Chapter 1 page 106

179 14 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣0⃣6⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*



Ya bude kofa ya fita ya zaga ya bude Mata har tayi hanyar Shiga aka Kira sunan ta ta juyo. Ahmad ta kalla tace
"Shiga gani Nan "

Ya shige ta tsaya kallon ta ta karaso tace
"Wai daman kina nan?"
"To ba gani ba kin ganni!"

"To ni ai abin ne yake bani mamaki da akace kin koma gida kin bar bariki!"
"Ke yanzu yaya kika gani? Hakan bai fi ba? Bai fi rufin asiri. Kalle ni na kara zama kamila na kara kwarjini da kyau "

Duban ta take tana tabe baki dan hijab ne a jikin ta har kada ba abinda ake iya gani a jikin ta. Dariya ta saki tace
"Ke kuwa menene ya karya miki zuciya haka ke da yar uwar ki? Ga Farisa nan dake tana shawanawa ita ake yayi. Wai ina son kudin, gayu,  da sauransu?"

"Gaskiya ita ta bayyana a gareni shiyasa na hakura na koma gida ko da dadi ko babu gwara na zauna a gaban iyaye na. Ku na gane duk wasu kayan kyale kyale da wasu kawa duk ribata ne daga shaidan! Wanda shi kuma shaidan la'anan ubangiji ne,  ba abinda yake sai so da yake mu bishi mu bar Allah!"
Dariya ta saki tace
"Hmmm Hafsat kenan rayuwa ba akwai dadi nasan nan gaba kadan da kafarki zaki dawo cikin bariki dan zaki samu abinda kika rasa har ma fiye dashi."

"Allah ya kiyaye ni daga dawowa wannan batattciyar hanyar Allah ya tsareni daga *wannan rayuwar* ta kaskance,  dabanci,  da asara."
Ta Dago hawaye na bin fuskar ta tace
"Da ace na koma *wannan rayuwar* wato rayuwar bariki gwara ace na mutu. Ina rokar Allah ya shiryar da duk ya'yan musulmai dake cikin *wannan rayuwar*"

"Ba amin ba malama. Ke da can da kike cikin *wannan rayuwar* baki da abinda kike fada ba sai yanzu!"
Wani murmushi mai ciwo Hafsat tayi tace
"Ko da ace na sani to shaidan ya rufe min bana ganewa ya mantar dani ya ribace ni amman yanzu haske yazo gareni wanda shi kansa shaidan zai ji tsoron tin kara ta da zinin manzon Allah.  Dan haka zan fada miki abinda kema kika sani shaidan ya mantar dake wato Lahira. Lahira gaskiya ce kuma dole muje kuma in mun mutu can zamu sai dai gida biyu kadai a cikin ta wuta da aljanna wanda kowa yasan aikin da zai kai daya daga cikin wadan nan gidajen kuma dole daya a ciki zaka shiga in ka mutu. Wato ko ka shiga aljanna ko ka shiga wuta. Su yan Aljanna sun kasance masu jin tsoron Allah,  da kiyaye dokokin sa da hakokin sa, da gaskiya,  ba masu fasadi a ban kasa ba ba mazina ta ko masu luwadi ba,  ba mara sallah da kin azumi ba yan Aljanna sune masu kiyaye alfasha da duk kan gabban su da idanun su. Wanda suke neman duk abu daga halak koman kan kantar sa su godewa Allah wanda koman yawan haram bata burge su, suna gudun ta sune masu tsarkake zuciyar su, su kadaita ubangijin su, su bishi da abinda yace ayi masu hakuri da juriyya kuma masu koyi da Annabi Muhammad SAW"

Ta shafa a fuskar ta. Har Izzy ma shafawa tayi. Hafsat ta cigaba da fadin
"Duk wanda ya sunffanta da wadan nan ya samu yardar ubangiji shin me kake nema a duniya in ba yardar Allah ba. Wanda in ka same tamkar ka samu ticket din Aljanna ne"
Jikin Izzy ne yayi sanyi.

Hafsat tace
"Masu wannan sufofin sune tawagar Annabi Muhammad wanda sune tawagar Ubangiji wato hisbullahi.  Wanda yan wuta shaidan ke jagorantar su yana cewa ku taho yana nuna musu duniya da alatun ta wanda yake matar dasu aljanna da ribar hakuri mai zatai musu,  wanda yake daurawa mutane suyi caca,  shan giya, sata,  fashi, gulma,  munafurci,  cin amana, ha'inci,  kisa,  a sace mutum,  aci naman mutum,  luwadi,  lesbian,  zina,  ayiwa yara fyade shin ina riba anan kaje kacewa Allah me?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now