Chapter 1 Page 48

271 20 6
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 4⃣8⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*




Sai bayan isha'i ya koma gidan sa. Bata falo dan haka ya nufi dining tin kayan da tayi amfani dasu na break har lokacin bata dauke ba. Kai ya girgixa sai ya juya ya nufi dakin ta.

Tana kwance akan gado hannun ta rike da wayar ta tana chat sai ganin sa tayi a kanta kawai dan ita ta zata ta rufe kofa. Da sauri ta mike tana zazzare ido.

Kallon ta yayi ya ga daga ita sai wani dan gajeren wando da half vest a jikin ta. Kai ya dan dauke yai gefe dashi yace
"Me kika dafa ne?"

"Banyi girki ba."
"Saboda me?"

"Saboda naga akwai ragowar kwan da na soya da safe sai kawai na kara shan tea."
"Ni kuma fa?"

Shiru tayi sai kuma tace
"Bari na samar maka wani abun!"

Kan yai magana ta fice da sauri. Dakin sa ya koma ya kakkabe gadon sa sannan ya shiga ya watsa ruwa ya fito. Gajeren wando kawai ya saka ya zauna a gefen gadon sa yana dailing number Hafsat amman a kashe.

Tsaki ya saki ya ajiye wayar dan kuwa ya manta sam number ta bata shiga. Yana zaune wayar ta hau kara ya dauka. Abokin aikin sa  ne lawan dan haka ya dauka yana fadin
"Assalamu Alaikum!"

Daga dayan bangaren aka amsa da
"Wa'alaikum salam ango kasha kamshi."
Yai murmsuhi yace
"Ya aiki?"

"Alhamdulillah ya hutu?"
"Hutu ya kare jibi zamu taho ai."

"Ok Allah kaimu agaida amarya sai da safe."
Ya fada yana kashe wayar. Hannah ce ta shigo hannun ta dauke da tray. Ajiyewa tayi plate ne sai juice da cup. Sauka yayi ya zauna ta mike zata fita yace
"Zauna in gama."

Kamar tayi kuka haka ta zauna ya bude plate din yaga indome ta dafa sai kwai da ta dafa. Ci yayi dan yai bai ci komai ba. Ya gama yasha lemo sannan ya ce
"Kwashe kayan ki dawo."

Debewa tayi ta kai ta dawo kallon ta yayi yace cire hijab din. Kallon sa ta tsaya ya mike ya shiga bathroom bai jima ba ya fito yace
"Me nace miki?"

Yadda ya hade fuska yasa ta zare hijab din. Zama yayi yana sakin murmushi yace
"Ko kefa."

Sai kuma yace
"Yanzu Hannah wane aiki ne a gidan nan da ba zaki iya ba. Just shara da wanke wanke ne fa kawai."

"Haba Yaa Ahmad amman ai yanzu da nai aure na huta ko? Nima a ajiye min masu min aiki na samu na huta."
"Au dan hutu kawai kike son masu aiki?"

Kai ta gyada yace
"Zan na taya ki sai muna yi tare kinga ai ba zaki wahala ba ko?"
"A'ah ni dai dan Allah ka bari kaga Momy ma ta kirani tace guda nawa nake so?"

Kallon ta yayi yace
"Nawa kike so to?"
" nace ko.uku ma sun yi."

"Uku kiyi me da guda uku?"
"Shara,  wanke wanke da girki."

"Ke kuma kiiyi me?"
"Nothing "

"To ban yadda ba."
"Kamar ya?"

"Ni ba zanci abincin masu aiki ba kuma daki na ma ba za a gyara min ba in ba ke ba dan haka ko an kawo yan aiki ke zasu nayiwa aiki bani ba kin gane?"
Shiru tayi. Ya kama hannun ta yace
"Ba zan hana ki yan aiki ba amman ki gane ni bana son su. Amman tinda kina so na barki a kawo amman ni koma nawa ke zaki na min kinji ko?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now