya ka xauna a haka."

Kallon Halima yayi yace
"Muje ko!"

Sukai gaba tace
"Wai meyasa Kabir baya son ya ganmu tare ne?"

Kafada ya dage yace
"Shi ya sani."

Daga nan suka karasa inda yake parking. Cikin motar sa suka shiga ya tada ta suka bar kasuwa, gidan sa ya nufa da ita kai tsaye a hanya ya tsaya ya siya mata abinci da lemo.

Tin a gate gidan yai mata kyau duk da karami ne amman yayi kyau har suka karasa falon ta zauna a two sittet shima zama yayi gab da ita sai ta dan makale jikin ta. Dariya yayi yace
"Haba Baby menene dan na zauna a kusa dake kada ki manta fa auren ki zanyi kuma ba mai ganin mu anan fa."

"Nasan aure na zakai Isma'il amman hakan bai dace ba. Kuma in ba mai ganin mu ai Allah na ganin mu ko?"
"Haka ne amman ai ba wani abu nayi ba ko?"

Shiru tayi nan ya mike ya matso mata da abincin da ya siyo tace
"Yanzu ban jin yunwa sai dai ko anjima!"

Mikewa yayi ya kamo hannun ta yace
"Zo mu zaga gidan ki gani yai miki ko a canja wani!"

Binsa tayi suja zagaye gidan sune har bedrroom din sa sunje na farko a na biyun ya zauna a gefen gadon yace
"Zo ki zauna!"

Daga gefe ta zauna ya mike ya sshiga bandaki ya jima sai gashi ya fito daga shi sai boxes da towel yana tsane ruwan kan sa. Mikewa tayi ta juya baya. Karasowa yayi ya hade jikin sa da nata wata ajiyar zuciya suka sauke dukkan su a tare. Kokarin barin wajen take ya matse ta a jikin sa yana shafa masa mai danshi a jikin ta. Tsigar jikin ta taji tana tashi.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now