Chapter 1 page 69

151 16 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 6⃣9⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Karfe bakwai ya tashi yai wanka ya shirya cikin milk wando da cofee kalar riga ya feshe jikin sa da turare cofe kalar takalmi ya saka ya futo ya kulle dakin sa.

Resturant ya wuce kai tsaye abinci yasa akai masa order dankali ne da kwai sai juice. Kafin yaci ya tashi ya fita. Motar sa ya shiga ya tafi unguwar su Sakina. Layi layi ya dinga bi yana tambaya wanda ba karamim wahala yasha ba duk da a mota yake kan rana ya gaji a wani masallaci yai sallah azahar yai la'asar sannan ya daura daga inda yake. A unguwar yai magariba sai da yaga dare yayi ya hakura ya koma inda ya fitowa.

Washe gari ma tin safe yake bulayi a unguwar amma sam ya kasa samun gidan har yamma. Yunwa da yaji yana ji yasa ya nufi wani resturant acan akai masa order aka kawo masa amman sam ya kasa cin wani abun kirki. Tashi yayi ya shiga masallaci yai sallah ya zauna yana addu'a tare da fadin
"Ya Allah ina roka ka in Sakina alheri ce a rayuwa tavAllah ka bayyana min ita in kuma.l ba alheri bace Allah ka ciren ita azuciyata."

Yana gama addu'ar ya rufe fuskar sa da hannu yana jin hawaye na zuba a idon sa. Hakika yau ya shiga tsaka mai wuya bai san damuwa ko rashi a rayuwar sa ba sai yau lallai yanzu ya gane rayuwa da abinda ke cikin ta.

In kaga Khaleel duk ya damu ga rashin lafiya da take damun sa na yadda ya saka damuwa a ransa. Wanda ya sa duk ya kara ramewa sam yaki fadawa Dad din sa komai.

Muhammad da ya idar da sallah ya mike zai fita ya hange shi yana kuka da sauri ya karasa yana fadin
"Bawan Allah lafiya?"

Kai ya hau girgizawa yana fadin
"Ka taimaka ka nemon ita wallahi ita ce rayuwa ta."

"Ya isa daina kukan ka nutsu wa kake nema?"
Hawayen sa ya goge ya fara bashi labari briefly. Kai ya gyada yace
"Ya sunan ta Sakina!"

"Sakina wa?"
"Wallahi ban sani ba!"

"Baka da number ta."
"Gata amman bata shiga."

"Ikon Allah kuma number dai dai ce?"
Kai ya gyada amsa yayi yai trying amman a kashe. Yace
"Kuma nan unguwar tace maka?"

Kai ya gyada. Yace
"Yanzu ina da ina ka tambaya?"

"kasan unguwar babba ce na tambayi a layi yafi goma ba respond."
"Ai gaskiya matsalar da kace sunan yarinyar kawai ka sani dama sunanvmahaifin tane da yafi sauki afi ganewa."

"Haka ne."
"Yanzu tashi na taya ka mu gani ko can kasan layi za a dace."
Tare suka fita ya dinga rakashi suna zagawa.


*
Zaune ta same ta ita da Hafsa dake hada kayan ta,  zama tayi a gefen gado ta kalli Halima tace
"Hafsa ta fada min duk abinda ya faru ba dan komai ba sai dan nice babbar ku kuma tasan ina kawo mata mafita a matsalar ta dan kinsan ko Ummah da Sakina bata fadawa ba Halima me ya ja hankalin ki. Nasan dai Hafsa ta miki fada amman kiji tsoron Allah in ada kinyi a rashin sani to yanzu kikai ke da Allah ki wallahi wuta xaki shiga dan zina babbar masifa ce kuma kika yi sai Allah ya kamaki kuma ki jawa jinin ki tabo. Allah ya yafe mana baki daya."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now