Chapter 1 page 30

291 16 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 3⃣0⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

Isma'il ne kwance suna waya da Halima, sai tsarata yakeyi dan tun daga lokacin da ya santa 'ya mace taki sakin jiki dashi, kamar da shi kuwa bazai bari ta subuce masa a yanzu ba dan gaskiya ta wuce yanda yake tinani dan gaskiya sai a tara mata dayawa ba a samu, mai niimar ta ba, duk da ya san mata da yawa amman bai taba tarrayya da macen da tai masa kamar Halima ba.

Kasancewar Isma'il dan duniya ne yasan duk logic din da zai bi ya  shawo kan mace, a haka yayi ta cusa kansa awajen Halima yana nuna mata bashi da sama da ita.
Kasancewar Halima mai raunin,  sanyi ga hakuri, ga zafin San da takeyiwa Isma'il yasa ta amince zai aureta, kuma ta cigaba da yadda dashi da kalaman sa. Amma bata kara gigin kara  zuwa gidan sa ba.

Kabir kuwa bawan Allah yana nan yana fama da San Halima a zuciyarsa, yana ta addu'a Allah ya cire ta a ransa tinda abokin sa ya yadda da zai aure tan. Amman ina kullum son ta kara shigar sa yake.

A wannan lokacin Isma'il ya kara tusa son sa a zuciyar Halima ya kuma kara manne mata. Dan duk yadda take dan share shi a farko yanzu duk sai ta daina.

Yau bayan ta fita bara da zata dawo suka hadu a hanya ya bata nama da lemo. Gida ta koma lokacin ana kiran sallah magariba. Wanka tayi tai sallah. Tana zaune har akai isha'i tayi sai wajen tara tazo kwanciyya taga ledar da Isma'il ya bata wannan yasa ta bude naman da yawa sai lemo guda daya.

Naman ta diba ta bawa yaran gidan su dan su raba ita kuma ta shiga  daki ta hau ci ta gama ta shanye lemon ta. Kan shinfiddar ta ta hau lokacin da wayar ta ta fara kara kenan. Dauka tayi ta saka a kunnen ta.

Yadda yai sallama da wani nunfashi ji tayi tsigar jikin ta ta tashi. Sabida yanayin garin na sanyi ga kwayar sha'awa da ya saka mata a lemo wannan yasa ta fara jin wani abu na yawo a jikin.  Hira suke har wajen sha daya lokacin da wata muguwar sha'awa ta taso mata. Take ta fara tinanin moment din da sukayi spending tare a baya. Yadda yake mata da sarrafa ta da romacing nata.

Ji tayi ba abinda da take so illa ta kasancewa dashi, ko taji saukin abinda takeji, Isma'il kuwa mai karantar yanayin mace tin daga kallon ta muryar ta da motsin ta yake ganewa. Dan haka yana jin sauyin muryar ta da ya canja dan ba a haka suke magana a farko ba. Yanzu sai wani dan nishi take tana shhh kamar wacce taci yaji.

Wannan yasa ya dauko wata hirar ta in sunyi aure ga yadda zai na mata na ya dinga burkita mata tunani da lissafi. Sai da ya kai in ya mata magana ma bata iya bashi amsa yai mata sallama akan dare yayi dan har biyu da wani abu tayi.
Zai kashe wayar kenan yaji tace
"Gobe kana gida ne ko xaka kasuwa?"

"Kai hutawa xan danyi."
"Alright kila na biyo "

"Oh da gaske wallahi daman nayi missing naki yanzu in mun hadu muntuna kadan mun rabu."
"Uhmm!"

Ta fada. Yace
"Sai da safe kiyi mafarki na."
Ya kashe wayar yana wani killer smile. Text ya tura mata wanda ya kara kashe zuciyar ta da tunanin ta ji take da da hali a lokacin zata tafi gun Isma'il.

*
Isma'il washe gari kin fita yayi duk da yai niyyar fita target din sa da yaga ya dano yasa ya fasa.

Halima kuwa har ta tashi da safe bataji karfin jikin ta ba. Allah Allah take rana tayi ta tafi wajen isma'il. Ai kuwa karfe biyu ta shiga ta yi wanka ita ce dirje can wanke can ta fito ta tsara kwalliya tai kyau da ita ta bade jikin da tuare. Gidan Isma'il ta nufa.
Tana shuga ta saka key ta rufe sannan tayi ciki tana sallama. Baya falo wannan yasa tayi hanyar bedroom tana kiran sunan sa. Har ta isa bakin kofa ta fasa ta juyo dai dai lokacin da Isma'il ya fito daga wanka kenan daure da towel a kugun sa.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now