chapter1 page4

319 26 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 0⃣4⃣

Lokacin da Rukkaya tayi graduation ne sai Muhammad ya sanar da ita yana son su fara zance, haka aka yi ta amince dan haka yaje ya gayawa Hajiyar sa tayi murna sannan ta sanar da dagin mahaifinsa, suma basu yi kasa a gwiwa ba suka nufi neman masa aure.

Alhaji Ibrahim ya amshe su hannu biyu da yaji abinda suka zo dashi sai yace yana zuwa. Lokacin daman karfe takwas da minti sha hudu ne bai jima da dawowa ba. Dakin Mama ya shiga ya same ta zaune ita da Sailuba da take nuna mata masu kaya da taga ana tallar su a online inda tace tana so, don haka suke maganar Mama tana fadin ta samo number me siyar da kayan. Sailuba na ganin Abban nasu ta mike zata basu waje amman sai yace
"A'ah dawo ki zauna, fita zanyi."
Ya fada yana mai da kallon sa ga Mama ya ce
"Ina Rukayya ne?"

Tsaki Mama ta yi ta ce
"Kila tana can wajen Amina, ta dai rabani da 'ya ta, ta karfi da yaji."
Mikewa Abba ya yi ba tare da ya tanka ta ba ya nufi bangaren Umma.

Duk suna falo ana ta hira ana wasa da dariya gwanin sha'awa, Ummulkursum ce ka dai ba ta dakin tana can karatun ta. Sallama ya yi suka amsa ya shiga, ya zauna, duk mikewa suka yi zasu bar dakin da sauri ya ce
"A'ah ku dawo ku zauna ba zama zan yi ba."
Ya dubi Rukayya ya ce
"Rukayya ke kika amice Muhammad ya aiko?"

Shiru ta yi kirjin ta na bugawa
"Ki kwantar da hankalin ki, ai kin gama karatu don haka ke kika amince ya turo kina sonsa? Kin yadda zaki aure shi?"
Kai ta gyada tana sunne kai a tsakanin kafafun ta.

Yar dariya  Abba ya yi ya ce
"Toh Allah ya yi albarka,"
Har ya mike ya juyo yana fadin
"Ina uwa ta? Tana daka tana karatu ko?"
Suka amsa masa da "eh."

Ya ce
"Toh Allah ya yi muku albarka gaba daya!"
Sannan ya sa kai ya fita.

Wajen iyayen Muhammad ya koma ya ce,
"Yarinya ta amince tana son sa, sai dai ina da sharadi bana son yawan zance, don haka bikin yan uwan ta kafin sallah ne na yanke hukunci kan cewa tinda ya fito yana son ta ya kawo abinda Allah ya hore masa a hada ayi bikin tare, don nasan Muhammad yaro ne mai hankali sam bai da aibu ban taba jin ance  ya yi abu kaza marar kyau ba don haka ina murna da yazo gun 'ya ta kuma na bashi auren ta yanzu ya kawo abinda ya sauwaka nan da wata biyun a hada ai musu auren gaba ɗaya."

Godiya Iyayen Muhammad suka yi suka tafi akan suna nan dawowa da kayan auren.  A cikin gida bayan fitar Abba sai murna yaran suke, ana ta tsokanar Rukayya daga baya ta shige dakin gun Ummulkursum. Ummulkursum ta kalli Rukayya ta ce
"Anty lafiya? Har kin gama hirar?"

"Uhmm Ummulkursum, Muhammad ne fa ya turo gun Abba."
Ta fada tana zama a kusa da ita. Kirji Ummulkursum ta dafe hadi da zaro ido tace
"Me Abba ya ce?"

Ajiyar zuciya Rukayya ta sauke ta ce
"Yanzu yazo ya tambayen na yi shiru shine ya ce ai na gama karatu in ina son sa ne to? Nan na gyada masa kai."

Murmushi Ummulkursum ta saki tana sauke ajiyar zuciya hadi da fadin
"Alhamdulillah! Allah tabbatar da alheri, Ameen! Ka ce kema amarya ce. Allah sarki ni, duk zaku tafi ku barni, ni kadai, sai Yaa Alkasim da Yaa Abdullah sai Khalil."
"Kar ki damu, ma tafi tare!"
"A'ah, ni ina gida tare da Umma nah!"
Haka suka ta hirar su har ta tashi zata kwanta. Nan ta koma falo wajen su Anty Zainab, da Yaya Abdullah, sai wajen goma da rabi ta tafi dakin ta.

Da Iyayen Muhammad suka koma, suka fadi abinda Babban Rukkaya ya fada nan suka tafi. Bayan sun fada musu ya kamata a fara kai kudin sa rana da sadaki.

Jin abinda aka fada yasa Hajiyar sa, fito da wani set din dankunnen ta da sarka da abin hannu na goal, sai tayi kasuwar rimi nan ta hada aka fada mata kudin kayan miliyan biyu da dubu dari uku don haka daga nan ta wuce sabon gari ta siyo set din akwatina da kayan da ba a rasa ba. Ta ware dubu hamsin na sadaki dubu hamsin na saka rana, nan ta hado abubuwa dai dai gwargwado ta taho gida da niki nikin kaya.

Muhammad zai fita shago yaji ana shigo da kaya wannan yasa ya fita cikin mamaki yaga hajiyar sa ce da kayan nan ya shiga taya su shiga da kayan yana mamakin a ina Hajiyar sa ta samo kayan. Sai da ta shiga ta zauna ya debo mata ruwa ta sha sannan ya kalle ta cike da mamaki yace
"Wannan kayan fa?"

"Siyowa na yi!"
ta bashi amsa. Yabce
"A ina kika samo kudin?"
"Wannan sakar da mahaifin ka ya siyo min su na siyar."

"Haba Hajiya saboda me kika siyar, zan dau dashi na wannan satin dasu nake so a fara abubuwa."
Kallonsa take cikin so dpn yadda take son sa  kamar sa daya da Mahaifin sa.
"Yanzu Muhammad don na siyar da kadarata na maka abu wani abune? In ban maka ba wa zan wa? Menene amfanin kadara, yanzu haka gona ta na saka ta a kasuwa goben nan zuwa anjima za a kawon kudin a siyo kayan abinci sannan a samu gidan da zaku zauna, a dan yi hidimar biki kuma, Tashi ka tafi shago Allah taimaka Allah ya yi albarka, ya kawo aikin yi!"

Kasa tashi ya yi sai godiya da yake yana mata addu'a sai da kyar Hajiyar sa ta kore shi ya tafi. Yana mai kara jin son mahaifiyar ta sa, shi kam da me zai saka mata in ba da addu'a ba.

Ranar da dare Muhammad yaje zance sun zauna sun fahinci junan su inda yake fada mata abinda mahaifin ta ya yanke, taji dadi daga nan suka yi sallama tin daga lokacin yake zuwa zance duk weekend. A haka soyayya mai karfi ta kullu tsakanin Rukky da Muhammad.

*Zaku ji tin ranar asabar na saki layi daga farkon labarin na dauko wani ku cigaba da bin na zakuji duk yadda abin zai hade da wancan labarin. Fatana dai kuna an tayo ruwan comment abinda zai na ban kwarin gwiwar daure na zubo muku posting duk weekend insha Allah*

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now