Chapter 1 page 63

212 18 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 6⃣3⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Ummu na shiga ta zauna anan falo tace
"Sannu Anty!"
"Yauwah me wanna shashashar ta zauna fada miki."

"Kai Anty!"
"Ba sha shashar bace."

Fuska ta bata. Anty Zainab tace
"Da yake na taba uwar ki ko?"
"Ba haka bane."

"Ai shikenan saura ki dauki shawarar ta."
"Haba Anty nima fa ina da hankali."

"Au haba?"
"Wallahi Anty ai na gane me tazo min dashi burgar cikina ta dinga yi da son kushe min auren har da Yaa Muhammad ma fa. wai na yadda kaza kaza haka nan wai ana tarewa da aiki na. Kisan me haka fa tace wai nace sai tai min lefe ni kuwa na bida ita a to."

"Oh ai nasa zuwan nata auko ta akai Allah yasa baki fada mata komai ba."
"Hmm Anty nima fa ina da wayo ko walima ban fada mata da yin ta ba in sun zo saji ko a aika mata da kati ta gani daga sama amman kiji wai nace masa ayi dinner ziga dai kala kala."

"Kinsan Allah Ummu ban yadda in kin tare tana zuwa miki gida ba kada ki kuskusara ki sakar mata fuska bare ta samu wajen zuwa ta kashe miki aure."
"Haba dai."

"To ki zauna."
Shiru Ummu tayi tace
"Wai yaya zanyi da kudin da Yaa Muhammad da ya turon."

"Nakine Ummu ki ajiye su bayan biki maga mai ya kamata ayi dasu ko?"
"Yanzu ba abinda ake bukata. Kudin fa da yawa ni bansan ina zan kai su ba. Shima Yaa Muhammad dai."

Murmushi Anty kawai tayi tace
"Dazu kuna ciki da Rukayya aka kawo bags da gift din da za a bayar an saka sunan ku sunyi kyau suna store din daki na."

"Waye ya aiko?"
"Kanin Muhmmad ne yazo ya kawo kayan sunyi yawa ma wallahi kuma sunyi kyau daga ga ni da tsada."

"Allah sarki Allah kara budi ya rufa asiri."
"Amin!"

"Imaan ta aiko dazu an bata sauran invitation din."
"Ni Anty bana son ma yaje wajen!"

"Saboda me?"
Shiru tayi. Anty tace
"Ba magana nake miki ba."

"Saboda Anty Rukayya kar ta kalle ahi."
"Ummu kishi!"

"Kai Anty ina kishin yake kawai dai kawai dai."
Murmushi tayi tace
"Dole kuyi hakuri abu dai na rana daya Allah zai kiyaye miki shi kinji, ki kwantar da hankalin ki insha Allahu babu kishiya agidan ki"

Murmushi Ummu tayi tace
"Nagode Anty."
"Amman fa sai kin dage Ummu!"

"Dame?"
"Kula dashi mana ki kula da komai nasa cin sa shan sa suturar sa farin cikin sa da bakin cikin sa,  ki taya shi son abinda yake a so ki taya sa kin wanda yake so in har bai kaucewa kaida ba ki zama mai bashi farin ciki da kwanciyyar hankali mai kore masa damuwa. Dole ki ajiye kunyar nan ki tallafi mijin ki, ki bashi abinda ya rasa a baya wato soyayya da tausayi ki zama uwa, 'kawa, kanwa,  matar sa ki zama abokiyar shawarar sa mai masa addu'a. Ki kansance macen da zai kalla yaji sanyi.
Dole ki rike tsabta duk da nasan kina da ita amman ki rike ta kam da kalolin girki kwalliya da kamshi. Komai naki ya zama na daban yadda zakiyi tafiya a gaban sa ta zama daban yadda zakiyi magana  a gaban sa komai dai ina fada miki.
Sannan shiga kala kala mai kyau da jan hankali ta safe daban ta rana daban sannan ko ya fita kina kiran sa ko tura masa sakonni na ban gajiya da salon soyayyar ki.
Duk da na lura da ya kamu da son ki amman kema sai kin kara tusa masa son naki. Ta hanyoyi da dama Ummu. Ki kwaci yancin ki ke matar sa ce kuma ke macece kina da abin so dan kinfi Rukayga nesa ba kusa ba kinsan a gida duk kin fimu kyau to kiyi amfani da kyan ki ilimin ki da tarbiyyar ki ki kara damke zuciyar sa.
Ki so Maman sa nasan kina son ya'yan sa to ki kara dan dama nasan kema ya'ya kine gashi aure ya hada ku da baban su dole ki kara son su da yan uwan su.
Bansan ki da rowa ba dan haka kina bayarwa da kyautata wa idan kina da shi,  Ya'yan nan amana ne ki rike masa su amana Ummu.
Nasan ki kina da hakuri da juriyya dan haka ki kara zaman aure ba zaman wasa bane da za ace za a fara ga lokacin kare shi muna fatan mutuwa ce kadai zata raba ku dan baka dole ki  kara dantse da riko da hakuri da juriyya.
Ki riki ibada komai ya faru kai kukan ki ga Allah ba mai magance miki sai shi kowa kika fadawa da addu'a zai taya ki dan haka ki kara riko da ibada da karatun Alkur'ani.
A bangaren gyara kanki kada ki yadda da wasu maganin mata komai zan rubuta miki wanda zaki hada da kanki in ma kayan zaki siyo ki bayar a hada miki ki bada kada yafi wanda zai kara miki lafiya kuma ya zama kamar abinci da kariya ga lafiyar ki,  ki kama yawan shan fruit da pepper soup inda hali in babu su ko gyada da zogale da aya ma sun wadata.
Sannan ki kasance mai yin ado a jikin ki kada ki bari yasan lokacin zuwa unguwar ki ko da yaushe ya zata unguwa zaki. Lalle da gyaran kai kina yin su akai akai. Haka nan gyaran jiki kina gani duk wata sai an min dan Allah Ummu duk abinda kika ga ina yi mai kyau kiyi koyi dashi marar kyau ki watsar ki dauki halin Umman mu nasan zakici riba.
Sai abu na karshe da zan kara fada shine kayi hakuri zaman aure dole sai da hakuri.
Kunya na fada miki ki cire ta ki ajiye ta gefe indai a gun faranta masa ne akwai gun da zaki dauko ki saka dan ta zama ado amman a gado gun bashi hakki ki nuna masa ke gwana ce kinji ko.
Bayan kwana biyu zan rubutu miki abubuwa masu yawa wanda a lokacin da abun yazo ina nufin ki fara amfani dashi kenan. Allah baku zaman lafiya da zuria mai albarka. Allah ya baki ladan biyayya yasa kici ribar ta kema ya baki masuyi miki biyayya hakika ko mu yayyen ki muna alfahari dake bare iyayen ki kuma na tabbata ya'yan ki da mijin ki zasuyi alfahari dake ummu kamar yadda alumma muslumai ma zasuyi Allah ya miki albarka!"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now