Chapter 1 page 22

266 29 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 2⃣2⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*


*********************************
Kabir ne zaune shi da Isma'il. Waya Isma'il yake da Halima yana fada mata kalaman dake kara narka mata zuciya da son Isma'il din. Kabir yana zaune ji yake kamar ya hadiyi zuciya ya mutu. Dan shi tausayin Halima yake daman ga son ta dake dawainiyya dashi dan ko bacci baya iya yi dan tunanin ta. Gashi ita ta gama yadda da Isma'il a ganin ta son Allah yake mata. Shin tayaya zai tsairatar da Halima daga halin abokin nan nashi.

Dabara ce ta fado masa dan haka yana ganin sun gama wayar yace dan bani na tura abinda nace maka zan tura. Wayar a miko masa yace
"Bari naje na dawo kan Baby na tazo."

Tsaki Kabir yayi ya amshi wayar number Halima ya dauka sannan ya ajiye masa wayar. Ya mike zai tafi kenan ya dawo yace
"Har me?"

"Zan shiga shago ne!!"
"Ok nima daman yanzu zamu fita da Halima. Aboki saura rikis fa!"

"Me fa?"
"Na gama da yarinyar man!"

"Wai kai Isma'il me yasa baka tsoron Allah ne ka sani fa duk abinda kake sai an ma ya'yan ka kanwar ka ko matar ka."
Idon Ismail ne yai jajir dan baccin rai yace
"Amman ban san baka so na ba sai yau Kabir yanzu ya'ya na ko matata kakewa wannan fatan dan Allah."

Dafashi Kabir yayi yace
"Sam ba haka bane. Ina son ka ina fada maka ne dan ka nutsu kuma fadadde ne in dai kayi sai an maka dan haka ka nutsu. Kana lalata rayuwar yara."

"Kamar ya ina lalata rayuwar yara duk wacce kaga na yi lalata da ita fa ita taso ban taba danne ya'yan mutane ba sai sun yadda."
"Hmmm ka dai kiyaye tinda ba kyau Allah ya haramta."

"Ai Allah mai gafara ne zai yafe mana kan mu mutu, ka nan da lokaci kadan ma!"
"Ka sani mutuwa dai bata alerting."

"Please Kabir kar ka ruguza min jin dadi na da wa'azin nan naka."
"To Allah ya shirya!"

"Amin!
Ya fada yai cikin shagon sa.

Kai Kabir ya girgiza sannan ya bar wajen. Wata waya ya dauko a motar sa sabuwa fil ya shiga office din sa. Number Halima da ya dauka a wayar Isma'il ya fara sakawa bayan ya saka har ya tafi kira sai ya fasa.

Ido ya lumshe wani abu na tsaya masa a kirji dan takaici da bakin cikin abunda Isma'il zai yiwa Halima ba bakin cikin sa kar yaso ta ba sanin shi ba son ta yake ba wata manufa ce kadai a ransa.

Mikewa yayi ya nufi tagar office sa dake saman shagon su. Yana tsayawa ya hangi Isma'il da Halima suna tafe yana ta mata surutu ita kuma sai murmushi take yi. Wajen motar su ya nufa ya bude mata ta shiga shima ya shiga ya tada motar ya bar wajen. Idon sa ya runtse yana jin kamar ya bisu ya fito da Halima daga motar amman ba hali.

Gun shakatawa ya kai ta kala kala ya dinga cika ta da kayan dadi sam bai nuna yana son ko da taba hannun ta a yau dan har kaf kaf yake in yaga zasu dan gogi juna. Ita kuma sai ta kara ji son sa dan yadda ta lura sam yana da kaf kaf bayan a lokacin zai iya mata komai da ta kama hannun sa ma da sauri ya janye. Wannan yasa ta kara yadda da aminta da cewa lallai Isma'il da gaske auren ta yake son yayi kuma son Allah yake mata ba na wani abu gare ta ba.

Shi kam Isma'il yana sane yake haka saboda sam baya gama nunawa mace true kalar sa sai a hankali a hankali wanda yau in ya nuna zulamar sa gobe zai nuna miki bai damu ba har ya baki hakuri akan abinda yai miki wannan ke kara sawa yan mata kara yadda dashi nan basu san halin sa ba.

****************************
Tin daga ranar kullum suna tare da Halima. Yau kamar kullun suna shiga wani restaurant zasu ci abinci bayan sun zauna an kawo musu abinci ne ya kamo hannun ta ya sumbata. Ido ta lumshe sannan ta zame hannun ta. Da sauri ya saki yana fadin
"Assatagafurullah in ina tare dake ne am total going bae gaskiya hakuri na ya fara kai karshe."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now