Chapter 1 page 37

251 11 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 3⃣7⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*
*
*
Samira wato matar Baban su Fauziyya wacce take ta uku. Itace wacce ta shiga kungiyar su Farisa in ba zaku manta ba tin a lokacin baya.

Zaune take ita da irin ta wadan da suka saba bin maza da auren su. Kamar yadda na fada muku tin baya wasu a ciki mazajen nasu basa zama ne suna can wata uwa duniya basa kula da lallurar iyalan su. Wasu kuma kwadayi yasa suka fada hanyar wasu kuma kuncin rayuwa a ciki har da Samira da kuncin gidan mijin ta ne ya jefata a cikin *wannan rayuwar.*

Zaune suke da Samira da Rabi'at wacce rashin zaman mijin ta shi ya jefa ta a wannan halin domin ita mace ce mai yawan bukata. Sai kuma Farida da kwadayi shi ya sa take bin maza dan mijin ta bashi da hali (Ku biyo Chapter 2/3) na labarin nan zakuji labarin sauran yan uwan nasu.

Rabi'at a cikin tafisu wayewa nesa ba kusa ba tana da ilimin boko da na addnin sai dai bata amfani dashi. Fara ce ga shi ta dada da mai sai ta kara haske. Tana da tsayi kuma kirar jikin ta na da kyau abinda yasa maza ke kara rubibi akan ta ne. Ga ta tana kula da kan ta da gyara jikin ta.

Ta yi kissa kallo tarairaya wanda duk su muke rasawa mazajen mu mafi a kasati ke neman matan waje. Matan banza na waje basu da kunya basu ki su side na miji ba indai zai ji dadi ya biya su. Amman mu sai mu zauna muce muna jin kunya. A ina kunyar take. Ai ba a wajen kula da miji kunya take ba. Kuma ma ku da akwai ta anan ai akwai lokacin da zaki nuna kina jin kunyar wani lokacin kuma ki nuna masa kema fa yar..... Dan Allah mata mu gyara mu kula da gyaran jikin mu tsabta da kula da abinda zai na kara mana ni'ima.

Kamar yadda nayi magana a some oage back akan magungunan mata. Waninillar tashi shine kin sa kudi mai yawa kin siya sai ya kare kuma baki da kudin siyar sa anan miji zai ji test din ki ya sauya bayan kin sabar masa da previous test kinga dole kullum yana neman na bayan. Amman in ke kika zauna kika hada abin ki da yar gyadar ki alkama aya ridi da sauran su kike yin kunun su kina saka madara a cikinina laifi. Ko kuma ki kasance kullum cikin tsarki da ruwan dumi bayan kinyi tsarki ki shafe gaban ki da al muski ko man zaibun. Haka nan kirjin ki kin yi yaye kinaso kar ya zube ki samu shinkafar ki ki dake ta da kanki kiyi gunbar ta kina sha da madara kina shafe shi da man hulba. Ko kuma ki samu kankana ki markada ki zuba mata madara a ciki. Haka nan yar ayar ki wanke ki markada ki tace ki zuba madara ko babu ki yini kina sha. Dan kifin ki in kin samu kiyi masa romo ki cinye ki shanye. Wallai kika riki yin abubuwan kula da kan ki zaki more rayuwar ki da kudin ki kadan kin biya bukata miji yasa miki albarka (Insha Allahu zan dubo muku wasu sinadaren na karin ni'ima wanda zaki hada  kanki ba sai kin fitae da makudan kudi ba.) Domin duk aikin daya ne dai.

Rabi'at ce rike da waya tana dubawa. Samira tace
"Wai ke me kike yawan yi a wayar nan ne?"

"Uhmm group ne dani kala kala na novels wallahi."
"Novels kuma?"

"Eh wallahi!"
"Menene a ciki da kike karantawa to?"

Dariya Rabi'at tayi tace
"Hmmm ke a novels din yanzu bama na online baki ga yadda nake kara samon salon kula da namiji ba shiyasa nake hargitsa tunanin duk wanda muke mu'amala."

Tabbas Rabi'a na daya daga cikin wadan da ake nema duk da matar aure ce. Dan haka Rabi'at tace
"Groups ne kala kala. Akwai na novels din wallahi kan ki gama karantawa kin gama jikewa akwai kuma na salihan bayi kamar wani da nake ciki *Indabawa hausa novels* kinga wannan group din da yan kungiyar wallahi su basa batsa a cikin littafin su amman kuma akwai dan karen dadi shiyasa sam bana barin littafi mai group din wato *Maryam S Indabawa* ya wuce ni ke bama ita kadai ba har na association din su *Hakuri da Juriyya Online writers* wato *HAJOW* Ya wuce ni. Hmmm wallahi in kina karanta buks din su ko dadin sa kamar me sam bana son littafin ta ya kare in ina karantawa. yana deben kewa sannan ina karuwa a wasu fannin rayuwar ga shi group din nasu da nata kullum sai an turo *azkhar* safe da  yamma, bama haka ba ga *HAJOW kitchen* da ake koya girke girke  wanda ko bakiniya ba zaki koyi kalolin girke girke da snacks. ga kuma *Ina Mafita* shirin dake kawo mana matsala da mafita da ta dace cikin hikima da dabara. Ga *Asan mutum asan sa'anar sa* shiri dake zaburar da al umma akan su nemi na kansu,  ba su tsaya sai abinda miji ya basu ba.  Ga *Hasken Musulunci* shima shiri ne dake wayar da al umma akan addinin musulunci bayan shi akwai *Musan Juna* inda ake tattaunawa da writers din association din har da member. Dadi da gari ga saukin kai ga dukkan marubutan kungiyar. Kinga ita *Indabawar* na sani ko? Amman wallahi baki ga yadda muke mutunci ba tana burge ni yarinya ce amman ba ruwan ta kowa nata ne ba girman kai."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now