Chapter 1 page 74

168 17 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 7⃣4⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*




Tinda ya tafi take cikin zulumi da fargaba. Bama da bai kara kiran ta ba itama tana son Khaleel amman bata jin zata iya auren sa saboda mahaifiyar sa da kuma shi kan da ba zai na ganin ta da daraja ba.

Ta godewa Allah da ya ganar da ita bata mutu tana saba masa ba. Ta godewa Allah da ya ganar da ita tin wuri ba sai tayi nisan da bazataji kira ba. Lallai Allah na son ta da ya jarabce ta kuma ya shiryar da ita Allah ya kare ta ya tsare ta daga duk abun ki Amin.

Sallah ta gama tana jan carbi aka shigo ana fadin
"Anty Sakina wai kije inji wani a waje!"
"Wani kuma je kace waye?"

Ya juya ya fita. Bai jima ba ya dawo yace
"Khaleel ne!"
Da sauri ta mike tana fadin
"Khaleel da gaske Khaleel ya dawo to me yazo min?"

Amsar da ta gaza samu ta fita kawai tayi ta saka silifas sai kofar gida. Tana ganin sa taga ya rame. Kallon sa ta tsaya yi ya dago yana kallon ta sai ya sakar mata murmushi ya karaso soron gida. Jikin ta ne yai sanyi tai kasa da kai.

"Ina yini?"
"Alhandulillah na same ki lafiya?"

"Lafiya lou!"
Sai sukai shiru kowa ya kasa magana. Shine yai karfin halin fadin
"Sakina na dawo a karo na biyu na dawo da neman soyayyar ki. Na tafi naje gida da zulumi akan ki na so na cire son ki a rai na sai dai bani na sakawa kai na ba Allah ne ya saka min kinga kenan ba ta yadda za ai na cire da kai na. Amman na godewa Allah da yasa hakan dan wannan zai zama izina ko akan momy masu irin halin ta su gane. Dan haka zaki aure ni Baby?"

Tin da ya fara magana hawaye ya wanke mata fuska. Yana kaiwa nan ta juya masa baya tace
"Khaleel ba zan iya ba."

Gaban ta ya dawo yana kallon ta yace
"Saboda mahaifiyata yar iska ce?"
Da sauri ta daura hannu akan bakin sa tana girgiza kai tace
"Ka daina fadar haka dan Allah!".

"To ki ban dalilin ki!"
"Khaleel baka dace dani ba kaje ka samo mace kamila kamar ka ka aura."

"Ni wa yace miki kamili ne?"
"Dabiun ka kadai sun nuna min haka Khaleel ba zan so in cuce ka ba ka, tq yadda ba zan zo a cuce ni ko wani nawa ba."

"Amman aini nace ina son ki ko?"
"Khaleel amman...."

"Amman me?"
Kai tayi kasa dashi yai murnushi yace
"Ki cire batun Momy na ba ita zata zauna dake ba ni ina sonki a haka kuma ba yadda zatai da *Hukkuncin Allah* dan haka ki cire batun ta a ranki. Mahaifiyya tace ba zan taba iya canja ta ba ke kuma *Hadin Allah* ce ba yadda zanyi na yadda na aminta da ina son ki da aure kuma kada kisa wai zan na kallon ki a fasika in na kalle ki a haka tamkar na kalli mahaifiyya ta ne. Fatana kawai ki koma ga Allah aure na dake zai ceto ki daga wannan hanyar da izinin Allqh."

Ya durkusa a gaban ta ya ce
"Dan Allah Love ki soni ki yadda dani wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba kwana biyun nan da nayi ni kadai nasan a halin da na shiga dan Allah Sakina!"

Ya karasa maganar yana kuka. Durkusawa tayi ta kama goge masa ido. Yace
"Ki daina gogen hawayen nan domin wanda zuciya ta keyi yafi wannan zafi da radadi ko shima zaki iya goge min. Ba abinda xaki ya gogu sai amsar soyayya ta. Wallah bake mutuwa zan yi. Ki taimakan na miki alkawarin rike ki da amana."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now