Chapter 1 page 89

167 14 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 8⃣8⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Karfe hudu da rabi Muhammad ya dawo. Yai parking Fauziyya ta fito ta kama hannun sa suka shiga ciki. Dining ta kai shi sai da ta ciyar dashi yaci ya koshi sannan suka koma falo tana jikin sa suna hira.
"Wai su Ahmad da Khaleel sunzo."

"Eh mana bakaga motar su ba."
"Tayaya zan gani ina tare dake."

Tai murmushi tace
"Sunzo suna can."
"Masha Allah"

*
Hirar soyayya suka sha abinsu wanda karfe biyar suka fito dan zuwa su gaida Yaa Muhammad. A kofar falon da Sakina take ta karasa tayi knocking.
"Busmillah."

Khaleel ya fada. Ta leka tace
"Xamu gaida Yaa Muhammad nace bari na fada muku."

Ya mike yana fadin
"Yanzu muke maganar."
Ya fito. Sakina da Hafsa sukai gaba suka biyo bayan su. Sallama sukai a kofar dakin. Fauziyya dake jikin sa tagyara zaman ta sannan suka amsa.

Shiga sukai su Ahmad na binsu a baya. Zama Hafsat da sakina sukai a two sitter. Ahmad da Khaleel suka shiga Muhammad ya mike ya mika musu hannu. Suka gaisa sannan yace
"Bismillah!"

Zama sukai sannan suka gaisa da Fauziyya cikin girmamawa. Anan suka zauna suna hira gaba dayan su. Har akai magariba suka tafi masallaci su kuma sukai sallah a ciki.

Bayan sun dawo Yaa Muhammad ne kadai ya shiga ciki su kuma suka tsaya a waje anan suka karasa hirar kamar kar su tafi. Daga baya dai suka rabu duk ba dadi.

Suna komawa suka kwaso kwanukan anan falo suka ci abinci sannan suka shiga da suka wanke kwanukan.

*
Washe gari da safe tana kwance kiran wayar Kabir ya shigo mata mikewa tayi ta kai kunnen ta tayi sallama. Ya amsa yana fadin
"Yaya Hafsa barka da safiyya!"

"Yauwah Kabir ka tashi lafiya?"
"Alhamdulilah! Dama kira nayi mu gaisa."

"Amman ka kyauta daman nima ina son na kira ka."
"To ina fatan lafiya dai ko?"

"Lafiya Alhamdulillah! Akan zancen turowarka ne in ka shirya kaanar dani zuwan magabantan naka sai na fadawa Baba."
"Alhamdulillah Baba kenan ya yadda?"

"Eh ya yadda dan haka daga ko yaushe zaka iya turowa."
"Insha Allah Yaya Hafsa a cikin satin nan zan fada musu in sun saka ranar zan fada miki."

"Insha Allahu!"
"To sai anjima."

Yana kashe wayar yai sujudul sukhur yana fadin
"Allah nagode maka. Allah kasa haka shine mafi alheri."

Ya mike ya shiga yai wanka ya fito ya shirya cikin kananun kaya yai kyau sosai. Bangaren Mamin sa ya shiga. A falo ya same ta a zaune ya durkusa ya gaishe ta cikin fara'a ta amsa taba fadin
"Me muka samu yau?"

Ya gyara zama yace
"Mami zancen aure nane!"
"To Alhamdulillah ya ake ciki?"

"Mami mata biyu nake son na aura a lokaci daya."
"Kabir mata biyu zaka iya kuwa?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now