Chapter 1 Page 39

342 16 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 3⃣9⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*



Farisa ce kwance jikin Alhaji Labaran sabon Alhajin da tayi kamu wanda ba abinda baya mata sai dai bata ce ba. Domin ita ma ba karamin wahalta masa take ba. Ko ina zata bishi domin bai taba samun mace mai kyau da kuruciya kamar Farisa ba. Ga ni'ima wanda daga halittar yan gidan su ne. Allah ya basu kyau,  kyan diri ga ni'ima wannan yasa maza ke haukace musu dan in sukai mu'amala da mutum ba zai kara jin dadin wata kamar su ba.

Gashin kan ta yake shafawa yana wasa dashi. Idon ta a lumshe a hankali yace
"Baby!"

Ido ta bude wanda suke son su rufe kamar me jin bacci ko dan menene oho? Kissing bakin ta yayi yace
"Na fada miki ki yadda na aure ki dan Allah wallahi da gaske nake son ki."

Ido ta bude tana kallon sa sai ta sheke da dariya sannan ta gyara kwamciyya tace
"Abinda kusan duk wanda nai taraiyya yake fada min kenan. Ban taba tambayar su dalili ba amman kai zan tambaye ka saboda me?"

"Saboda ina son ki!"
Wani kallo take masa tace
"A'ah fadi gaskiya dai cene min kada gaba na guje maka ko? To Alhaji a gaskiya zan fada maka ko na aure ka ko is fot just 2/3 month dan haka tsarin kungiyar mu yake kaga kenan gwara mu karasa a hakan ko?"

"Baby ba zaki gane bane? Ni babban mutum ne a yanzu bana son ina yawan neman mata saboda kar asiri na ya tonu. Kuma ni tinda nake neman mata ban taba samun wacce tai min kamar ki ba. Gashi young ga kyau ga sweet in dai zaki ban dama zan zama abokin rayuwar ki na har abada."
Ya fada in a serious tongue.

Kallon sa tayi ta girgiza kai tace
"A gaskiya Alhaji kayi hakuri a yanzu ba zancen aure a gaba na. Sai na gama abinda na shigo bariki dan shi."

"Me ya kawo ki bariki me kike bukata?"
"Kudi!"

Ta bashi amsa tana tsare shi da ido. Murmushi yayi yace
"In dai sune zan baki iya yadda kike so?"

Murmushi tayi tace
"Nawa kake dasu kai kam bayan ban taba jin sunan ka a jerin masu kudin nigeria ko masu kudin yan siyasa ba. Bayan ni kuma so nake kudin da xan mallaka ya zama za a na kira na a cikin jerin masu kudi. Domin ina son na inganta rayuwar yan uwa na da ya'yan da zan haifa bana son ko kadan su tashi a cikin irin *wannan rayuwar* Alhaji ka bar zancen kawai ka sha abinda zaka sha ka ban rabo na a wajen ka in kara gaba."

Ta fada tana shafo fuskar sa. Ido ta kanne masa tace
"Kada ka damu nima kana daya daga cikin wadan da nafi so a barik domin kana daya daga cikin masu min abinda nake so da kulawa dani sosai."

"Baby manya kenan. Ina son ki."
Ya hade bakin su. Nan suka cigaba da yin masha'ar su.

Sai da suka gama sukai wanka sannan ya dauke ta suka nufi supermarket dinsa ta dinga jidar abinda take so har da sabuwar waya ta dauka sannan ya bata kudi masu yawa ta koma gidan ta.

Tana shiga ta tadda su Anty Samira da Rabi'a da Bilkisu. Tana zama aka shigo mata da manyan ledojin hannun ta aka ajiye mata anan tsakar dakin.

Anty Samira uwar son abin duniya ta mike tana leka cikin ledoji ido ta zaro tace
"Me nake gani haka Farisa. Gaskiya ke me sa'a ce."

Bilkisu tace
"Duk sa'ar ta takai yayar ta ne wacce ake dambe da fada tsakanin manyan alhazawa wannan yace ya riga booking nata wani ma haka. Ke in kinga yadda Momy ta samu kudi da Fauziyya sai kin rike baki ga ta bata da son abin hannun ta ko mu nan mun dandani arziki."

Rabi'ah dake karatun novel ma bata san me suke yi ba dai da Farisa ta tabo ta sannan ta dago. Kallon ta tayo tace
"Yaushe kika dawo ince ya jika ki da naira."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now