Chapter 1 page 29

232 23 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 2⃣9⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

Ya tsaya Hannun sa Basma ta kama ta sakala a cikin na Hannah abinda ya haifar masu da wani shock wanda yasa ya dago yana kallon ta ita ma kallon nasa take. Sai yau ya taba tsayawa ya kalli kanwar ta sa har wani abu ya shiga ransa. Tayi kyau har ta gaji da yin kyau.

Shi yai karfin halin janye idanun sa. Domin Hannah ta kasa janye nata bata taba ganin Ahmad yai mata kyau irin na yau ba. Ya gama tafiya da ita daman ita tana sonsa.

Shima a ransa fadi yake
"Daman haka yarinyar nan take ba laifi zan gyara mata zama mu zauna tare da amarya  ta Hafsat."
Ya fada yana murmushin tunawa da yayi yau ya samu number ta yaga kuma gidan su. Ji yake kamar ma har ya aure ta. Tunanin Hafsa shi ya saukar masa da fara'a akan fuskar sa har ake zaton na auren ne.

A haka aka shiga hall din har suka zauna agun zaman su. Duk abinda ake gaba daya rabin hankalin sa naga a tashi yaje yaji muryar sahibar tasa. Amman ina taro ake kamar ba a san dare yayi ba dan sai karfe sha biyu aka tashi.
Yana fitowa ya shige motar gida ya amshi key wajen driver yana fadin zai bayar a kawo masa yanzu. A guje ya bar wajen.

Yana zuwa ya bada motar a mayar ya shige bangaren sa. Kayan jikin sa ya cire ya fada ban daki. Wanka yayi ya fito ya saka kayan bacci. Kan gado ya fada yana salati domin kuwa ya gaji tin da ya dawo bai huta ba.
Wayar sa ya janyo da nufin kiran ta sai yaga sha biyu da rabi da minti tara.
"Dare yayi."

Ya fada yana shiga message. Text ya tura mata mai dadi sannan ya ajiye wayar yana addu'a. Bacci me dadi ya debe shi da mafarken Hafsat.

Hafsat kuwa bayan ta shiga gida tunani ta fara. Anty Fauziyya ce ta shigo ta zauna a kusa da ita tace
"Ya dai sister?"

"Tsoro nake ji Anty."
"Tsoron me?"

"Ina son aure kuma ina tsoron abinda zan fuskanta."
Dafata Anty Fauziyya tayi tace
"Ki kwantar da hankalin ki kina addu'a Allah ya daura miki abinda xamu iya kuma Allah ya yafe miki. Insha Allahu! Allah zai kawo miki tallafi ta inda bakya zato ba gani nan ba. Na fada miki halin da nake ciki da Muhammad tin ina yakice shi har na hakura na bawa zuciyata abinda take so. Kema da sannu zaki samu mai tallafawa rayuwar ki ya cire ki daga *wannan rayuwar* damuke ciki kinji."

Kai ta gyada. Anty Fauziyya tace
"Ya kukayi da shi?"

"Uhmm ya amshi number ne?"
"Ok amman ina son in dai da gaske yake kar ki boye masa komai."

"Saboda me?"
"Saboda gwara ya sani tin kan ki shiga ki fuskanci matsala."

"Anya kuwa Anty xan iya. Sam bana son tuno *wannan rayuwar* sam."
"Duk da haka. Ni kina ganin zan yi fargaba nan gaba in Muhammad yasan koni wacece bayan a yanzu ya riga ya sani."

"Anty kenan son da Mubammad yake miki ba irin namu bane. Kuma ni ba zan ce zan tsaya neman wanda yake miki irin son nan ba dan wahala zai ji. Kema Allah ne ya dube ki ya kawo miki shi."
"Kema Allah ne ya dube ki ya aiko da wannan dan ni har ya kwantan tin yanzu."

"Toh Allah yasa mu dace."
"Amin ina wayar taki?"

"Ba caji."
"Ok muje muyi sallah ko?"

"Toh Anty."
Suka mike suka fita sukayo alwala .

******** ******** **********
Daga masallaci ya fito ya kalli agogon hannun sa karfe tara da kwata tinda yai sallah isha'i yake masallacin yana tilawa sai yanzu ya fito. Daga nan direct gidan su Fauziyya ya isa. A kofar gida ya tsaya dai dai lokacin da kanin Fauziyya xai shiga gidan ya kira sa.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now